Friday, June 16, 2017

Falalar I’itikafi cikin karshen watan Azumi




Goron Azumi: Falalar I’itikafi a cikin watan Ramadan



  • Musulmai na azumi a fadin Duniya a cikin wannan wata
  • Akwai matukar lada ga wanda ya kebe a masallaci
  • Wannan kebewar ake kira I’itikafi a Addini



Akwai matukar lada ga wanda ya samu yin I’itikafi a cikin wannan wata. Manzon Allah SWT ya kan zauna a cikin masallaci yayi ta ibada. Ana so Musulmai su yi koyi da wannan ibada na Manzon Allah.

Yayin da ake azumin watan Ramadan yana daga cikin ayyukan lada shiga I’itikafi watau kebawa a Masallaci ba a wani aiki face salloli da karatun Al-kur’ani mai girma. A cikin Bukhari ya tabbata cewa Manzo SAW na yin I’itikafi a irin wannan lokaci na karshen Ramadan.

Akwai Hadisi daga Abdullahi ‘Dan gidan Abbas RA daga Manzo SAW da ke cewa duk wanda yayi I’itikafi a kwanaki goma na karshen Ramadan ba zai shiga wutar Jahannama ba. Wannan Hadisi dai Imam Tabarani ya kawo shi.




Ana shiga I’itikafi ne cikin watan Ramadan wanda aka fi ba karfi musamman a kwanaki goma na karshe. Sunnah ta tabbatar da cewa an fi so a shiga I’itikafi kafin rana ta fada kuma a fito da zarar an ce an ga wata watau kafin a shiga watan Eid.

Ana kuma I’itikafi ne a kowane Masallacin da ake Sallar Juma’a watau ba sai mutum ya fita domin zuwa Masallaci ba. Akwai dai Malamai irin su Nasir-Deen Albani da ke ganin Annabi SAW ya kayyade ga Masallatan nan uku mafi maraja.




[Muhammad Malumfashi ya fara rubuta wannan a NAIJ Hausa a matsayin goron Jumu'a]


Thursday, June 15, 2017

An koma saida dabinon da Saudi ta aikowa Najeriya sadaka




Abin kunya: Saudi ta aikowa Najeriya dabino sadaka amma an saida


  • Kasar Saudi ta aikowa Najeriya sadakar dabino na azumi
  • Sai ga shi yanzu ana saida wannan dabino a kasuwa
  • Ministar kasar da tayi alkawarin za a rabawa ‘yan gudun hijira




Wannan abin kunya sai ace da me yayi kama. Najeriya dai ta kara buga abin kunya a idon Duniya bayan an fara saida dabinon sadaka a kasuwa. An dai aikowa Najeriya sadaka amma an kai kasuwa domin a ci riba.

Kwanakin baya kun ji cewa Ofishin Jakadancin Saudiya a Najeriya ya bayyana cewa kasar ta aikowa Najeriya tulin dabino domin buda baki. Sai dai yanzu haka wannan dabino na yawo a kasuwa cikin Abuja ana saidawa.



Karamar Ministar harkokin kasar waje Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim tayi alkawari da fari cewa za a raba kayan ne musamman ga ‘Yan gudun Hijira da ke Yankin Arewa maso gabas sai dai ba haka abin ya kasance ba.

Gwamnatin Tarayya ta bakin Ma’aikatar harkokin kasar wajen ta ba Kasar Saudiya hakuri inda tace wasu bata-gari ne su ka yi gaba da dabinon bayan an kai inda ya kamata a raba su domin su samu abin Duniya.




[NAIJ Hausa]

‘Dan Najeriya ya kashe Biliyan 2 wajen auren 'Yar Iran



Yadda ‘Yar da ba kowa ba ta auri ‘Dan wanda ta fi kowa kudi a Duniya


  • Ko kana da labarin wata mata Folorunsho Alakija?
  • Alakija na cikin matan da su ka fi kowa kudi a tarihin Duniya
  • Kwanan nan ‘Dan ta ya kashe kusan Dala Miliyan 5 wajen auren sa








Folarin Alakija ya tada kusan Biliyan 2 wajen bikin aure. Folarin ya auro wata ‘Yar kasar Iran ce da ke zaune a Ingila. Asali Amaryar sa Nazanin ba ‘yar gidan kowa bace a Duniya. 

