Na gaba yayi gaba: Chelsea ba za ta tsaidu ba
– Kungiyar Chelsea na daf da daga kofin
firimiya na Ingila
– Yanzu nasarar wasa guda kurum
Chelsea ke bukata
– Hakan ya zo bayan Chelsea ta
lallasa Kungiyar Middleborough
Yanzu
dai Chelsea ta kama hanyar lashe gasar Firimiya. Kungiyar
Chelsea na neman maki uku ne rak domin zama zakara. ESPN ta rahoto Dan
wasa Nemanja Matic yace har yanzu ba za su ce sun ci gasa ba.
Chelsea
za ta iya lashe gasar Firimiya na shekarar bana daga ta samu maki uku kacal
cikin wasannin da su ka rage. Tottenham Hotspur ne dai ke bin Kungiyar
sau-da-kafa a baya sai da alamu ba za ta kamu ba.
Hakan
ya zo ne bayan Chelsea ta ba Kungiyar Boro kashi a wasan da su ka buga jiya da
dare. Chelsea ta doke Boron ne da ci uku da nema wanda duk Fabregas ne ya
haddasa su. Chelsea za ta kara da Wes Brom Ranar Juma’a.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment