An
kulla yarjejeniyar makamai tsakanin Amurka da Kasar Saudiyya
– Shugaban kasar Amurka Trump ya kai ziyara kasar Saudi
– Kasashen sun
shiga yarjejeniyar makamai na sama da Dala Biliyan 100
– Amurka da
mukarabban ta na yaki a Yemen da ‘Yan Shi’a
Duk
da irin maganganun da Donald Trump ya rika yi a baya abubuwa ba su canza ba. Kasar
Amurka za ta cigaba da saidawa Saudiya manyan makaman yaki. Amurka
dai ta nan ta ke samun makudan kudi.
Shugaba
Donald Trump ya isa kasar Saudiya jiya inda aka kulla wata yarjejeniya na
makamai na sama da Dala biliyan 110 wanda kuma nan da shekara goma za a kara
sayan wasu na sama da Dala Biliyan 350.
Ba
dai a ga maciji tsakanin Saudiya da kasar Iran, asali ma dai Saudiya na cigaba
da yakar ‘Yan Houthi da ke Yemen wanda Kasar Iran ke marawa baya. Trump dai
yana ma nema ya zarce Shugaba Obama wajen kawancan sa da kasar Saudiya.
No comments:
Post a Comment