Wednesday, May 31, 2017

An sace wani Dan Majalisar Tarayya


An sace wani Dan Majalisa a hanyar Kaduna-Abuja 



 Masu garkuwa da mutane sun yi gaba da wani Dan Majalisar Tarayya


– Yanzu haka an nemi Dan Majalisar Sumaila da Takai an rasa


– Honarabul Durbunde ya fada hannun barayi






  • Masu garkuwa da mutane sun sace wani Dan Majalisa
  • Yanzu haka mu ke samun wannan labari
  • An dai nemi Dan Majalisar Jihar Kano ba a san inda yayi ba

Ba mamaki masu garkuwa da mutane sun yi gaba da wani Dan Majalisar Jihar Kano mai wakiltar Yankin Sumaila da Takai a Majalisar Tarayya. Yanzu haka dai NAIJ.com ke samun wannan labari maras dadi.

Ana dai samun karuwar masu garkuwa da mutane a Najeriya tun ba yau ba. Yanzu haka dai an nemi Honarabul Garba Durbunde an rasa yayin da yake hanyar komawa gida Kano daga Birnin Tarayya Abuja a daidai hanyar Jere jiya.


[NAIJ Hausa]

Dalilai 3 da su ka sa APC ke cikin matsala



Siyasa: Matsalolin da Jam’iyyar APC ke fama da su




– A cikin makon nan ne Gwamnatin Buhari ta shekara biyu da kafuwa


– Sai dai har yanzu Jam’iyyar APC ba ta samu alkibla ba


– Kamar dai PDP, Jam’iyyar mai mulki tana cikin rikici


Jam’iyyar APC na fama ta zama Jam’iyya mai mulki tun kafuwar Gwamnati. Shugaban Jam’iyyar da kan sa ya bayyana cewa ba haka su ka so ba. Ko daga ina aka samu matsala a Jam’iyyar? G




  • 1.      Rashin kudi

Jam’iyyar APC na fama da matsalar rashin kudi tun bayan hawan Shugaba Buhari mulki wanda ya toshe duk wata kafa da Jam’iyar za ta rika tatsa daga Gwamnatin Tarayya.
2.     


  • Nadin Shugaban kasa
Shugaban Jam’iyyar Cif John Oyegun ya bayyana cewa Jam’iyyar ba ta jin dadin irin nadin da Shugaban kasa yake yi. Mafi yawanci ba a tuntubar Jam’iyya da ‘Ya ‘yan ta. Sannan kuma har yanzu ‘Yan PDP na nan rututu cikin wannan Gwamnati rike da matsayi ba a sauya su ba.

  • .      Rikicin Majalisa da sauran na cikin gida

Tun wajen nadin Shugabannin Majalisa Jam’iyyar APC ta fara dabawa kan ta wuka a ciki. Yanzu dai kusan aikin gama ya gama kuma ana yi wa juna kallon doya da manja ne.





[NAIJ Hausa]

Turnuku fadan aljanu: Sojoji sun kashe Jami'an 'Yan Sanda


Rikicin ‘Yan Sanda da Sojoji bai yi dadi ba a Kalaba






Yadda rikicin Sojoji da ‘Yan Sanda ya ga bayan Jami’ai da dama



 – Sojojin Najeriya sun kai wa ‘Yan Sanda hari a Garin Kalaba


– Ba mamaki wasu manyan Jami’an ‘Yan Sanda sun rasa ran su


– Abin ya kai har an kona ofishin ‘Yan Sanda



  • Rikicin Sojoji da ‘Yan Sanda ya bar gawawwaki Jami’ai da dama
  • An yi fada ne tsakanin ‘Yan Sanda da Sojojin ruwa
  • Daga baya dai Sojojin sama da kasa su ka shigo ciki


Mun samu labari daga kafafe da dama cewa jiya da dare an yi wani mugun fada tsakanin ‘Yan Sanda da Jami’an Sojoji wanda yayi sanadiyar mutuwar ‘Yan Sanda da dama. Majiyar mu tace an fara rikicin ne da Sojojin ruwa daga baya sauran Sojoji su ka kutso ciki.

Wanda ya ji yadda abin ya faru cikin dare ya bayyana mana cewa an kona ofishin ‘Yan Sanda. Abin dai ya kai an bude barikin Sojoji kowa ya dauki manyan makamai inda aka shiga budawa ‘Yan Sandan wuta. An dai ce an harbi wani Sojan ruwa ne a hannu.



[NAIJ Hausa]

Tuesday, May 30, 2017

Liman ya kusa kashe mutane da doguwar salla






An yi doguwar sallar Tarawihin da ba a taba yin irin ta ba


– A azumin bana an yi sallar da ba a taba yin ta a Duniya ba


Alaranma Badr Zafar ya karanta Suratul-Baqara a Raka’a guda


– Jama’a da dama sun samu rauni kafin a kammala sallar



Ramadan: Yadda wani Alaranma ya karanta Suratul-Baqara a Raka’a daya


  • A Masallacin Ar-Razzak da ke Birnin Landan an ga wata doguwar salla bana.
  • Wani saurayi ya saukewa jama’a izifi kusan 5 a tashi guda domin nuna gwanewar sa.
  • Sai da wasu su ka kassara a cikin wannan salla.


A wani masallaci a Birnin Landan mun ji labarin cewa wani Alaranma mai suna Badr Zafar ya sauke Suratul Bakara mai ayoyi 286 a Raka’a guda ta wata sallar tarawihi. Sai da aka dauki sama da minti 3 wajen furta ayar farko kurum watau Alif-Lam-Mim.

Wadanda su ka halarci Sallar dai kamar yadda mu ka samu labari daga shafin Maniac Muslim, da dama sun samu rauni inda wasu su ka sare a gwiwa, akwai wani dan wasan kwallon Kwando dai da yanzu an ce ba zai iya kara komawa wasan ba. 



[NAIJ Hausa]

Monday, May 29, 2017

Ranar bikin murnar Damukaradiyya a Najeriya



Damukaradiyya a Najeriya: Hanyar da aka baro da inda aka kamo!



Damukaradiyyar Najeriya ta balaga a halin yanzu


– Sau biyu Soji na yin katsalandan a harkar siyasa


Tun daga 1999 farar hula ke mulkin kasar nan





Muhammad Malumfashi ya rubuta wannan  a yau da ake bikin murnar Damukaradiyya a Najeriya.


  • Yanzu dai ba shakka Damukaradiyya tayi karfi a Najeriya
  • A baya dai sau biyu Sojoji na kifar da Gwamnatin farar hula
  • An yi haka a shekarar 1966 da kuma 1983


Ka iya cewa Damukaradiyyar Najeriya ta balaga bayan an yi shekaru 18 ana bugawa babu tangarda. Ana kuma sa ran cewa abubuwa ma sai dai kyau kurum za su kara duk da cewa an fara jin kishin-kishin din juyin mulki, sai dai kamar 2010, babu inda yunkurin zai kai.

A rana irin ta yau Janar Abdussalami Abubakar ya mikawa tsohon shugaba a mulkin Soja Janar Olusegun Obasanjo mulki. Har yau kuma tana hannun farar hula inda mutanen kudu su kayi kusan shekaru 14 inda ‘Yan Arewa su ka yi mulkin shekaru 4.




Akwai maganar cewa Shugaba Obasanjo ya nemi ya zarce fiye da wa’adin sa, uwar-bari dai ta sa dole ya kakaba tsofaffin Gwamnoni Marigayi Ummaru ‘Yaradua da Goodluck Jonathan. Bayan rashin lafiya ta kashe Ummaru ‘Yaradua ne Jonathan ya dare mulkin kasar har ya zarce.

An samu hadakar Jami’iyyun adawa inda su ka yi kutun-kutun su ka tika Shugaba Jonathan da kasa. Jam’iyyar APC ta su wani Janar din, Muhammadu Buhari ta karbi mulki wanda kawo yanzu shugaban kasar da wasu tulin alkawuran da APC ta dauka na kwance. Tuni dai har wasu sun fara hangen 2019!



Saturday, May 27, 2017

Huduba kan Aure-Dr. Saeed Yunus



HUDUBAR JUMA’A DAGA MIMBARIN ITN-ZARIA




Huduba kan Aure-Daga Bakin Imam Dr. Saeed Muhammad Yunus


Assalamu Alaikum wa Rahmatul Lah,

Godiya ta tabbata ga Allah SWT wanda ya halitta mu daga rai guda. Muna shaida cewa babu abin bauta da gaskiya face Allah dai shi kadai, ba shi da ‘da ko mata ko tamka ko wani abokin tarayya ko mataimaki. Muna kuma shaida cewa Annabi Muhammad SAW, Bawan Allah ne kuma Annabi wanda ake koyi da Shi, tsira ta tabbata gare Sa da Alayen sa da Sahaban sa da wanda su ka bi tafarkin Su.
Jama’a mu kiyayi Allah mai girma mu ji tsoron Sa, mu kuma guji saba masa alhalin muna sane. Daga cikin abubuwan da Musulunci ya jawo hankalin Jama’a akai da kiyayewa shi ne abin da ya shafi Auratayya. Auratayya abu ne da ya shafi zamantakewa na Duniya da kuma Addini. A cikin aure akwai hikima madaukakiya da amfani bi-la-adadin da kuma ma’anoni manya-manya. Wani abu ne na tilas domin kuwa da shi ake gina gida da al’umma kuma da shi ne ake samun daukaka kuma a rufe idanuwa da farji. Da auratayya ne ake kara yawa, yayin da wani ya fita sai wani ya shigo. Ai aure ya isa ka ga aya daga ayoyin Allah, ai aure ayar Allah ce! Allah SWT yana cewa: Daga cikin ku Allah ya halitta maku matayen ku, domin ku samu natsuwa da soyayya da tausayi. Allah yace hakan lallai aya ce ga masu tunani. Allah ka sa mu cikin masu tunani.

Addinin Musulunci ya buga wani misali mai ban sha’awa da mamaki wanda ya nuna cewa ana samun aure ne ta hanyar iyaye kuma lallai a nemi albarka a cikin auren wajen sauwake shi. Daga ciki akwai wani hadisi da Imamu Ahmad da Bayhaqy su ka fitar daga bakin A’isha mai gaskiya ‘yar mai gaskiya RA tana cewa mafi albarka game da mata da kuma mafi girma ga mata su ne wadanda ba a wahala ba wajen auren su, watau ba a wahalar da mutum ba; ya samu sauki wajen auren su. Mu sani cewa wadanda ke wahalar da Jama’a, su ke daura nauyi game da auratayya, su na sabawa tsari na shari’a na Allah da Manzon sa Annabi SAW. Ya ‘Yan uwa ku sani cewa ya halatta Mace tace da Namiji tana son sa kamar yadda ya halatta Namiji ya ce yana son mace wanda shi ma ya fi sauki (dama Namiji an san shi wanda bai jin kunya ba, (ba wai bai da kunya ba)). Kuma don Mace tace da Namiji tana son sa, wannan an gani a lokacin Manzon Allah SAW wanda wata tace tana son Sa, amma dai bai ce bai so ba, sai ya nema mata wani Mijin. A takaice ya ku iyaye, ya halatta ku nemawa ‘Ya ‘yan ku Mata ko Maza, amma idan har wata ko wani tace ko yace ba ta ko ya so, don Allah ka da a matsa sai an yi aure, domin wannan yana haifar da fitina da bala’i iri-iri a doron kasa. Idan mutum yace bai son wani sai a hakura, aure dai ba za ayi ba! Domin Manzon Allah ya dukar da kan sa; don ba a san abin da zai biyo baya ba.

Akwai wasu matsaloli da su ke faruwa a yanzu wanda ya kamata a jawo hankali a game da su; matsala ta farko ita ce samari sun zama dika-dika, sun ki aure sun tsaya su na kakalo wasu abubuwa da ba su cikin Al-Kur’ani ko Sunnah, sai ka ga mutum ya cika shekara 40 bai yi auren fari ba. Ana makalewa da wasu dalilai marasa amfani yayin da Ubangiji SWT yace idan har kun yi aure don Allah kuna talakawa zai azurtaku daga cikin falalar sa (A cikin Suratun Nur). Abdullahi Dan Abbas yana cewa: Ku nemi wadatuwa cikin aure watau Idan ka na son kudi, sai ka yi aure. Amma fa ban fada maku cewa Hadisi ne na Manzon Allah SWT ba! Ban ce da ku Hadisi bane! Magana ce ta Dan Abbas wanda Sahabi ne da imanin sa ya cika har ya batse. Akwai wani Hadisin karya da ake cewa idan talauci ya addabi mutum to ya kara aure, to ai kuwa za ka kara talauci, ka kara lalacewa! Allah ka shiryar da mu!

Abubakar As-Sadiq RA babban Sahabi kuma Abokin Manzo SAW yana cewa Mutane: Ku bi Allah ku bi abin da ya umarce ku a cikin auratayya sai ya cika maku alkawarin ku. Kun ji Maza! Yace idan har kun bi Allah, zai cika maku alkawari. Ya ku ‘Yan Uwa akwai wadanda kuma kudi su ke nema da auren watau auren jari; ba za a nemi kowa ba sai ‘Yar mai kudi. Annabi SAW wanda ba ya karya yace duk wanda yayi aure don kudi, to karshen sa Talauci. Haka nan duk wanda ya dubi kyau kurum wajen aure wata rana zai ga matar ta kare mummuna har ta zama bai kaunar ganin ta-Akwala! Amma duk wanda yayi aure domin addini Allah Madaukaki zai cika masa burin sa. Amma Addini kuma bai hana idan mutum ya ga wata mai kyautatawa mutane kuma kyakkyawa ya aura ba, asali ma addini ya ba da dama ne. Daga cikin matsalolin da ake fama da su a yau shi ne rashin daraja masu addini, ana hana mata su auri mutanen kirki. Alhali fa Annabin Rahama SAW yana cewa duk wanda ya zo maku (neman aure), kuma ku ka yarda da halin sa da addinin sa to ku aura masa. Wadannan sharuda 2; ko da mutum yana kwana a masallaci amma bai da halin kirki bai cancanta ba, haka-zalika akasin haka. Amma fa ku sani cewa babu kamala sai Allah Mai Girma, domin ka da a ce ai yana da ‘yar matsala kaza a hana sa, kowa kuwa yana da ‘yar matsala. Allah ka shiryar da mu! Annabi SAW yake cewa idan ku ka ki aurar masa, za a samu fitina da barna da yawa a doron kasa, Tirmidhi da Ibn Majah da Hakim su ka fitar da wannan Hadisi da sanadi mai kyau.

Akwai wasu daga cikin Iyaye; Allah ya shiryar mana da su da ke cin amanar ‘Ya ‘yan da Allah ya dora masu. Su na hana ‘Ya ‘ya su auri wadanda su ka dace da su; Yarinya tayi karatu amma sai su aurar da ita ga wani ma-ci amana, su na neman mukami da matsayi da darajar wannan mutumi sun manta da darajar da Allah ya ba su. Daga cikin Iyaye akwai makwadaita wadanda su ke maida ‘Ya ‘yan su wasu kayan kasuwanci; ana cewa waye ya zo? Shin ya zo da mota? Wace irin mota? Allah ka shirye su! Wannan babban bala’i ne! Ina rahama ga wadannan iyaye da ba su tunanin aurar da Diyar su ga wanda bai da addini ba? Jama’a ina za mu je ne? Lahira fa za a tafi!

‘Abubuwan da ya zo mana a wannan zamani shi ne za a iya ba Likitocin mu dama su binciki lafiyar Ma’aurata. Domin musamman a auren zumunci a kan gaji rashin lafiya wanda wannan Littafin Tib-An-Nawawi ya tabbatar’. Ba mamaki a cikin zumuntar nan a samu cuta irin ta Sikila don haka Likitoci amintattu su yi bincike. Har da kuma sauran cututtuka na bala’i irin su Kanjamau. Ba haramun bane yin bincike wajen aurar da Budurwa ko Bazawara. Allah mu ke roko ya shiryar da mu da zuriyar mu!

Huduba ta biyu tana cewa bayan godiya ga Allah da yabo ga Annabin mu SAW wanda yake cewa yin aure na cikin Sunnar sa. Allah ka kara daraja ga farin Jakada Annabi Muhammadu SAW. ‘Yan uwa mu kara godewa Allah Ubangiji, a yau muna ganin abubuwa na lalata su na faruwa ga ‘Ya ‘yan Musulmi masu tsari. Wa ya haifar mana wannan bala’i kafin aure da bayan aure? Ya ku Al’ummar Manzon Allah SAW ku sani cewa da dama sun bar Sunna yayin da za su yi aure; ba a yin aure yadda Sunna tace; kawai ana haduwa ne yadda aka ga dama. Wannan yana haifar da fitina. Kuma ana yin barna wajen aure tare da almubazzaranci da alfahari da nuna an-isa, wanda hakan na sa Allah yayi fushi. Abincin da ake zubarwa a rana guda, na rantse da Allah sai wasu mutanen su samu na cin wata gudu. Abu na uku kuma shi ne cakuduwar maza da mata da kuma yadda Amarya da Ango ke fitowa gaban mutane; ka ga macen kirjin ta (har ma da sashen nonon ta) a waje a gaban wasu mutane sha’awa. Amarya tana rawa a gaban wani Makadi rike da hannun Angon ta. Jama’a ina koyarwar Annabi Muhammadu SAW? Idan abin ya cika, sai ka ga an kashe kudin gaske wajen haskawa a Talabijin. Sannan kuma ka ga ana daukar hotuna na haram wanda ba abin da wannan yake haifarwa sai fitina! Daga ciki akwai wasu wasanni na banza da ake yi; akwai wani zama na Party ‘Till-Dawn’ har gari ya waye a sa’ilin da Bayin Allah na kwarai ke neman gafarar Allah Madaukaki. Allah Tabaraka Wa Ta’ala yace su na neman gafara ga wasu can kuma su na ta lalata. A dalilin bikin aure sai a bar sallolin da aka farlanta don wai rana guda! Abu na biyar kuma, a kan cire rigar kunya. Ita ce kadai ranar da ake warewa Shaidan amma ban da ita kullum ta Allah ce, amma a ranar dai sai a dan huta; rai dangin goro. Ka ga an sa motoci da babura su na kara, ana tukin ganganci, wai duk ana murnar auratayya. Abu na karshe watau na bakwai shi ne cutar da samari da ‘yan mata da kowa game da abubuwan da ake ji na sauti a cikin Unguwanni da ke hana mutane ambaton Allah kuma yana jawo fitina a doron kasa.

‘Yan uwa wadannan abubuwan su na cikin abin da su ka jawo wasu matsaloli da mu ke fuskanta a yau. Daga cikin matsalolin da ake samu shi ne sai ka ga mata na tafiya tsirara; idan har ka yi magana sai a fada maka cewa ‘Ai Imani yana zuciya!’ Mata na cin amanar Mazajen su, su na rashin da’a ga Allah. Ubangijin Ka na nan a madaka! Lallai Ubangijin Ka bai manta ba!! Al’ummar Musulmi sun shiga rudu an manta da tafarkin Allah; sai ka ga yaro na tuka babur bisa titi yana goge tayan baburin dsr, sai ka tambaya ka ji ya aka yi a Ranar aure. Abu na uku kuma shi ne rashin ba iyali hakkin su na ciyarwa da sauran su; sai ka ga daga an yi albashi mutum ya raba kudin sa ga matan banza wadanda yake kwanciya da su ba matan sa ba. Wannan yana kawo bala’o’i wanda an bar hanya tun kafin aure. Ga batun sake-sake; daga yaro ya balaga ko bai da sana’a sai ace za ayi masa aure, kuma Jama’a su yarda. A kafin ranar aure a sabawa Allah haka a ranar, ga shi nan an haifi bata-gari. Daga cikin Manyan mu kuma sun goyi baya; ku dubi yadda Majalisar Dattawar da ya kamata su zama masu kafa doka su ke goyon-bayan wannan barna. Allah ka shirya su kuma Allah yana kallon ku Dattawa! Ko ku cika alkawarin da ku ka yi ko kuma Allah ya kama ku! Ban ce dukkanin su ba amma ku tuba don kuwa kun ci amanar Manzon Allah da al’umma kaf don kuwa zaben ku aka yi, amma a dalilin wani son zuciyar ku kun saba. Wai sai ace mutum guda ne ko 10 za su gyara kasa? Su suka hana ruwa gudu, ga masu tuki a kan hanya ba su da hankali. Wanda ba Likita ba yayi karyar Likitanci. Wanda ba Malami ba ya bude Makaranta! Kasa kuma tayi shiru. A ce mutum daya yayi gyara. Kai! Komai ka gani kurum hauka ne! Jama’a duk wannan matsalar ba komai ya jawo mana su ba Wallahi Auratayya ce; kar ka raba daya biyu; da aure yayi kyau, da abubuwa sun yi kyau. Lokaci ba zai bamu damar mu fadi irin abin da auratayya ta haifar na kirki ba. A haka za a haifi fitinanne, ya kuma tafi Majalisar ya zama Dan kuka. Allah ya shiryar da mu!

Abin da ya jawo aka wulakanta auratayya tun farko shi ne an bar Malamai na Allah an koma ga Malaman Duniya wadanda ba su ba da fatawar komai sai shirme. Dole mu yabi wadanda su ka bi hanyar Allah da Manzon Sa wajen Auratayyar su, Allah ka taimake su. Daga karshe muna ta’aziyyar babban Malamin Al-Kur’ani da ya rasu a Kano shekaran jiya watau Dakta Alhassan Sa’eed Jos. Allah ka masa rahama ka haskaka kabarin sa ka za ya zama dausayi na Aljanna ka sa Aljanna makoma ka cika burin sa ga Iyalin sa. Allah ka mana rahama gaba daya don mu ma muna tafe. Allah ka azurta mu da aminci a Najeriya ka taimaki dukannin Shugabannin mu. Allah ka karawa Shugaba Buhari lafiya da daukaka ka kuma gusar da damuwar sa da Makiyan sa ka watsa su. Allah ka sa mu cikin Bayin kwarai ka kuma taimake Musulmai da Musulunci. Allah duk wanda ba su da aure a cikin masallacin nan da wajen masallacin, Allah ka ba su, masu son karawa idan har alheri ne, Allah ka ba su dama! Ya Allah muna rokon ka wadanda su ka rasa maza ka ba su. Allah ka kawowa masu neman aure na kirki!



Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba.
(Malam ya gabatar da wannan huduba tun kwanaki, ban samu damar buga ta ba)

Muhammadmalumfashi@gmail.com          
Twitter: @Ya_waliyyi




Wednesday, May 24, 2017

Tsohon Shugaba Obasanjo na shirin zama Dakta


Obasanjo ya koma Makaranta; yana shirin zama Dakta


– Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya koma karatu


– Obasanjo ya fara Digiri na uku watau karatun zama Dakta


– Janar Obasanjo na karatun ne a Jami’ar NOUN






Tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya daura damarar zama Dakta. Olsuegun Obasanjo na Digiri na uku a fannin ilmin addinin kirista. Cif Obasanjo ya fadawa Malaman sa cewa idan bai yi kokari ba ka da su duba aikin sa.

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya koma Makaranta domin yayi karatun Digiri na uku inda zai zama Dakta idan har ya kammala. Yanzu dai har yayi nisa don kuwa ya gabatar da sharen fagen kundin da yake kokari yayi aiki a kai.

Cif Olusegun Obasanjo yana nazari ne a kan rashin cigaba da talauci a Yankin Arewa-maso-gabashin Najeriya a mahangar ilmin addinin kirista wanda a nan yayi Digiri na biyu. Tsohon Shugaban yace Malaman su tsaya su duba aikin sa da kyau.





[NAIJ Hausa]

Ahmed Musa ya auri Juliet bayan ya rabu da Jamila


Karamar magana ta zama babba: Ahmed Musa ya angonce da Juliet Ejue


 – Babban Dan wasan Super Eagles Ahmed Musa ya auri Juliet


– Dan wasan na Najeriya ya saki matar sa kwanaki


– An ji cewa matar tace sam ba za ta zauna da kishiya ba




Da alama Ahmed Musa ya auri sahibar sa Juliet. Dan wasan mai shekaru 24 ya shiga daga ciki. Kwanaki dai ya rabu da matar sa Jamila.

