Rikicin
‘Yan Sanda da Sojoji bai yi dadi ba a Kalaba
Yadda rikicin Sojoji da ‘Yan Sanda ya ga bayan Jami’ai da dama
– Sojojin Najeriya sun kai wa ‘Yan
Sanda hari a Garin Kalaba
– Ba mamaki wasu
manyan Jami’an ‘Yan Sanda sun rasa ran su
– Abin ya kai
har an kona ofishin ‘Yan Sanda
- Rikicin Sojoji da ‘Yan Sanda ya bar gawawwaki Jami’ai
da dama
- An yi fada ne tsakanin ‘Yan Sanda da Sojojin ruwa
- Daga baya dai Sojojin sama da kasa su ka shigo ciki
Mun samu labari daga kafafe da dama cewa jiya da
dare an yi wani mugun fada tsakanin ‘Yan Sanda da Jami’an Sojoji wanda yayi
sanadiyar mutuwar ‘Yan Sanda da dama. Majiyar mu tace an fara rikicin ne da
Sojojin ruwa daga baya sauran Sojoji su ka kutso ciki.
Wanda ya ji yadda abin ya faru cikin dare ya
bayyana mana cewa an kona
ofishin ‘Yan Sanda. Abin dai ya kai an bude barikin Sojoji kowa ya dauki manyan
makamai inda aka shiga budawa ‘Yan Sandan wuta. An dai ce an harbi wani Sojan
ruwa ne a hannu.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment