Shugabannin kasashe sun
yi tir da harin da aka kai a kasar Birtaniya
– Shugabannin kasashe sun yi tir da harin da aka kai a kasar Birtaniya
–
‘Yan ta’adda sun kai wani mugun hari inda aka kashe Jama’a da dama
–
Har yanzu dai ana zaman dar-dar a Garin Manchester
Wani ‘Dan ta’adda ya kai
wani mugun hari a Garin Manchester na Ingila inda fiye da mutane 20 su ka
mutu nan take. Mutane akalla 60 kuma
sun jikkata a harin.
Wani Dan ta’adda ya
kashe mutane 22 a wani hari da ya kai a Garin Manchester yayin da wasu da dama
su ka samu rauni. Shugabannin kasashen Duniya irin su India, Japan, Canada, da
Australlia dai sun yi tir da wannan mugun hari.
Shugabannin Jam’iyyu
dai sun daga kamfen din zabe a dalilin hakan. Kungiyar ISIS ta Duniya dai ta
fitar da sakonni inda ta ke murnar harin da aka kai. Abin dai ya faru ne ana
wani shirin wasa na waka.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment