Sunday, April 30, 2017

Wasan dambe: Dan Najeriya ya gabje Klitschko

     
Abin alfahari: Dan Najeriya ya zama ‘Dan damben Duniya



 – Wani asalin dan Najeriya ya doke Klitschko a wasan dambe


– Yanzu haka ya karbi kambun damben Duniya


– Wladmir Klitschko ya sha kashi hannun Joshua






A wani wasan damben Duniya da aka yi a Kasar Ingila wani ainihin Dan Najeriya ne yayi nasara. Wannan dai abin farin ciki ne ga ‘Yan kasar da kuma daukacin bakaken Mutanen Afrika baki daya.

Anthony Joshua ya gabje Wladmir Klitschko a damben Duniyar da aka gwabza a filin wasa na Wembley da ke Birnin Landan inda mutane kusan 90, 000 su ka hallara gudun a gani a ba su labari.




Yanzu haka Joshua wanda asalin sa Dan kasar Najeriya ne ya karbe kanbun damben Duniyar na Heavyweight inda ya zama zakara bayan ya tika Zakaran Duniya Wladmir Klitschko da kasa a kusan zagaye na daf da karshe.

Anthony Joshua ya bayyana sirrin karfin da yake da shi yace ba zai rasa nasaba da sakwara da teba da sauran abincin 'Yan Najeriya ba.



[NAIJ Hausa]

Saturday, April 29, 2017

HUDUBAR JUMA’A DAGA ITN-ZARIA



HUDUBAR JUMA’A DAGA MIMBARIN ITN-ZARIA


Watan Sha’aban; Jakadan Ramadan-Daga Bakin Imam Sheikh S. S Abubakar






A’udhu BilLahi minas Shaidan Ar-Rajim,
BismilLahir Rahman Ar-Raheem,

Godiya sun tabbata ga Allah, muna yabo gare sa Madaukakin Sarki. Muna shaidawa lallai babu abin bauta da gaskiya face Allah shi kadai ya ke wanda ya shar’anta ga Bayin sa tafarkin da zai kai ga samun yardar Sa. Muna shaidawa lallai Shugaban mu; Annabi Muhammad SAW Bawan Allah ne kuma Manzon Sa, wanda ya shiryar da Al’ummar sa ga yin biyayya ga sunnar sa.

Bayan haka:
‘Yan uwa a yau muna cikin rana ta farko na Watan Sha’aban wanda Manzon Allah SAW ya kasance yana damuwa da shi saboda abin da aka ruwaito daga Usama Dan Zaid RA, yace: Na ce da Manzon Allah SAW meyasa yake azumi a cikin Watanni amma ba kamar yadda yake yin azumi a Watan Sha’aban ba? Sai Manzo SAW yace: Saboda wannan wata ne da Mutane su ke rafkana da shi wanda yake tsakanin Rajab da kuma Ramadan kuma wata ne wanda a cikin sa ana daukaka ayyuka zuwa ga Allah, sannan Ni ina so a daukaka ayyuka na ina mai azumi. Imam Al-Nisa’i ya ruwaito wannan Hadisi kuma Malaman Hadisi sun inganta shi.

Kenan Annabi SAW yana son Azumi a cikin wannan wata saboda a cikin sa ake daukaka aiki a gaban Allah Madaukaki inda yake so a bayyana ayyukan sa yana mai azumi. Wannan wata dai shi ne Jakadan mai martaba wanda yake zuwa kafin abin so mai girma da daraja. Shi dai wannan wata Sha’aban shi ne Jakada na watan Ramadan abin son mu. Kuma wannan zai kasance ne ta hanyar aikata al’amura masu sauki ga wanda shi damuwar sa ya samu yalwa da haske a cikin kabarin sa bayan mutuwa. Kuma abubuwa ne da Mutum zai gabatar idan har manufar sa ya samu jin kai da yardar Ubangiji SWT, wanda ya kasance haka ne tunanin sa zai yi kokari ya girmama Jakada ga watan Ramadan.

Ta yaya ake girmama wannan Watan? Ta yin Azumi a cikin sa kamar yadda Hadisi ya gabata da kuma abin da aka ruwaito daga Aisha RA inda ta ke cewa: Ni, ban ga Annabi SAW yana cika Azumi wani Wata in ba Ramadan ba, amma kuma ban taba ganin Watan da yake yawaita Azumi ba kamar Watar Sha’aban. A wata ruwayar Nana A’isha RA ta ke cewa Manzo SAW yana azumtar daukacin Watan. Don haka ya kamata muyi kwaikwayo da wannan Sunnah na yawaita Azumi domin karrama wannan Wata.

Abu na biyu da za muyi domin karrama wannan Watan da yake Jakada na Ramadan shi ne mu tsarkake rayuwakan mu daga abubuwa na zunubi da kuma sabon Allah. Gidajen mu su tsabtatu daga duk wata kazanta. Sannan kuma a kula da tuba Bayin Allah; tuba ta nasiha zuwa ga Allah. Mu kuma yi kokari mu ga abin da zai zama sulhu tsakanin mu da Mahallicin mu; mu bude wani sabon farin shafi ga abin da yayi saura na rayuwar mu kuma kullum mu rika jin albishir da cewa Allah zai yafe mana idan mu ka nemi ya yafe kana ya karbi tuba ba tare da cire tsammani ba,  kamar yadda aka fada a Al-Kur’ani cewa ka da a yanke tsammani daga gafarar Ubangiji don lallai Allah yana yafe zunubai baki daya domin shi mai yawan gafara ne da jin kai.

Saboda haka ‘Yan uwa Musulmi sai duk mu yawaita kwadayi na cewa ka da Watan Ramadan ya shigo mana face cewa muna cikin tsarki da tsabta a wannan Wata da za muyi tattali. Sai mu kiyayi wani abu na shirka wanda Allah SWT yayi alkawari ba zai yafewa duk wanda ya mutu yana kai ba. Shirka dai abu ne da ya zama ruwan dare a yau, Jama’a na rayuwa cikin Mutane da yawa ba tare da sanin haka ba. Dole ne ayi kokarin kaucewa Shirka. Mu’amular da Jama’a ke yi na jefa su hannuwan Bokaye masu yi masu alkawari na banza su na nuna masu cewa za su yi masu abubuwan da babu mai yin su sai Allah Sarki. Haka kuma ga Shirka ta riya da ta ke bayyana wanda Mutum ba zai aikata alheri ba sai dai don a gani a yaba. Wannan duk ya kamata mu kaurace masu.

Sannan kuma mu kiyayi zalunci duk irin zalunci da Shari’a ta fada don ba shi da rana. Kamar yadda ba za mu so a zalunci namu ba, don Allah ya fada da kan sa cewa shi ya haramtawa kan sa zalunci, don haka mu ma ka da mu yi zalunci mu nisance sa kamar yadda Shari’a ta fada. Sannan kuma ya kai wanda hakkokan Mutane ya ke gare ka, ka tabbatar cewa ka da ka tare hakkin wani ko har wani yayi kuka da kai. Wannan yana cikin aikin zalunci wanda bai dace duk wani mai jiran Rahamar Allah SWT yayi ba.

Ya kai wanda ka ke kangarewa ga Mahaifan ka, ya kamata ka nemi yardar Allah SWT ta kofofin da ake samun yarda. Daga cikin wadannan kofofi akwai hanyar biyayya ga Iyaye. Saboda haka idan kana da iyaye kuma har Allah ya hada ka zama da su. Ka yi kokari ka samu yardar su don biyayya gare su wajibi ne idan har bai saba fushin Allah ba. Fushin Allah kuma yana ga fushin Mahaifa idan har sun yi bisa ga abin da su ke da hakki a kai.

Girmamawa na uku da za muyi wa wancan Wata shi ne mu yawaita karatun Al-Kur’ani. Hakika wadanda su ke magabata kuma managarta shugannin mu su na iya bakin kokari na tattali domin shiga cikin Watan Ramadan. Ga duk wanda ya san irin falalar Watan Ramadan ba zai yarda cewa sai ta shigo kafin ya fara azumi ba watau tattalin abin cin riba na Watan. Wanda yake Dan kasuwa mai hangen nesa zai yi tattali ne tun kafin Ranar kasuwa ya ci riba, ba sai Ranar ne zai nemi kayan da zai sayo sannan ya saida ba. Don haka dai komai yana bukatar shiri; Magabatan mu kan yi shirin ne domin cin ribar Watan Ramadan. Ba su kyale Duniya ta rude su har su shantake ba wanda Duniya mai yawan yaudara ce da makirci da rudurwa. Saboda haka ya kai wanda ka ke so ka mori Watan Ramadan ta ya za ka samu ganima na wannan Wata sai ka takar-kare ka dage da ayyuka. Ta ya za ayi wannan ba tare da tsarkake dukiya ba ko wanda yake cikin tabon shan kayan maye da aikata ashha na zunubai? Ta ya Mutum zai ji dadin karatun Al-Kur’ani a watan Ramadan alhali bai tsarkake harshen sa daga giba ba ko kuma cin dukiyar Jama’a ba? Annamimi, ko ta ya zai amfana da Watan Ramadan idan har yana wannan dabi’a? Ta ya Mutumin da zuciyar sa ke cike da keta da kiyayya da hassada ga Musulmai zai yi tsammanin amfana da wani abu na Watan Ramadan? Ta ya ya Mutum da yake kasance tsundum cikin abinci da suturar Haramun zai samu Allah SWT ya amsa masa addu’ar sa kamar yadda Imam Muslim ya ruwaito.

A sani Bayin Allah cewa Ubangiji Allah SWT Tsarkakakke ne wanda bai karba face tsarkakakke, mu yi kokari wajen rabuwa da duk wani mugun hali ko dabi’a, mu tsarkaka wajen duk abin da Allah SWT ba ya so a ko ina. Lallai Allah SWT ya umarci masu imani da irin abin ya umarci Manzonin sa na cewa: Ku ci daga abu mai tsarki ku kuma yi aiki na gari. Wannan kuma shi ne umarnin da ke kan sauran masu imani. Ka da Mutum dai ya zama ya ci face daga mai tsarki ta kowace fuska.



Allah ya ba mu fahimtar Al-Kur’ani mai girma, ya amfane ni da ku duka daga ayoyi masu wa’azi na hikima. Allah ya tsare ni da ku daga azabar wuta mai radadi don kuwa shi mai ji ne kuma mai gani. Allah ka dada tsira da Annabi Muhammmad SAW da Iyalin sa ka tabbatar da yardar ka da Sahaban sa ka kuma buwayar da Addinin Musulunci, ka rugurguza makiyan mu. Allah ka cika ayyukan mu da abin da zai zama alheri a gare mu ka tserar da mu da kunyar Duniya da lahira.




Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga Masallacin I.T.N-Zaria.
Muhammadmalumfashi@gmail.com          
Twitter: @Ya_waliyyi





Wednesday, April 26, 2017

Anya kalau: Yau ma Shugaban kasa bai halarci taro ba



Makonni kusan uku kenan ba a ga Buhari a taro ba
 

– Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai halarci taron FEC ba


– Yanzu haka Osinbajo ke jan ragamar taron


Makonni uku kenan ba a ga shugaban kasar ba




Kusan makonni uku kenan ba a ga shugaba Buhari a taron Majalisar FEC da aka saba yi kowane mako ba. A halin yanzu haka Mataimakin shugaban kasa Farfesa YemiOsinbajo ke jan ragamar taron da ake yi na yau.

Wancan makom da ya wuce ba ayi taron ba sam, inda shugaban kasar yace lokacin an dawo daga hutun Easter a kurarren lokacin don haka aka bari sai Ministoci sun kintsa tukun ta bakin Malam Garba Shehu.

A makon baya ma dai shugaban kasa bai halarci taron ba inda Mataimakin sa ne ya ja ragamar. Ministan yada labarai yace ba wata matsala ce ta sa hakan ba illa-iyaka shugaban kasar ya ba Farfesa Yemi Osinbajo domin ya cigaba da wasu ayyuka na dabam.

Kwanaki aka kori wani Dan jarida daga Fadar Villa mai suna Olalekan Adetayo bayan Dan jaridar ya bayyana cewa shugaban kasar bai lafiya ba kuma a ganin sa. A taron na yau dai akwai wanda ta maye gurbin Babachir Lawal watau Dr. Habiba Lawal.

Yanzu haka mu ke jin cewa Ministan yada labarai na kasa Lai Mohammed yace shugaba Buhari na bukatar hutu don haka daga gida zai rika aiki. 



[NAIJ Hausa]

Tuesday, April 25, 2017

Yadda fadar shugaban kasa tayi amai ta lashe

Yadda fadar shugaban kasa tayi amai ta lashe


– Kwanaki aka kori wani Dan jarida daga fadar shugaban kasa


– Jim kadan kuma sai ga shi an maido sa


– Hakan ya jawo alamar tambaya a kasar




Idan kuna biye za ku san cewa a farkon makon da ta wuce shugaban masu tsare shugaban kasa Bashir Abubakar ya kora wani Dan Jaridar Punch daga fadar shugaban kasar a cewar yayi wani rahoto game da lafiyar shugaban kasa Buhari.

Jim kadan kuma sai ga shi shugaban kasar ya bada umarni a maido Olalekan Adetayo ya cigaba da aikin sa. Shugaban kasar ya bayyana cewa Bashir Abubakar bai tuntube sa kafin ya dauki wannan mataki ba.

Shugaban kasar wanda tsohon Soja ne dai yana cikin abin da ya fara yi hawan sa mulki dawo da wani Dan jaridar kasar waje da aka kora a lokacin shugaba Jonathan ya cigaba da aikin sa domin nuna riddar sa zuwa Damukaradiyya.

Olalekan Adetayo ya bayyana cewa ana cewa ana neman sa dama dai yayi wuf ya kira mai magana da bakin shugaban kasar Femi Adesina. Nan gaba dai maganar za ta kara fitowa don kuwa Dan jaridar ya bayyana cewa shugaban kasar bai lafiya.




[NAIJ Hausa]

Monday, April 24, 2017

Messi ya bar tarihi a gidan Madrid



Hatsabibin Dan wasa Messi ya bar tarihi a Madrid



 Barcelona ta doke Real Madrid a gidan ta


– Real Madrid ta sauko daga saman teburin La-liga


– Messi ya nuna kan sa a wasan Elclasico




Dan wasan Barcelona watau Lionel Messi ya kara nunawa Duniya kan sa inda ya lallasa Real Madrid har gida a wasan da suka kara jiya. Lionel Messi ya ci wa Barcelona wasa ana daf da tashi.

Yanzu haka Messi na da kwallaye 500 a rayuwar sa, sai dai magoya bayan Real Madrid ba za su ci da dadin wannan ba ganin a gaban su aka yi. Real Madrid dai ta samu jan kati a wasan ta hannun Sergio Ramos.

Hakan na kuma nufin cewa Barcelona ta doke Real Madrid daga saman teburin gasar La-liga sai dai Real Madrid na da wasa guda da yayi kwantai. An dai dade Dan wasa Messi bai samu galaba a kan Real Madrid ba sai wannan karo.





[NAIJ Hausa]

Bill Gates ya hana yaran sa su rike wayar salula


Mai kudin Duniya bai bari yaran sa su rike wayar salula sai sun girma


Attajirin Duniya Bill Gates yace bai barin kananan ‘ya ‘yan sa su mallaki waya


– Bill Gates yace sai sun girma yake ba su damar samun tarho


Bill Gates dai yace agogon hannun sa bai wuce Dala 10 ba




Tun shekaru 23 da suka wuce Bill Gates yake cikin Attajiran Duniya to sai dai duk da haka agogon da yake daurawa bai wuce Dala 10 rak ba kamar yadda NAIJ.com ta samu labari daga wata Jaridar Amurka.

Bill Gates da matar sa Melinda suna da ‘ya ‘ya 3 ne rak a Duniya inda babban ke da shekaru 20. Mr. Gates yace bai bari yaran su taba rike waya sai sun kara girma sun kai shekara 14. Bill Gates ne dai wanda ya kirkiro manhajar Microsoft a Duniya.




Mai kudin Duniyan yake cewa kuma ba kasafai yake bari yaran su rike waya ba a ko da yaushe musamman cikin dare lokacin barci. Bill Gates yace hakan zai taimaka masu kwarai da gaske a rayuwar su.

