Saturday, November 26, 2016

Hudubar Jumu’a Masallacin ITN: ASARAR LOKACI


Hudubar Jumu’a daga Masallacin I.T.N Zangon-Shanu, Zaria

Daga Bakin Malam Farfesa Ibrahim Ahmed Aliyu




Asslamu Alaikum.

Bayan haka:

‘Yanuwa Musulmai, ‘lokaci’; Lokaci yana da muhimmanci, lokaci shine rayuwa, kamar yadda Hasan Al-Banna ya fada. Lokaci ya fi komai tsada, lokaci ya fi Zinari da Azurfa da Lu’u-lu’u... Wadannan abubuwa masu karewa ne, amma lokaci shine rayuwa, duk wanda ya bata lokaci, bangare na rayuwar sa ya bata. 

Laifin da ya fi kowane laifi a Musulunci shine wanda za ayi ta hanyar bata lokaci. Laifin bata lokaci yafi laifin barnar dukiya. Muna ganin Al’ummar mu tana bata lokaci a banza, lokaci ya zo, ya wuce ana wasanni. Yawancin mutane ba su yin abin da ya dace da lokaci. Da dare, wasu su zauna ba su wani abu. Da rana kuma suna zaman banza da wofi, ana hira, ana zancen banza da na sabon Allah; ana cin mutuncin mutane, ana kuma yi da su. Har wadanda ke wajena aiki ba su tsira ba. 

Saboda haka lokaci yana da matukar amfani a Musulunci, don hakane Allah ya rantse da lokaci da bangarorin lokaci kamar su Alfijir, walaha, dare, da wuni. Meyasa Allah yayi wannan rantsuwa? Saboda Allah ya nuna mana muhimmancin wannan abu. 

Lokaci kamar takobi ne, idan har kai ba ka yanke shi ba, ya yanke ka. Saboda lokaci yana aiki a kan ka, kamar yadda Umar dan Abdul Azeez ya fada. Hakika lokaci yana aiki a kan ka kai mutum, kai ma kayi aiki a cikin sa. Ma’anar suna aiki a kan ka shine suna rage maka tsawon rayuwar ka. Duk wani sabon abu, lokaci zai maida sa tsoho. Duk abin da ke nesa, lokaci zai kawo sa kusa. A kullum lokacin mu ne yake tafiya da wani bangare na rayuwar mu. Kamar yadda Hasan Al-Basri yake cewa, ya kai ‘Dan Adam, kai ba komai illa tari na lokaci, lokaci ne aka tara ya zama kai. Saboda haka duk wata rana da ta tafi, wani bangaren ka ne ya tafi. Don haka, ka da ka jinkirta aikin yanzu zuwa dare, ko kuma aikin yau zuwa gobe. Malalaci ne kawai yake yin wannan, amma Musulmai a yau sun zama masu kasala,’yan zaman kashe wando. Muna cewa da sannu zan yi kaza. 

Ka da mutum ya zama yana cewa da sannu zan yi kaza, nan gaba zan tuba…ya aka yi ka san cewa za ka rayu zuwa wannan lokaci? Wa ya lamunce maka rayuwar ta ka? An ce maka za ka rayu zuwa wannan lokaci ne bayan kana da wannan dama a yanzu? Ko waya fada maka cewa idan ka fito daga gidan ka, za ka koma? Wa ya tabbatar maka da cewa tufafin ka, kai ne za ka tube su, ba mai wankan gawa ba?  

Saboda haka ya wajaba mu yi wa kan mu hisabi, mu ga me ya dace mu cigaba da aikatawa. Magabatan Malamai su kan ce; duk wanda yau din sa ta zama kamar jiya, kamar yana ciniki ne yayi asara, wanda kuma yau din sa ta fi jiya sharri, wannan la’ananne ne. Sai mu roki Allah ya fitar da mu daga cikin masu asara da kuma la’anannu. 

Muyi kokari mu tashi tsaye, muyi aiki wurjanjen domin mu samu Aljanna da ta fi kowace. Kamar yadda aka ruwaito Manzon Allah SAW yana cewa idan za ku roki Aljanna ku roki Aljannar Firdausi. Muna rokon Allah ya azurta mu da Aljanna Firdausi. 

Ya wajaba a kan mu, a wannan tsayuwa da muka yi, a wannan lokaci, mu gane abin da ya kufce mana, wanda ba mu aikata ba. Mu san kimar lokaci, da wannan rayuwa da Allah ya mana ni’ima da ita, za a fa yi mana tambaya a game da abin nan duka a Filin Tashin Kiyama, domin ya zo a wani Hadisi Ingantacce da Bazzar da Tabarani suka ruwaito. Sai an tambayi Dan Adam, a kan me ya gudanar da rayuwar sa; samartakar sa da kuruciyar sa, dukiyar sa, da Ilmin sa. Guda biyu daga cikin su, sun shafi lokaci ne. Annabi SAW yayi wa’azi yake cewa ku ci gajiyar abubuwa 5 kafin abubuwa 5 su same ku. Ka ci gajiyar samartakar ka kafin tsufa ta same ka. Lafiya, kafin rashin lafiya ta same ka. Wadata kafin talauci ya zo maka. Kana da lokacin yin abubuwa, kayi amfani da lokacin kafin abubuwa su sha kan ka. Rayuwar ka gaba daya kafin mutuwa ta zo maka. A lokacin Samartaka ne mutum yake da karfin ikon aiki ga Musulunci. Ka da mutum ya bata kuruciyar sa. Haka lafiya babbar ni’ima ce, ya kamata mutum yayi amfani da lafiyar sa wajen aikata alheri. Haka nan kuma mutum yayi amfani da wadatar sa ta hanyar alheri kafin talauci ya zo. 

Ba ana nufin mutum ya zama yana cikin Sallah da Zikiri a kodayaushe ba, A’a gaba dayan rayuwar Addinin Musulunci, ibada ne. Amma mutane ba su san kimar rayuwa ba har sai lokacin da Mala’ikan mutuwa ya zo zai karbi rai, a lokacin ne mutum zai rika neman ina ma a jinkintar masa kamar yadda Allah SWT yayi bayani a cikin Ayoyi. Saboda haka lokaci abu ne mai tsada kwarai, abu ne mai darajar gaske, domin lokaci idan har ya tafi ba ya dawowa. Kamar yadda Hasan Al-Basri ya fada. Muna rokon Allah ya bamu ikon amfani da lokacin mu ba tare da mun yi almubazaranci ba.

  
Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga Zaria.

Friday, November 25, 2016

Atiku Abubakar ya cika shekaru 70

An taya Atiku murnar zagayowar Ranar haihuwar sa

– Tsohon mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya cika shekaru 70 da haihuwa

 

– Jam’iyyar APC ta taya Atiku murna, tace sune Najeriya

 

– Tsohon mataimakin Shugaban Kasan yayi hidima wajen inganta rayuwa da siyasar al’umma

 


Tsohon mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya cika shekaru 70 a duniya, Jam’iyyar su ta APC ta taya sa murnar wannan rana. APC tace ba zai yiwu a rubuta Tarihin Najeriya ba tare da sunan Atiku ba. 

APC tace Atiku Abubukar ya inganta rayuwar ‘Yan Kasar nan ta fannin mu’amala, zaman siyasa, tattalin arziki da cigaban al’umma. APC tace Atiku mutum ne wanda aba ruwan sa da bambancin kabila ko yare.

A sakon taya Atiku Abubakar din murnar zagayowar Ranar haihuwar sa, Jam’iyyar APC ta roka masa karin shekaru cikin koshin lafiya da arziki, Shugaban Jam’iyyar ne dai ya aika da wannan sako. APC tace alherin Atiku ya taba kowa a Kasar nan.

Haka kuma dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya Atiku Abubakar din murnar zagayowar wannan rana ta haihuwar sa, Shugaba Buhari ya taya Atiku shigowa sahun ‘Yan Saba’una irin sa.


Thursday, November 24, 2016

Ka san wanene Angon Zahra Buhari?


Ko shin wanene sabon sirikin Buhari?

– Diyar Shugaba Muhammadu Buhari, Zahra za ta auri dan Gidan hamshakin Attajirin nan, Muhammad Indimi

 

– Muhammadu Indimi kasurgumin Attajiri ne a Kasar Borno

 

– Ahmed Indimi yana daga cikin ‘Ya ‘yan wannan mai kudi

 

Ana ta samun rahoto cewa Diyar Shugaban Kasa, Zahra Buhari za tayi aure nan da kwanaki kadan masu zuwa. Zahra Buhari dai tayi fice ko a cikin ‘ya ‘yan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Mun kawo maku bayani, ko shin wanene wannan sabon sirikin na Buhari?