Folarin Alakija wanda ‘Da ne wajen matar da duk Duniya da wuya a samu bakar mace da ta taba kera ta dukiya ya auri Nazanin Jafarian Ghaissarifar wata ‘Yar asalin kasar Kasar Birtaniya. A bikin dai an kashe kudi sama da Naira biliyan 2.



Nazanin Jafarian tayi Digiri kan fannin likitanci da kuma wata difloma a harkar shari’a sannan kuma tana aikin kwalliya ne da gayu har ta kan yi aiki da Iyalan Kardashians da su kayi fice a Duniya. 

An yi wannan kasaitaccen biki ne a Fadar Blenhim da ke Garin Oxfordshire a Kasar Birtaniya. Asalin Nazanin dai ba masu wadata bane don kuwa Mahaifiyar ta sai da tsiyace ma bayan dawowar su Ingila inda su ke zaune hannun ubangiji.

Shekarun baya dai Mahaifiyar Angon Alakija ta zarce Attaajira Oprah Wimfrey ta Amurka kudi. Alakija mai shekaru 66 ta mallaki sama da Dala Biliyan biyu.





[Muhammad Malumfashi ya fara kawo wannan rahoto a NAIJ Hausa]


<script async src="//pagead2.googlesyndication.com/pagead/js/adsbygoogle.js"></script>
<script>
  (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({
    google_ad_client: "ca-pub-4526893122328023",
    enable_page_level_ads: true
  });
</script>

Wednesday, June 14, 2017

Kwanan nan Dan wasan Duniya Messi zai zama Ango


Kasar Argentina za ta cika makil a ranar bikin auren Messi



  • Auren Dan wasan Barcelona Lionel Messi ya karaso
  • Za dai a ga cincirindo a kauyen Dan wasan a Kasar Argentina
  • Dan wasan Real Madrid Morata zai yi aure wannan makon



Dan wasan Duniya zai yi aure: Kauyen su Messi zai yi irin cikar da bai taba yi ba


Cikin wannan watan dai ‘Yan wasa da dama za su yi aure. Kwanan nan Dan wasan da ke tsaron ragar Kungiyar Bayern Munchen watau Manuel Nueuer ya shiga daga ciki. Irin su Lionel Messi na shirin biyo shi kwanan nan. 

A karshen wannan watan Dan wasa Lionel Messi na Barcelona zai zama Ango a Birnin Rosario da ke Kasar Argentina. Messi zai auri sahibar sa da su kayi shekara da shekaru tare tun su na yara Antonella Roccusso.

Haka kuma 'Yan wasan Real Madrid har 3 za su angonece. Daga ciki Alvaro Morata zai auri Budurwar sa Alice Campello a wannan Asabar din mai zuwa. Haka ma Lucas Vasquez da Mateo Kovacic na Kasar Kuroshia. 

Kwanaki kun ji cewa babban Dan wasan nan na Real Madrid Cristiano Ronaldo ya samu jarirai tagwaye masu suna Mateo da Eve a Amurka. Ko da yake dai har yanzu kamar ba a san Mahaifiyar 'Ya 'yan ba kamar yadda har yau ba a sa wanda ta haifa masa 'Dan sa na farko ba. 





[NAIJ Hausa] 

Za a iya jefa Dan wasa Ronaldo a gidan yari




Ana zargin Dan wasan Real Madrid da laifin haraji


 – Ana zargin Dan wasan Duniya Ronaldo da laifin rashin biyan haraji


– Hukuma za ta tuhumi ‘Dan wasan da wannan babban laifi


– Akwai yiwuwar Dan wasan bai biya sama da Dala Miliyan 16 na haraji ba





Ana iya kama babban Dan wasa Ronaldo da laifin haraji. Haka dai aka yi da Dan wasa Lionel Messi. Duk 'Yan wasan Duniya babu wanda ya kai Dan kwallon karbar albashi a halin yanzu. 

Ana zargin Babban Dan wasan kwallon kafar nan na Duniya Cristiano Ronaldo da rashin biyan kudin harajin da ke kan sa na sama da Dala Miliyan 16. Kwanaki Kotu ta yankewa Lionel Messi daurin watanni 21 bayan an same sa da irin wannan laifi na kin biyan haraji.

Akwai zargin cewa Dan wasan bai bayyana asalin abin da yake samu ba wanda ta hakan ne ya biya kasa da abin da ya kamata ya Hukuma a matsayin kason haraji. Ronaldo dai na samun kudi ta wasu hanyoyin iri-iri ban da albashin sa irin su talla da kudin rigar wasa.



[NAIJ Hausa]

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...