Saturday, May 27, 2017

Huduba kan Aure-Dr. Saeed Yunus



HUDUBAR JUMA’A DAGA MIMBARIN ITN-ZARIA




Huduba kan Aure-Daga Bakin Imam Dr. Saeed Muhammad Yunus


Assalamu Alaikum wa Rahmatul Lah,

Godiya ta tabbata ga Allah SWT wanda ya halitta mu daga rai guda. Muna shaida cewa babu abin bauta da gaskiya face Allah dai shi kadai, ba shi da ‘da ko mata ko tamka ko wani abokin tarayya ko mataimaki. Muna kuma shaida cewa Annabi Muhammad SAW, Bawan Allah ne kuma Annabi wanda ake koyi da Shi, tsira ta tabbata gare Sa da Alayen sa da Sahaban sa da wanda su ka bi tafarkin Su.
Jama’a mu kiyayi Allah mai girma mu ji tsoron Sa, mu kuma guji saba masa alhalin muna sane. Daga cikin abubuwan da Musulunci ya jawo hankalin Jama’a akai da kiyayewa shi ne abin da ya shafi Auratayya. Auratayya abu ne da ya shafi zamantakewa na Duniya da kuma Addini. A cikin aure akwai hikima madaukakiya da amfani bi-la-adadin da kuma ma’anoni manya-manya. Wani abu ne na tilas domin kuwa da shi ake gina gida da al’umma kuma da shi ne ake samun daukaka kuma a rufe idanuwa da farji. Da auratayya ne ake kara yawa, yayin da wani ya fita sai wani ya shigo. Ai aure ya isa ka ga aya daga ayoyin Allah, ai aure ayar Allah ce! Allah SWT yana cewa: Daga cikin ku Allah ya halitta maku matayen ku, domin ku samu natsuwa da soyayya da tausayi. Allah yace hakan lallai aya ce ga masu tunani. Allah ka sa mu cikin masu tunani.

Addinin Musulunci ya buga wani misali mai ban sha’awa da mamaki wanda ya nuna cewa ana samun aure ne ta hanyar iyaye kuma lallai a nemi albarka a cikin auren wajen sauwake shi. Daga ciki akwai wani hadisi da Imamu Ahmad da Bayhaqy su ka fitar daga bakin A’isha mai gaskiya ‘yar mai gaskiya RA tana cewa mafi albarka game da mata da kuma mafi girma ga mata su ne wadanda ba a wahala ba wajen auren su, watau ba a wahalar da mutum ba; ya samu sauki wajen auren su. Mu sani cewa wadanda ke wahalar da Jama’a, su ke daura nauyi game da auratayya, su na sabawa tsari na shari’a na Allah da Manzon sa Annabi SAW. Ya ‘Yan uwa ku sani cewa ya halatta Mace tace da Namiji tana son sa kamar yadda ya halatta Namiji ya ce yana son mace wanda shi ma ya fi sauki (dama Namiji an san shi wanda bai jin kunya ba, (ba wai bai da kunya ba)). Kuma don Mace tace da Namiji tana son sa, wannan an gani a lokacin Manzon Allah SAW wanda wata tace tana son Sa, amma dai bai ce bai so ba, sai ya nema mata wani Mijin. A takaice ya ku iyaye, ya halatta ku nemawa ‘Ya ‘yan ku Mata ko Maza, amma idan har wata ko wani tace ko yace ba ta ko ya so, don Allah ka da a matsa sai an yi aure, domin wannan yana haifar da fitina da bala’i iri-iri a doron kasa. Idan mutum yace bai son wani sai a hakura, aure dai ba za ayi ba! Domin Manzon Allah ya dukar da kan sa; don ba a san abin da zai biyo baya ba.

Akwai wasu matsaloli da su ke faruwa a yanzu wanda ya kamata a jawo hankali a game da su; matsala ta farko ita ce samari sun zama dika-dika, sun ki aure sun tsaya su na kakalo wasu abubuwa da ba su cikin Al-Kur’ani ko Sunnah, sai ka ga mutum ya cika shekara 40 bai yi auren fari ba. Ana makalewa da wasu dalilai marasa amfani yayin da Ubangiji SWT yace idan har kun yi aure don Allah kuna talakawa zai azurtaku daga cikin falalar sa (A cikin Suratun Nur). Abdullahi Dan Abbas yana cewa: Ku nemi wadatuwa cikin aure watau Idan ka na son kudi, sai ka yi aure. Amma fa ban fada maku cewa Hadisi ne na Manzon Allah SWT ba! Ban ce da ku Hadisi bane! Magana ce ta Dan Abbas wanda Sahabi ne da imanin sa ya cika har ya batse. Akwai wani Hadisin karya da ake cewa idan talauci ya addabi mutum to ya kara aure, to ai kuwa za ka kara talauci, ka kara lalacewa! Allah ka shiryar da mu!

Abubakar As-Sadiq RA babban Sahabi kuma Abokin Manzo SAW yana cewa Mutane: Ku bi Allah ku bi abin da ya umarce ku a cikin auratayya sai ya cika maku alkawarin ku. Kun ji Maza! Yace idan har kun bi Allah, zai cika maku alkawari. Ya ku ‘Yan Uwa akwai wadanda kuma kudi su ke nema da auren watau auren jari; ba za a nemi kowa ba sai ‘Yar mai kudi. Annabi SAW wanda ba ya karya yace duk wanda yayi aure don kudi, to karshen sa Talauci. Haka nan duk wanda ya dubi kyau kurum wajen aure wata rana zai ga matar ta kare mummuna har ta zama bai kaunar ganin ta-Akwala! Amma duk wanda yayi aure domin addini Allah Madaukaki zai cika masa burin sa. Amma Addini kuma bai hana idan mutum ya ga wata mai kyautatawa mutane kuma kyakkyawa ya aura ba, asali ma addini ya ba da dama ne. Daga cikin matsalolin da ake fama da su a yau shi ne rashin daraja masu addini, ana hana mata su auri mutanen kirki. Alhali fa Annabin Rahama SAW yana cewa duk wanda ya zo maku (neman aure), kuma ku ka yarda da halin sa da addinin sa to ku aura masa. Wadannan sharuda 2; ko da mutum yana kwana a masallaci amma bai da halin kirki bai cancanta ba, haka-zalika akasin haka. Amma fa ku sani cewa babu kamala sai Allah Mai Girma, domin ka da a ce ai yana da ‘yar matsala kaza a hana sa, kowa kuwa yana da ‘yar matsala. Allah ka shiryar da mu! Annabi SAW yake cewa idan ku ka ki aurar masa, za a samu fitina da barna da yawa a doron kasa, Tirmidhi da Ibn Majah da Hakim su ka fitar da wannan Hadisi da sanadi mai kyau.

Akwai wasu daga cikin Iyaye; Allah ya shiryar mana da su da ke cin amanar ‘Ya ‘yan da Allah ya dora masu. Su na hana ‘Ya ‘ya su auri wadanda su ka dace da su; Yarinya tayi karatu amma sai su aurar da ita ga wani ma-ci amana, su na neman mukami da matsayi da darajar wannan mutumi sun manta da darajar da Allah ya ba su. Daga cikin Iyaye akwai makwadaita wadanda su ke maida ‘Ya ‘yan su wasu kayan kasuwanci; ana cewa waye ya zo? Shin ya zo da mota? Wace irin mota? Allah ka shirye su! Wannan babban bala’i ne! Ina rahama ga wadannan iyaye da ba su tunanin aurar da Diyar su ga wanda bai da addini ba? Jama’a ina za mu je ne? Lahira fa za a tafi!

‘Abubuwan da ya zo mana a wannan zamani shi ne za a iya ba Likitocin mu dama su binciki lafiyar Ma’aurata. Domin musamman a auren zumunci a kan gaji rashin lafiya wanda wannan Littafin Tib-An-Nawawi ya tabbatar’. Ba mamaki a cikin zumuntar nan a samu cuta irin ta Sikila don haka Likitoci amintattu su yi bincike. Har da kuma sauran cututtuka na bala’i irin su Kanjamau. Ba haramun bane yin bincike wajen aurar da Budurwa ko Bazawara. Allah mu ke roko ya shiryar da mu da zuriyar mu!

Huduba ta biyu tana cewa bayan godiya ga Allah da yabo ga Annabin mu SAW wanda yake cewa yin aure na cikin Sunnar sa. Allah ka kara daraja ga farin Jakada Annabi Muhammadu SAW. ‘Yan uwa mu kara godewa Allah Ubangiji, a yau muna ganin abubuwa na lalata su na faruwa ga ‘Ya ‘yan Musulmi masu tsari. Wa ya haifar mana wannan bala’i kafin aure da bayan aure? Ya ku Al’ummar Manzon Allah SAW ku sani cewa da dama sun bar Sunna yayin da za su yi aure; ba a yin aure yadda Sunna tace; kawai ana haduwa ne yadda aka ga dama. Wannan yana haifar da fitina. Kuma ana yin barna wajen aure tare da almubazzaranci da alfahari da nuna an-isa, wanda hakan na sa Allah yayi fushi. Abincin da ake zubarwa a rana guda, na rantse da Allah sai wasu mutanen su samu na cin wata gudu. Abu na uku kuma shi ne cakuduwar maza da mata da kuma yadda Amarya da Ango ke fitowa gaban mutane; ka ga macen kirjin ta (har ma da sashen nonon ta) a waje a gaban wasu mutane sha’awa. Amarya tana rawa a gaban wani Makadi rike da hannun Angon ta. Jama’a ina koyarwar Annabi Muhammadu SAW? Idan abin ya cika, sai ka ga an kashe kudin gaske wajen haskawa a Talabijin. Sannan kuma ka ga ana daukar hotuna na haram wanda ba abin da wannan yake haifarwa sai fitina! Daga ciki akwai wasu wasanni na banza da ake yi; akwai wani zama na Party ‘Till-Dawn’ har gari ya waye a sa’ilin da Bayin Allah na kwarai ke neman gafarar Allah Madaukaki. Allah Tabaraka Wa Ta’ala yace su na neman gafara ga wasu can kuma su na ta lalata. A dalilin bikin aure sai a bar sallolin da aka farlanta don wai rana guda! Abu na biyar kuma, a kan cire rigar kunya. Ita ce kadai ranar da ake warewa Shaidan amma ban da ita kullum ta Allah ce, amma a ranar dai sai a dan huta; rai dangin goro. Ka ga an sa motoci da babura su na kara, ana tukin ganganci, wai duk ana murnar auratayya. Abu na karshe watau na bakwai shi ne cutar da samari da ‘yan mata da kowa game da abubuwan da ake ji na sauti a cikin Unguwanni da ke hana mutane ambaton Allah kuma yana jawo fitina a doron kasa.

‘Yan uwa wadannan abubuwan su na cikin abin da su ka jawo wasu matsaloli da mu ke fuskanta a yau. Daga cikin matsalolin da ake samu shi ne sai ka ga mata na tafiya tsirara; idan har ka yi magana sai a fada maka cewa ‘Ai Imani yana zuciya!’ Mata na cin amanar Mazajen su, su na rashin da’a ga Allah. Ubangijin Ka na nan a madaka! Lallai Ubangijin Ka bai manta ba!! Al’ummar Musulmi sun shiga rudu an manta da tafarkin Allah; sai ka ga yaro na tuka babur bisa titi yana goge tayan baburin dsr, sai ka tambaya ka ji ya aka yi a Ranar aure. Abu na uku kuma shi ne rashin ba iyali hakkin su na ciyarwa da sauran su; sai ka ga daga an yi albashi mutum ya raba kudin sa ga matan banza wadanda yake kwanciya da su ba matan sa ba. Wannan yana kawo bala’o’i wanda an bar hanya tun kafin aure. Ga batun sake-sake; daga yaro ya balaga ko bai da sana’a sai ace za ayi masa aure, kuma Jama’a su yarda. A kafin ranar aure a sabawa Allah haka a ranar, ga shi nan an haifi bata-gari. Daga cikin Manyan mu kuma sun goyi baya; ku dubi yadda Majalisar Dattawar da ya kamata su zama masu kafa doka su ke goyon-bayan wannan barna. Allah ka shirya su kuma Allah yana kallon ku Dattawa! Ko ku cika alkawarin da ku ka yi ko kuma Allah ya kama ku! Ban ce dukkanin su ba amma ku tuba don kuwa kun ci amanar Manzon Allah da al’umma kaf don kuwa zaben ku aka yi, amma a dalilin wani son zuciyar ku kun saba. Wai sai ace mutum guda ne ko 10 za su gyara kasa? Su suka hana ruwa gudu, ga masu tuki a kan hanya ba su da hankali. Wanda ba Likita ba yayi karyar Likitanci. Wanda ba Malami ba ya bude Makaranta! Kasa kuma tayi shiru. A ce mutum daya yayi gyara. Kai! Komai ka gani kurum hauka ne! Jama’a duk wannan matsalar ba komai ya jawo mana su ba Wallahi Auratayya ce; kar ka raba daya biyu; da aure yayi kyau, da abubuwa sun yi kyau. Lokaci ba zai bamu damar mu fadi irin abin da auratayya ta haifar na kirki ba. A haka za a haifi fitinanne, ya kuma tafi Majalisar ya zama Dan kuka. Allah ya shiryar da mu!

Abin da ya jawo aka wulakanta auratayya tun farko shi ne an bar Malamai na Allah an koma ga Malaman Duniya wadanda ba su ba da fatawar komai sai shirme. Dole mu yabi wadanda su ka bi hanyar Allah da Manzon Sa wajen Auratayyar su, Allah ka taimake su. Daga karshe muna ta’aziyyar babban Malamin Al-Kur’ani da ya rasu a Kano shekaran jiya watau Dakta Alhassan Sa’eed Jos. Allah ka masa rahama ka haskaka kabarin sa ka za ya zama dausayi na Aljanna ka sa Aljanna makoma ka cika burin sa ga Iyalin sa. Allah ka mana rahama gaba daya don mu ma muna tafe. Allah ka azurta mu da aminci a Najeriya ka taimaki dukannin Shugabannin mu. Allah ka karawa Shugaba Buhari lafiya da daukaka ka kuma gusar da damuwar sa da Makiyan sa ka watsa su. Allah ka sa mu cikin Bayin kwarai ka kuma taimake Musulmai da Musulunci. Allah duk wanda ba su da aure a cikin masallacin nan da wajen masallacin, Allah ka ba su, masu son karawa idan har alheri ne, Allah ka ba su dama! Ya Allah muna rokon ka wadanda su ka rasa maza ka ba su. Allah ka kawowa masu neman aure na kirki!



Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba.
(Malam ya gabatar da wannan huduba tun kwanaki, ban samu damar buga ta ba)

Muhammadmalumfashi@gmail.com          
Twitter: @Ya_waliyyi




5 comments:

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...