Duk Duniya a wannan shekarar ma dai kasurgumin Attajirin ne ya fi kowa kudi a Duniya. Arzikin Bill Gates ma dai karuwa yayi daga Dala Biliyan 75 zuwa Dala Biliyan 86 a bana. Duk da haka Bill Gates bai wasa da tarbiyyar iyalin sa.




[NAIJ Hausa]

Sunday, April 23, 2017

Hudubar Juma'a 'Wahala a Duniya'-Sheikh S. S Abubakar


HUDUBAR JUMA’A DAGA MIMBARIN ITN-ZARIA



Wahalar Duniya-Daga Bakin Imam Sheikh S. S Abubakar




A’udhu BilLahi minasshaidan Ar-Rajim,
BismilLahir Rahman Ar-Raheem,
Dukkan godiya sun tabbata ga Allah, wanda yake bada Duniya ga wanda yake so da wanda ma ba ya so. Amma ba ya bada lahira face ga wanda yake so, muna yabo da godiya gare sa Madaukakin Sarki. Muna neman tsari da hasken zatin sa mai daraja daga duk abin da zai samu cikin aikin gajiya da wahala. Muna rokon sa ya dawwamar da mu a cikin gidan sa na aminci inda yake babu yasasshiyar magana da kururuwa na ihu. Muna shaidawa lallai babu abin bauta da gaskiya sai Allah shi kadai wanda gare sa komawa take. Sannan Shugaban mu; Annabi Muhammad SAW Bawan Allah ne kuma Manzon Sa ne wanda ya zo mana da mafi adalcin hukunce-hukunce alhali bai yi karatu ko rubutu ba.


Bayan haka:
Ku sani ‘Yan uwa an gina rayuwar ‘Dan Adam ta Duniya bisa ga wahala da yin ayyuka masu gajiyarwa da yin gwagwarmaya da fadi-tashi kuma babu hutu a cikin wannan rayuwa ta Duniya. Allah Madaukakin Sarki yana cewa ya kai Dan Adam lallai kai mai wahala ne, mai fadi-tashi a yayin da kake kokarin komawa ga Ubangijin ka.

Saboda haka ya kai ‘Dan uwa ka sani cewa a duk wani lokaci kana ketawa ne cikin lokacin da aka diba maka na doron kasa a yayin da kuma ka ke ketawa kana ta fadi-tashi ne a cikin rayuwar ka. Babu mutumin da zai zauna a cikin rayuwar sa yace babu fadi-tashi sai dai hutu, dole sai yayi fadi-tashi komai matsayin sa da dukiyar sa, illa yanayi ne kurum yake bambanta. A ko yaushe haka za ka cigaba da wannan har ka sadu da Ubangijin ka domin a gare sa wurin komawa ya ke.

Wannan fadi-tashi ko ya zama ta hanyar wani aiki da za kayi da jikin ka ko kuma ta hanyar wata gwagwarmaya na abin da za kayi da tunanin ka ko hankalin ka. Saboda haka Dan Adam ka sani cewa ba za ka samu hutu ba har abada. Ana samun hutu ne bayan an komawa Allah amma fa ga wanda yayi abin da za a sama masa hutun watau na gabatar da biyayya da da’a ga Ubangiji. Mu sani ‘Yan uwa lallai duk abin da ke cikin wannan Duniya tamkar inuwa ce wanda za ta gushe; duk wani rai da mukami da dukiya da Allah zai ba ka aro ne na wani lokaci kafin Ubangiji mai shi ya karbe abin sa.

Annabi SAW ya siffanta Duniya kamar kurkuku ce ta Mumuni mai imani sannan Aljanna ce ta Kafiri wanda Imamu Muslim ya fito da wannan Hadisi. Kurkuku wuri ne mai tsanani da kunci da wahala saboda Mumuni kullum a Duniya yana cikin fadi-tashi da gwagwarmaya na biyayya ga Ubangijin sa da kuma sabawa abin da rai da zuciya da ma shaidan yake so. Kullum mai imani na kokarin samun yardar Allah Ubangiji, don haka Duniya tamkar wanda aka takurawa ne ga mai Imani. Shi kuwa kafiri Aljanna ce a wurin sa don kuwa bai damu da ya lazumci dokokin shari’a ba, kuma ba ya shiryuwa da wani Addini ko tafarki na gaskiya ko ya mika wuya ga Ubangiji. Shi Kafiri a kullum bukatar sa tana kan bukatun ran sa tamkar ya samu Aljanna kenan tun da yana abin da ya ga dama.

