La
haula: Cutar Ebola ta dawo Afrika
– Cutar nan Ebola ta dawo cikin Nahiyar Afrika
– Yanzu
haka cutar ta kashe Jama’a a kasar Congo
– Ebola dai tana kisa cikin lokacin
kan-kani
Cutar
nan da ta kashe Jama’a ta kara dawowa Afrika. Dama kwanakin bayan WHO tace babu makawa sai cutar
Ebola ta dawo. Dole
Jama’a su yi hattara domin cutar na kisa.
Tun
a kwanakin baya muka bayyana maku cewa Cutar nan ta Ebola na shirin
dawawo kasashen Duniya. Sai dai ba a san a ina cutar za ta barke ba kamar yadda
Hukumar kula da lafiya ta Duniya WHO ta fada.
Sai
dai ga shi yanzu cutar ta barke a Kasar Congo inda har mutane akalla 3 sun
bakunci lahira. Ministan lafiya na kasar ya tabbatar da wannan bayan an samu
Jama’a da dama na fama da zazzabi.
Shekaru
3 da su ka wuce cutar ta hallaka mutane kusan 50 a annobar da ta barke. Gaba
daya dai a shekarar 2013 annobar tayi barna a Afrika musamman irin su kasar
Liberia, Guinea, da Sierra Leone inda aka rasa mutane sama da 11,000.
No comments:
Post a Comment