Falalar azumin Ranar Arafah a
Musulunci
- Ranar 9 ga wannan wata ce Ranar
nan ta Arafah a Addinin Musulunci
- Allah Madaukaki ya rantse da
ranakun Watan da kuma ta Ranar Arafah
- Ana karbar addua da kuma 'yanta
bayin Allah a wannan Rana ta musamman
A
cikin al kurani Ubangiji ya rantse da wannan rana ta Arafah da ake taruwa na
musamman a Suratul Buruj.
Daga
cikin darajar wannan rana akwai cewa:
- A wannan rana ne aka cika sakon Addinin
Musulunci inda har Aya ta sauka a cikin Suratul Ma'ida
- Kuma a wannan rana ne ake 'yanta
bayin Allah da dama kamar yadda Hadisi ya zo a littafin Sahih Muslim
- Har wa yau kuma babu ranar da
Ubangiji yake karbar addua kamar wannan rana wanda shi ma ya zo a littafin
Silsilal hadith na Sheikh Nasir Deen Albany.
Duk wani Mahajjaci a
wannan rana ya dukafa ana kuma neman rahamar Allah. Ana son azumi ga wadanda ba
su je Hajji ba wanda ke kankare zunuban shekara biyu. Azumin ranar Arafah na yafe zunuban shekarar bara da
kuma shekarar bana da ake ciki inji Manzon Allah SAW.
Dr. Isa Ibrahim Ali Pantami yayi wannan jawabi a wani karatu da yayi