Tuesday, February 21, 2017

Kiristocin Katsina sun yi wa Buhari addu’a


– Kiristocin Jihar Katsina suna ta addu’a domin ubangiji ya ba Buhari lafiya


– Kungiyar CAN dai ta fara fara azumi da salloli domin shugaban kasar


Shugaba Muhammadu Buhari yana Ingila tun-tuni




A Jihar Katsina mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari Kiristoci ne suka shiga addu’o’i dare da rana domin Ubangiji ya ba shugaban kasar lafiya. Kiristocin dai sun tashi ne da azumi da kuma addu’o’i domin shugaban kasar ya dawo aiki.

A Jiya Litinin dai Kungiyar CAN ta Kiristoci suka tashi da niyyar azumi har na mako guda domin Buhari. Kungiyar dai tana da ‘Ya ‘ya kusan 65,000 a Jihar Katsina. Kamar dai yadda muka samu labari daga Jami’an NAN masu dillacin labarai.

Kiristocin za su yi addu’a ne na musamman a manyan Cocin da ke Jihar, kamar su Cocin da ke Kofar Kaura da dai wasu da ke cikin gari. Kiristocin suka ce addu’ar su shugaba Buhari ya samu sauki ya dawo ya cigaba da aikin gyaran da ya faro.

'Yan Kungiyar Jama'atu Nasril Islam dai su ma sun dage da yi wa Shugaba Buhari addu'a. A Jihar Borno kuwa, sai sauke Al-Kur'ani ake yi. 



[NAIJ Hausa]




An sace wani babban Soja a Legas


– An sace wani babban Jami’in Soja a Garin Legas


– A jiya ne dai aka nemi wani Laftanan Soji aka rasa


Babu mamaki masu garkuwa da mutane suka yi gaba da shi





A jiya Litinin ne aka nemi wani babban Jami’in Sojan Najeriya aka rasa a Garin Legas. Wannan abu dai ya faru ne a Yankin FESTAC da ke Garin Legas da yammacin jiya. Ana zargi masu garkuwa da mutane ne suka sace Sojan.

Duk da cewa kwanan nan Gwamna Ambode na Jihar ya shigar da dokar harbe duk wanda aka kama yana satar mutane da alamu wasu ba su koyi hankali ba tukun. Wasu bata-gari ne dai suka kai hari ga Rundunar Sojin yayin da suke wucewa, bayan nan aka nemi wani Soja aka rasa.

Yanzu haka an shiga neman wannan Soja da aka bayyana da Laftana Diya a Yankin na Unguwar FESTAC, Sojoji da sauran Jami’ai sin hargitsa wurin da harbe-harbe da sauran cikin bacin ran ‘dan uwan su da suka nema suka rasa.

Kwanaki ne kuma Mutanen Garin Agatu na Jihar Benuwe su ka tsokano tsuliyar dodo idan har ba ayi wasa ba, don kuwa sun kashe wani Sojan Najeriya kwanan a wata hatsaniya da aka yi tsakanin mutanen Garin da Jami’an tsaro. Sai dai sun nemi a yefa masu kuskuren na su.


[NAIJ Hausa]

Monday, February 20, 2017

Babu wanda ya isa ya karbe mani daloli na-Andrew Yakubu


Hukumar EFCC ta karbe kusan Dala Miliyan 10 daga hannun Andrew Yakubu


Tsohon Manajan NNPC Andrew Yakubu yace dole a maido masa kudin sa


Andrew Yakubu ya dai ce ba satan kudin yayi ba



Kwanakin baya wani babban Kotun Tarayya da ke Garin Kano ya bada dama Gwamnatin tarayya ta rike makudan kudin da aka samu daga gidan Tsohon Manajan Kamfanin main a Najeriya watau NNPC Andrew Yakubu.

Sai dai tsohon shugaban NNPC din ya nemi Kotu tayi watsi da hukuncin da aka yanke a baya kurum a maido masa kudin sa. Lauyan Andrew Yakubu yana karar Kotun da ta yanke shari’ar a baya yace babu wanda ya isa ya taba masa kudin sa.



Lauyan da ke kare Andrew Yakubu, Ahmed Raji SAN yace ana zargin Andrew Yakubu ya saci kudin ne a Birnin Tarayya Abuja don haka wata Kotu a Garin Kano ba ta isa tace za ta karbe kudin ba kamar yadda dokar kasa tace.

Kwanaki ne dai Hukumar EFCC ta samu wasu mahaukatan kudi kusan Dala Miliyan 9.8 a gidan tsohon Manajan Kamfanin NNPC din na kasa. Andrew Yakubu dai yayi wuf yace duk kyaututtuka ne aka rika kawo masa lokacin yana Ofis.


[NAIJ Hausa]





Likitoci sun fadawa shugaba Buhari ya huta


– Da alamu Likitocin Ingila sun fadawa shugaba Buhari ya huta tukun


– An ba sa wannan shawara ne saboda lafiyar jikin sa


Yanzu haka dai Farfesa Osinbajo ke rike da kasar nan




Mun samu kishin-kishin din cewa Likitocin da ke kula da lafiyar shugaba Muhammadu Buhari a kasar Ingila sun fadawa shugaban kasar da ya rabu da mulkin kasar nan har sai ya samu sauki nan gaba.

Likitocin dai sun ba shugaba Muhammadu Buhari wannan shawara ne saboda ya kula da lafiyar jikin sa kamar yadda muke samun labari daga wata Majiya daga Jaridar Sahara Reporters ta kasar da ke Amurka.

Sai dai wasu na kusa da shugaban kasar suna kokarin ganin shugaba Muhammadu Buhari yayi watsi da wannan shawara na Likitoci ya dawo kurum ya cigaba da rike madafan iko na kasar. Ba mamaki Likitocin dai sun gargadi shugaba Buhari game da dawowa ba tare da ya kammala ganin Likita ba.


Yanzu haka dai Mataimaki Farfesa Yemi Osinbajo ke rike da kasar tun tafiyar shugaba Buhari Ingila.  An fara cewa dai har shugaban kasar ya fara rage nauyi saboda rashin lafiyar da ke damun sa wanda har yau ba a san menene ba. Mun samu labari dai cewa Shugaba Buhari ya kara ganawa da Bukola Saraki jiya a Landan.




[NAIJ]

Sunday, February 19, 2017

Yaushe Dujjal zai bayyana?



Me ka sani a game da Dujal?




Ya tabbata dai a hadisai na Manzon Allah SAW cewa Dujjal zai bayyana a can karshen Duniya. Ko wanene Dujjal? Yaushe zai zo? Ya za ayi da shi?

Dujjal dai zai zo a karshen Duniya ya kuma kawo fitina babba kamar yadda Annabi SAW yayi bayani. Dujjal zai do ido guda yayin da dayan yake kuma a shafe, sannan a gaban goshin sa an rubuta ‘kafir’ da larabci. Haka Dujjal zai keta Duniya cikin ‘yan kwanaki kadan.

Dujjal dai zai rika tafiya da Jama’a wadanda suka yi imani da shi, wadanda suka kafirce masa kuma yayi masu barazanar azaba. Kai har dai na kabari bai tsira ba daga wannan mugun halitta. Saboda haka ne Manzon Allah yayi umarni da haddace da karanta Suratul Kahfi a cikin Al-Qur’ani.

Dujjal dai yana daga cikin alamomin karshe na tashin kiyama, tare da Mahadi da kuma Annabi Isa wanda zai dawo nan gaba kamar yadda Hadisai suka nuna. Zai zagaye Duniya kaf ban da kasar Makka mai tsarki.

Wata rana ne dai Annabi Isa AS bayan ya dawo Duniya zai isa wani wuri tare da sauran Musulmai sai ya iske Dujjal a wani Gari mai suna Lud kusa da Garin Tel-Aviv sai ya jefa masa mashi ya kashe sa.
Allah yayi mana gab-da-katar daga sharrin Dujjal. Ameen.


[NAIJ Hausa]

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...