Ahmed Indimi yayi karatun share fagen Digiri a Legas, a wata Makaranta ‘Global International’, daga nan ya wuce Jami’ar InterContinental ta Amurka da ke Atlanta domin yin digiri na farko a Bangaren Fasahar Komfuta da bayanai.




Ahmed Muhammad Indimi shine Shugaban Kamfanin ‘Oriental Energy Resources’ masu harkar Man fetur. Ahmed Indimi dai saurayi ne kyakkyawa kuma son kowa. Sannan Ahmed yana da ban dariya da kuma son dariya. 

Ahmed Indimi mutum ne mai son karatun tsiya, bayan yayi digiri, ya koma yayi digiri na biyu kan harkar kasuwanci da ake kira MBA game da Harkar tsaron yanar gizo a Jami’ar nan dai ta Amurka. A wannan Makaranta ya rike matsayin Ma’aji na Kungiyar dalibai, Tun shekaru uku da suka wuce kuwa, Angon Zahra ya ba Miliyan dari baya. Kyaun da ya gaji uban sa, Ahmed Muhammad Indimi. Ko ba a fada maka ba, daga jin sunan Indimi, ka san kuwa akwai 'dimi'

[Karanta NAIJ Hausa domin samun kayatattun labarai]

Wednesday, November 23, 2016

Babban Dan wasan duniya 'Neymar' zai shiga kurkuku


Dan wasan Barcelona, Neymar za shi gidan yari?


– Shegen Dan wasan nan na Kungiyar Barcelona zai iya shiga Gidan Yari


– Neymar ya shiga matsala game da cinikin sa zuwa Barcelona shkearu 3 da suka wuce


– Dan wasan na Brazil, Neymar Jr. na iya kwashe shekaru biyu a Gidan maza




Hatsabibin matashin Dan wasan nan na Kasar Brazil, Neymar Jr ya shiga cikin babbar matsala a halin yanzu. Dan wasan na iya zarcewa kurkuku idan ba ayi wasa ba. Hukumar Kasar Spain suna kira da a daure Dan wasan inji BBC.

Akwai hannun Dan wasan a wata badakala cikin cinikin sayan sa da aka yi daga Kungiyar Santos zuwa Kungiyar Brazil shekarun baya kadan da suka wuce. Ana dai zargin dan wasa Neymar Jr. da Mahaifin sa da laifi.

Alkalin shari’ar, Jose Perals ya jaddada cewa dole a kama Tsohon Shugaban Kungiyar ta Barcelona, Sandro Rosell. Mista Rosell ne dai ya sayo Dan wasan daga Kungiyar Santos zuwa Barcelona a shekarar 2013.

Shekaru biyu da suka wuce ne dai dole ta sa Sandro Rosell ya sauka daga matsayin na sa saboda laifin da aka kama sa da shi. Ana zargin rashin gaskiya wajen cinikin dan wasan Neymar da aka saya kusan Miliyan €60.

Ta sayar da abinci domin dan ta yayi karatu

Kaji abin da wata uwa tayi domin ta tura yaro makaranta

– Wani mutumi ya jinjinawa mahaifiyar sa da irin kokarin da tayi


– Uwar sa ta sayar da abinci na shekara da shekaru domin ganin dan ta yayi karatu

 

 
 
Wani mutumi ya jinjinawa Mahaifiyar sa domin irin namijin kokarin da tayi da shi domin yayi karatun boko. Wannan matashi yayi amfani da kafar watsa labarai na zamani domin gudumuwar da ta ba sa a rayuwa.

Wannan matashi mai suna Tochukwu Ebeh yace uwar sa ta aika sa Makarantar boko tun daga Makarantar kafin firamare, zuwa Firamaren har zuwa Makarantar gaba da Sakandare. Mahaifiyar wannan matashi ta kasance tana dafa abinci ne a gefen titi.

Wannan mata dai tayi shekaru 30 tana sana’ar abinci, da haka ta biyawa dan nan na ta kudin makaranta. Tun daga Ajin Nursery har ya kammala Sakandare inda ya rubuta jarrabawar WAEC. Wannan yaro dai yace uwar sa ce uban sa.

A jiya kuma wani matafiyi mai suna Abubakar Duduwule ya shirya yin tattaki tun daga Garun Kaduna zuwa Kasar Ingila. Abubakar zai bi ta Jihar Neje ne, daga nan sai Garin Abuja, sai ya zarce har Kasar Birtaniya, inda zai tsaya. Kuma dai zai yi wannan tafiya ne duk a kafa.

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...