Ko ka dai har yanzu ba mu samu tabbaci ba amma ba mamaki babban dan wasan gaban Super Eagles Ahmed Musa ya auri Sahibar sa Juliet Ejue. Mun dai ga wasu hotuna da takwarar sa 'dan wasan Najeriya Juwon Oshinawa ya dora na yawo da ke nuna hakan.

Kwanaki dai Ahmed Musa ya rabu da uwar ‘ya ‘yan sa bayan yayi niyyar kara mata inda ta tubure tace ba za ta sabu ba. Mun ji cewa dai sun rabu bayan ya ba ta kyautar wata katuwar mota da gida a Kano.

Tun a Kano dai Ahmed Musa ya hadu da Jamila sai dai yanzu ya zama Angon Juliet wata mutumiyar Garin Kalaba na Jihar Kuros-Riba. Musa dai ya sayawa Juliet gida a Lekki da ke Legas da kuma zugegiyar Marsandi.



[NAIJ Hausa] 

Tuesday, May 23, 2017

Bam ya kashe mutane sama da 22 a Manchester


 
Shugabannin kasashe sun yi tir da harin da aka kai a kasar Birtaniya



– Shugabannin kasashe sun yi tir da harin da aka kai a kasar Birtaniya


– ‘Yan ta’adda sun kai wani mugun hari inda aka kashe Jama’a da dama


– Har yanzu dai ana zaman dar-dar a Garin Manchester




Wani ‘Dan ta’adda ya kai wani mugun hari a Garin Manchester na Ingila inda fiye da mutane 20 su ka mutu nan take. Mutane akalla 60 kuma sun jikkata a harin.

Wani Dan ta’adda ya kashe mutane 22 a wani hari da ya kai a Garin Manchester yayin da wasu da dama su ka samu rauni. Shugabannin kasashen Duniya irin su India, Japan, Canada, da Australlia dai sun yi tir da wannan mugun hari.

Shugabannin Jam’iyyu dai sun daga kamfen din zabe a dalilin hakan. Kungiyar ISIS ta Duniya dai ta fitar da sakonni inda ta ke murnar harin da aka kai. Abin dai ya faru ne ana wani shirin wasa na waka.



[NAIJ Hausa]

Monday, May 22, 2017

Kungiyar Real Madrid ta lashe gasar La-liga


Barcelona ta rasa kofin La-liga hannun Real Madrid


– Kungiyar Real Madrid ta lashe Gasar La-liga


– Real Madrid za kuma ta kara a kofin Turai


–Dan wasa Ronaldo ne ya fara jefa kwallo a wasan karshen





Real Madrid ta lashe gashe gasar La-liga karo na farko cikin shekaru wajen 5. Koci Zinedina Zidane ya dauki kofin sa na 4 a kulob din. Real Madrid ta daga kofin bayan ta doke Malaga jiya.

Real Madrid ce tayi nasara a Gasar La-liga bayan Ronaldo da Benzema sun jefa kwallo a wasan karshe da Malaga duk da Barcelona ta dawo ta ci wasan ta da Kungiyar Eibar. Tauraron Dan wasa Cristiano Ronaldo ne ya jefa kwallo a ragar Malaga ana take wasa.




Rabon Real Madrid din da kofin tun lokacin Koci Jose Mourinho wanda wannan karo ta gama da maki 90 kuma ta zura kwallo a kowane wasan da ta buga. Wannan ne dai kofin La-liga na 33 da Real Madrid ta ci.

Juventus ta isa zagayen karshe a gasar UEFA Champions League na zakarun Nahiyar Turai inda za ta kara da Real Madrid. Ita ma Juventus ta ci Gasar Seria A na kasar Italiya.