Ya Kai ka sani cewa duk wani Dan Adam da yake wani kokari yana fadi-tashi ya kan hadu da abin da ba ya so a cikin Duniya wanda wannan da Musulmi da Kafiri; Mace da Namiji; Mai kudi da Matsiyaci duk daya su ke. Sai dai akwai bambanci; watau wani shi wahalar sa tana ga biyayya ga Allah da Addinin sa. Akwai kuma wanda duk wahalar sa ba ta wuce ta sha’awar sa ba. Don haka akwai bambanci tsakanin wanda yake wahala wajen cigaban al’umma da yada manufofi na alheri da tunkude duk wani tsanani da kunci da wanda ya damu kurum da sha’awowin da sabon Allah da jawo fushin Ubangiji a cikin gwagwarmayar sa. Wadannan mutane su na raba kawunan Jjama’a suna zubar da jini tare da ha’intar mutane.

Don haka dai wahala da fadi-tashi ya zama dole, sai dai abin tambayar shi ne a kan menene mutum yake wahala? Wannan manufar ita ce abin dubawa. Duk wanda yace ba zai kara wani aiki na wahala ba yayi karya. Abin da ake so ya zama duk wahala da za ayi, ta zama wahala ce mai riba. Allah yake fada mana a Al-Kur’ani cewa ko shin za mu sanya al’amurran Musalmai wadanda su ke biyayya ga Allah da wadanda su ke keta iyakokin Ubangiji? Allah yace ta ya ma za su zama daya??? A wani Hadisin kuma na Imam Muslim, Annabi SAW yake cewa Al-kur’ani hujja ne a gare ka ko a kan ka.
Saboda haka kowane cikin mu idan ya fito wahala kullum sai ya rika tambayar kan sa ko shin abubuwan da yake yi na kirki ne ko wanda za su dulmiya sa cikin wuta. Wahalar da ake magana watau mutum ya tafi zuwa wajen sana’ar sa, kai ko wurin hira mutum ya tafi, ya duba ko shin me yake kokarin samu a wannan hira. A kan haka ne za a auna kai-kawon mu a ga ko a kan me muke wahala. Wannan shi ake so mu rika tambaya kullum ba jifa-jifa ba; mutum ya duba kan sa domin yayi farin ciki ko kuka da nadama idan yayi daidai ko akasin haka.

Mu sani a Duniya daga Ma’aikaci ko ‘Dan kasuwa ko wani Mai sana’a ko Mai mukami kowane dai akwai rawar da yake takawa a cikin aikin na sa. Duk wanda yake wannan wahala domin samun yardar Allah ko da kuwa zai samu wani abu na Duniya sai ka ga yana samun aikin sa gwanin kyau. Irin wannan mutumi yana mai yawan hallarto Allah yana gujewa haram kuma ba zai yarda Duniya ta rude sa ba komin yaya. Kai komai karfin abokan gaba wannan mutumi ba zai rabu da addinin sa da ka’idojin sa ba komai makirci da rudani ko yawaitar barna. Wannan mutumi zai yi wahala amma fa ba ta banza ba wanda iyakar ta zuwa lokacin rayuwar Duniya don abin da Allah mai girma ya masa tanadi shi ya fi wanzuwa.

Allah SWT yake cewa: Hakanan muka yi wahayi watau ga Manzo Annabi na Al-kur’ani cikin larabci domin ka gargadi mutanen Garin Makkah da sauran Mutane na Garuruwa domin yi masu kashedi da Ranar Kiyama inda za a kasa Mutane gida biyu. Saboda haka kullum mu rika yi wa kan mu hisabi muna duba ko wahalar mu ta banza ce domin mu ci riba a Duniya da lahira.


Allah ka ba mu fahimtar Addini ka tseratar da mu daga azaba mai radadi ka karbi ayyukan mu ka dada tsira ga Annabi Muhammadu SAW da wadanda su ka bi tafarkin sa. Allah ka buyawar da addinin ka kuma kayi maganin abokan gaba. Allah ka jikan masu rauni ka karfafa masu ka gafarta mana akan abin da muka zame ciki. Allah ka yaye mana musiba ka sa ayyukan mu su zama na gari. Allah ka sa kar muyi wahalar banza a Duniya. Allah ka shiryar da shugabannin mu ka sa su aikata alheri Duniya da Lahira.




Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga Masallacin I.T.N-Zaria.
Muhammadmalumfashi@gmail.com          
Twitter: @Ya_waliyyi



Thursday, April 20, 2017

Juventus sun gagari Barcelona


UEFA Champions league: Juventus sun gagari Lionel Messi

 

Barcelona tayi waje daga Gasar UEFA Champions league


– Juventus ta doke Barcelona tun a zagayen farko


– Wannan karo an tashi 0-0 ba tare da ci ba





An yi waje da Kungiyar Barcelona daga daga Gasar UEFA Champions league na zakarun Nahiyar Turai na kakar bana a jiya inda su ka fafata da Juventus. Yanzu Juventus ta karasa zagaye na gaba.

An dai tashi wasan ne babu ci sai dai a karo na farko Juventus sun doke Barcelona da ci 3-0. A wancan karo Dan wasa Dybala ne yayi tashe. Wannan karo dai Barcelona sun yi kokarin rama kwallayen amma Juventus su ka kare ragar su.


A zagayen baya Barcelona ta fitar da PSG bayan da farko ta sha mugun kashi wannan karo dai duk da ‘Yan wasan Barcelona abin ya faskara. Dama can Real Madrid sun yi waje da Kungiyar Bayern Munich daga Gasar a wasan Ranar Talata.

Dortmund ta yi waje bayan da Kungiyar Monaco ta kara lallasa ta da ci 3-1. Yanzu dai ba wata Kungiyar Jamus da Ingila a Gasar.




[NAIJ Hausa]

Wednesday, April 19, 2017

UCL: Real Madrid ta kora Bayern Munich gida


Ronaldo ya kai Real Madrid zagaye na gaba a Gasar UCL 

 

Real Madrid ta kara ba Kungiyar Bayern Munich kashi


– A zagaye na biyu an tashi 4-2 a gidan Madrid


– Cristiano Ronaldo ya kara jefa kwallaye 3



A bangaren wasanni Zakaru Real Madrid sun yi waje da Kungiyar Bayern Munich ta Kasar Jamus daga Gasar UEFA Champions league na zakarun Nahiyar Turai a wasan jiya Talata.

A wasan farko kuna da labari cewa Real Madrid ta doke Bayern Munich da ci 1-2 a gasar. Haka wannan karo Real Madrid ta kara ba Kungiyar Bayern Munich kashi a wasan zagaye na biyu inda aka tashi 4-2 a gidan Santiago na Madrid.




Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo ya jefa kwallaye 3 duk shi kadai a wasan inda ya zama dan wasan farko da ya zura kwallaye 100 a Gasar UEFA Champions league. Sai dai Jama’a sun yi korafi game da yadda Alkali ya busa wasan.

Har wa yau Atletico Madrid ta doke Leicester City ta Ingila inda tayi waje a Gasar. Haka kuma yau za a fafata tsakanin Juventus da Kungiyar Barcelona. Dama wancan makon Monaco ta ba Dortmund kashi a Jamus.



[NAIJ Hausa]

Tuesday, April 18, 2017

Ya za a kare tsakanin Buhari da Sanatoci



Yaushe za a kawo karshen rikicin Buhari da Sanatoci


– Ana ta samun rikici tsakanin shugaban kasa da ‘Yan majalisar Dattawa


An nada Kwamitin sulhu amma har yanzu ba a fara aiki ba


– Shugaban Majalisar yace yana bayan shugaban kasa





Kuna da labari cewa an nada kwamiti da zai zauna domin kawo karshen rikicin da ake ta fama tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buahri da kuma ‘Yan majalisar Dattawar kasar.

Kwanaki aka yi ta samun takaddama tsakanin mutanen shugaban kasar da kuma Sanatocin Najeriya musamman game da shugabannin kwastam da kuma EFCC. Har dai ta kai Gwamnatin tarayya ta ke cewa za ta nemi ta shawo kan lamarin don yana ci mata tuwo a kwarya.




Shi dai shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya bayyana cewa babu wani rikici tsakanin su da shugaban kasa kai-tsaye inda ma ya nemi mutanen Najeriya su kara hakuri su kuma cigaba da marawa Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari baya yace shi ma yana goyon bayan ta. 

Shugaban kasa ya nada kwamiti domin sulhu da Majalisar daga ciki akwai dukkanin Ministocin kasar da su ka taba zama Sanatoci ko 'Yan Majalisar Tarayya a baya da kuma masu ba shugaban kasa shawara game da Majalisa Sai dai har zuwa yau Ranar Talata ba su fara wani zama ba.


[NAIJ Hausa]





Monday, April 17, 2017

Abin da ya sa Ahmed Musa ya rabu da matar sa



Dalilin da ya sa Dan wasa Ahmed Musa ya saki matar sa



– Babban Dan wasan gaban Najeriya Ahmed Musa ya saki matar sa


– Mataimakin Kyaftin din Najeriya ya nemi ya kara aure


– Matar sa tace sam ba za ta yarda ba


Ahmed Musa da Sahibar sa a da


Kuna da labarin cewa Dan wasan gaban nan na Najeriya da kuma kungiyar Leicester City ta Ingila yayi wa matar sa duka wanda daga baya ya karyata ya kuma ce zai maka gidan jaridar da su ka fara masa wannan kazafi a kotu.

Yanzu haka majiyar mu ta bayyana mana babban dalilin da ya sa Dan wasan ya rabu da uwar ‘ya ‘yan sa. Ahmed Musa dai yayi niyyar kara mata, wanda mai dakin sa fa ta tubure tace sam ba za ta yarda ba duk da cewa addini bai hana ba.



Juliet; Budurwar Tauraro Ahmed Musa

Abin ta kai har manya da iyaye su ka shigo cikin maganar domin a lallabi Jamila ta hakura da karin auren Mijin na ta amma abu ya faskara. Har Mahaifiyar Dan wasar ta je har Ingila domin ta shawo kan Sirikar ta amma fa tace sam ba za ta yarda ayi mata kishiya ba.

Hakan ta sa aka raba jiha tsakanin Ahmed din da Jamila uwar ‘ya ‘yan sa biyu bayan da ya tubure cewa sai ya kara aure ita ma ta cije.



[NAIJ Hausa]

Jose Mourinho ya dauki fansa a kan Chelsea


Kocin Man Utd Jose Mourinho ya dauki fansa



Man Utd ta ba Chelsea kashi a Gasar Firimiya


– Kungiyar Manchester ta ba doke Chelsea da ci 2-0


– Chelsea sune a kan saman teburin Gasar




A bangaren wasanni cewa Kungiyar Manchester United ta ba Chelsea kashi a Gasar Firimiya ta Ingila. Man Utd din dai ta doke Chelsea ne da ci 2 da nema ta hannun Dan wasa Rashford da kuma Ander Herrera.

Chelsea ce dai ke saman teburin Gasar na Firimiya amma kuma hakan ya sa ta rage maki inda Tottenham ke jiran ko-ta-kwana. Kocin Chelsea Conte yace sun yi sakaci a wasan kuma ya dauki laifi.



A farkon kakar bana dai Chelsea ta dagargaza Man Utd a Filin Stamford Bridge da ci 4-0. Wannan karo tsohon Kocin Chelsea Jose Mourinho ya dauki fansa. Tun da Koci Mourinho yake wasa a Ingila dai babu kulob din da ta taba dukan sa gida-da-waje.

Barcelona da Real Madrid sun yi nasara a Kasar Spain da ci 3-2 inda Isco da Lionel Messi suka jefawa Kungiyar su kwallaye biyu. A kasar Italiya kuma kunnen doki aka yi tsakanin Inter Milan da AC Milan.




[NAIJ Hausa]

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...