Obasanjo
ya koma Makaranta; yana shirin zama Dakta
– Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya koma karatu
–
Obasanjo ya fara Digiri na uku watau karatun zama Dakta
– Janar Obasanjo na karatun ne a
Jami’ar NOUN
Tsohon
Shugaban kasa Obasanjo ya daura damarar zama Dakta. Olsuegun Obasanjo
na Digiri na uku a fannin ilmin addinin kirista. Cif
Obasanjo ya fadawa Malaman sa cewa idan bai yi kokari ba ka da su duba aikin
sa.
Tsohon
Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya koma Makaranta domin yayi karatun Digiri
na uku inda zai zama Dakta idan har ya kammala. Yanzu dai har yayi nisa don
kuwa ya gabatar da sharen fagen kundin da yake kokari yayi aiki a kai.
Cif
Olusegun Obasanjo yana nazari ne a kan rashin cigaba da talauci a Yankin Arewa-maso-gabashin
Najeriya a mahangar ilmin addinin kirista wanda a nan yayi Digiri na biyu.
Tsohon Shugaban yace Malaman su tsaya su duba aikin sa da kyau.
No comments:
Post a Comment