 [NAIJ Hausa]


Sunday, May 21, 2017

Shugaba Trump na Amurka zai saidawa Saudi makamai

An kulla yarjejeniyar makamai tsakanin Amurka da Kasar Saudiyya


 Shugaban kasar Amurka Trump ya kai ziyara kasar Saudi


– Kasashen sun shiga yarjejeniyar makamai na sama da Dala Biliyan 100


– Amurka da mukarabban ta na yaki a Yemen da ‘Yan Shi’a




Duk da irin maganganun da Donald Trump ya rika yi a baya abubuwa ba su canza ba. Kasar Amurka za ta cigaba da saidawa Saudiya manyan makaman yaki. Amurka dai ta nan ta ke samun makudan kudi.

Shugaba Donald Trump ya isa kasar Saudiya jiya inda aka kulla wata yarjejeniya na makamai na sama da Dala biliyan 110 wanda kuma nan da shekara goma za a kara sayan wasu na sama da Dala Biliyan 350.

Ba dai a ga maciji tsakanin Saudiya da kasar Iran, asali ma dai Saudiya na cigaba da yakar ‘Yan Houthi da ke Yemen wanda Kasar Iran ke marawa baya. Trump dai yana ma nema ya zarce Shugaba Obama wajen kawancan sa da kasar Saudiya.






[NAIJ Hausa]

Thursday, May 18, 2017

Shugabannin Afrika 5 da su ka fi shekaru



Shugabannin kasa da su ka fi kowa tsufa a Afrika



– A Nahiyar Afrika dai ana buga wani irin mulki


– Shugaban kasa Zimababwe Mugabe yana da shekaru fiye da 90


– Shugaban Najeriya Buhari kuwa ya fi shekara 73



Shugaba Muhammadu Buhari bai cikin shugabannin 10 da su ka fi tsufa a Afrika duk da kuwa ya zarce shekaru 70 a Duniya don kuwa akwai manyan sa.




1.      Robert Mugabe
Shekarun shugaba Robert Mugabe na kasar Zimbabwe 93 a Duniya ke nan duk Afrika babu shugaban da ya kai sa tsufa da kuma dadewa a Ofis watau shekaru 40.


2.      Beji Essebsi
Shugaban kasar na Tunisia ya haura shekaru 90 shi ma a Duniya wanda ya zo na biyu a jerin shugabannin da su ka sha miya.


3.      Paul Biya
Shugaba Biya na nan Makwabtan Najeriya watau kasar Kamaru ya zarce shekara 83 a Duniya kuma har yanzu ana damawa da shi.


4.      Abdelaziz Bouteflika
Shugaba Bouteflika na Algeria yana da shekaru 80 a Duniya kuma duk kasar Algeria babu shugaban kasar da ya kais a dadewa a mulki.


5.      Ellen Johnson Sir-Leaf
Tana cikin shugabannin kasa mata da ake da su a Duniya, Shugaba Ellen Johnson ta Kasar Liberia tana da shekaru 78 a Duniya.




[NAIJ Hausa]

Tuesday, May 16, 2017

Abubuwa sun fara sukurkucewa Donald Trump


Shugaba Trump bai jin dadin yadda abubuwa ke wakana a 'White House' 

 

Shugaban kasar Amurka Trump na shirin yin wani mugun garambawul


– Abubuwa su na kara cabewa Shugaba Donald Trump


– Wata Jaridar kasar waje ta bayyana wannan




Mun ji cewa Shugaba Donald Trump na Amurka bai jin dadin yadda abubuwa ke gudana a White House. Shugaba Trump dai bai gane yadda Gwamantin sa ke tafiya ba Hakan ta sa yake shirin canzawa Gidan Gwamnatin salo. 

Muna jin labari cewa shugaban kasar na Amurka Donald J. Trump zai kawo sabon sauyi a fadar shugaban kasa na White House bayan abubuwa sun fara sukurkuce masa. Ba mamaki irin su Micheal Dubke da Sean Spicer su tattara ina su-ina su.

Ana samun babbar matsala a game da yadda harkar yada labarai ke gudana. Kwanan idan ku na biye aka samu ‘yar kwamacala bayan da shugaban kasar ya sauke Shugaban Hukumar FBI ta kai ayi ta samun kwan-gaba-kwan baya.



[NAIJ Hausa]

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...