Monday, May 15, 2017

Real Madrid na daf da lashe gasar La-liga

Real Madrid ta kama hanyar cin kofin kasar Spain


                                          
– Kungiyar Real Madrid ta ba Sevilla kashi a Gasar La-liga


– Real Madrid na iya kare bana da kofin gida da na Turai


–Dan wasa Ronaldo ya kara nuna kan sa




Kungiyar Real Madrid na iya gashe gasar La-liga idan abubuwa su ka cigaba da tafiya a haka. Real Madrid ta doke Sevilla da ci 4-1 jiya. Tauraron Dan wasa Cristiano Ronaldo ya jefa kwallaye 2 a daren. 

Real Madrid na neman maki 4 ne kacal domin ta lashe kofin La-liga na kasar Spain wanda ta dade rabon da ta daga sa. Hakan ya zo ne bayan Real Madrid din ta lallasa Kungiyar Sevilla da ake tunani za ta kawo mata tangarda.




Dan wasa Cristiano Ronaldo ya jefa kwallaye 2 shi kadai sannan kuma Toni Kroos ya karasa. Kafin nan dai Nacho ya jefa wata kwallo da ta jawo surutu da farkon wasa. Yanzu Real Madrid za ta kara da Malaga da kuma Celta Vigo.

Barcelona ta ba takwarar ta La Palmas kashi da ci 4-1 ita ma wanda Suarez ne ya zura 3 duk shi kadai sannan Neymar ya ci kwallo guda. 



[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...