Shugabannin
kasa da su ka fi kowa tsufa a Afrika
– A Nahiyar Afrika dai ana buga
wani irin mulki
– Shugaban kasa Zimababwe Mugabe
yana da shekaru fiye da 90
– Shugaban Najeriya Buhari kuwa ya
fi shekara 73
Shugaba
Muhammadu Buhari bai cikin shugabannin 10 da su ka fi tsufa a Afrika duk da
kuwa ya zarce shekaru 70 a Duniya don kuwa akwai manyan sa.
1. Robert Mugabe
Shekarun
shugaba Robert Mugabe na kasar Zimbabwe 93 a Duniya ke nan duk Afrika babu
shugaban da ya kai sa tsufa da kuma dadewa a Ofis watau shekaru 40.
2. Beji Essebsi
Shugaban
kasar na Tunisia ya haura shekaru 90 shi ma a Duniya wanda ya zo na biyu a
jerin shugabannin da su ka sha miya.
3. Paul Biya
Shugaba
Biya na nan Makwabtan Najeriya watau kasar Kamaru ya zarce shekara 83 a Duniya
kuma har yanzu ana damawa da shi.
4. Abdelaziz Bouteflika
Shugaba
Bouteflika na Algeria yana da shekaru 80 a Duniya kuma duk kasar Algeria babu
shugaban kasar da ya kais a dadewa a mulki.
5. Ellen Johnson Sir-Leaf
Tana
cikin shugabannin kasa mata da ake da su a Duniya, Shugaba Ellen Johnson ta
Kasar Liberia tana da shekaru 78 a Duniya.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment