Thursday, February 2, 2017

Babban dan wasa ya ajiye kwallo




Babban Dan wasan nan na Ingila Frank Lampard ya ajiye wasan kwallon kafa bayan yayi shekara da shekaru ana gwabzawa da shi. Lampard dai ya dauki fiye da shekaru 20 yana taka leda a Kasar Ingila da kuma Amurka.
Lampard ya fara bugawa Chelsea tun a shekarar 2001 bayan ya baro Kungiyar West Ham, sai da ya kai har shekaru fiye da goma a Kungiyar. Frank Lampard ya kuma bugawa Kasar sa ta Ingila kwallo na kusan shekaru 15.
Dan wasa Lampard ya kafa tarihi inda ya fi kowa cin kwallaye a Chelsea, Lampard duk da dan wasan tsakiya ne ya ci wa Chelsea kwallayen da ba a taba samun irin su ba. Lampard ya zurawa Chelsea kwallaye 211; wanda ya fi na duk wanda ya taba bugawa Kulob din.
Lampard ya sanar ta Facebook cewa daga yanzu ya aijye tamula yana kuma mai alfahari da sunan da yayi. Lampard ya ci kwallaye kimanin 300 a fadin wasan rayuwar sa. Da alamu Lampard zai dawo bangaren horas da ‘Yan wasa. Lampard yayi ritaya yana da shekara 38.

Wani matashi ya rataye kan sa a Kano



 Wani matashi ya kashe kan sa Garin Kano


– Wannan abu ya faru ne a Karamar Hukumar Gezawa


Ko me ya kawo wannan? Duniya ce ta masa zafi




Mun samu labara daga Jaridar Daily Trust cewa wani matashi ya rataye kan sa har Lahira a Garin Kano. Har yanzu dai ba za a iya cewa ga dalilin da ya sa wannan matashi ya aikata wannan mugun abu ba.

An dai gane wannan matashi mai suna Nura kuma har a lokacin da aka samu wannan labari kafafun sa na lilo a bisa bishiyar sa ya rataye kan sa. Matashin ya rubuta sunan sa ne a wurin kafin ya kashe kan san.

Wannan abu dai ya faru ne a Garin tsamiya da ke cikin Karamar Hukumar Gezawa na Jihar Kano. Wanda yake wurin yace babu wanda ya san mai yayi wa wannan matashi zafi, sai dai aka iske gawar sa tare da casbaha da riga da wasu komatsen sa.


[NAIJ Hausa]

An gano maganin Kanjamau a Najeriya



– An gano maganin cutar nan ta Kanjamau a wata Jami’a da ke Najeriya


Farfesa Maduike Ezeibe na Jami’ar Michael Okpara ta Jihar Abia yayi wannan bincike


Shugaban Makarantar ya bayyana haka a jiya



Idan dai ta tabbata Najeriya za tayi kudi da wannan magani


Bayan shekara da shekaru ana bincike wani Farfesa mai suna Maduike Ezeibe a Jami’ar koyon aikin gona ta Michael Okpara ya gano maganin cutar nan da ta gagari mutane watau Kanjamau. A Turance kuma ana kiran ta HIV wanda ke zama AIDS idan ta rika.

Shugaban Jami’ar da ke Garin Umudike na Jihar Abia ya bayyana haka bayan ya tara manema labarai. Farfesa Francis Otunta yayi ikirarin cewa wani Malamin Makarantar ya gano maganin cutar da ke karya garkuwar jiki.

Farfesa Maduike Ezeibe da yayi wannan bincike dai yayi bayanin matakan da ya bi, da kuma sakamakon da ya samu. Yayi amfani da sinadarin Aluminium Silicate da kuma Magnesium Silicate. Sai dai abin da ban mamaki musamman dai tun da Farfesa Ezeibe Likitan dabbobi ne, ita kuma Kanjamau garkuwar jikin Dan Adam ta ke karyawa.

Kwanaki Jaridar Huffington Post ta rahoto cewa yanzu haka an samo maganin Kanjamau kuma har an yi wa wani ma’aikaci a Kasar Birtaniya magananin wannan cuta, kuma ya warke.


[NAIJ Hausa]

Amarya ta mutu bayan mako uku da aure


 Wata Amarya ta rasu makonni uku bayan an daure mata aure


– Amaryar ta rasu tana da juna biyu


Asali ma dai ta rasu ne bayan nakuda





Wani abin tausayi ya faru kamar yadda muka karanto a shafin Facebook. Wata Amarya dai tace ga garin ku nan, duka-duka ba ayi wata guda da yin auren ta ba. Wannan Amarya dai ta rasu jim kadan bayan an daura auren ta.

Wata kawar Amaryar mai suna Princess Nkiru ce ta bayyana haka yayin da ta ke mata ta’aziya a shafin ta na Facebook. Nkiru Momah tace dama can Amaryar tana da juna biyu, sai ga shi ta cika wajen haihuwar ‘da.

Kawar Marigayiyar tana mai kokawa da jimami da ce: ‘Dama na kwarai ba su dadewa.’ Har yanzu dai tana jin abin kamar a mafarki. An daura auren wannan Budurwa mai shekaru 23 a Watan Disamba, ta kuma haihu a Ranar 11 ga Watan Junairu, sai dai jim kadan bayan nan ta ce ga garin ku nan.

Haka kuma kwanaki dai wani Ango daga Garin Katsina ya rasu shi ma ba a dade da daura auren sa ba. Allah ya bada ikon hakuri. 



[NAIJ Hausa]

Wednesday, February 1, 2017

Dubu ta cika: Ana cigiyar wasu Ma’aikatan Kwastam


– Hukumar Kwastam na neman wasu Ma’aikatan ta ruwa-a-jallo


– Wadannan Jami’ai biyu suna da hannu wajen shigo da wasu tarin makamai


– Duk wanda ya ga wadannan Jami’ai ana bukatar ya nemi Hukuma






Hukumar Kwastam ta sanar da cewa tana neman wasu Ma’aikatan ta guda biyu ruwa-ajallo. Wadannan Ma’aikata suna da hannu wajen shigo da wasu tarin makamai cikin Kasar ta hanyar Legas.

Idan ba a manta ba Ranar Lahadi ne Hamid Ali wanda shine Shugaban Hukumar ta Kwastam din ya bayyana cewa an samu datse wasu kwalaye dauki da tulin bindigogi. An dai samu sababbin bindigogi har guda 661 fil a cikin kwali ana neman a shigo da su cikin Kasar.




Yanzu haka dai Hukumar Kwastam na neman Ma’aikatan na ta biyu da ke da hannu wajen shigowa da wadannan makamai; Abdullahi I da kuma Odiba Haruna Inah. Ana neman duk wanda ya gan su ya hanzarta ya sanar da Hukumar Kwastam.

Tuni dama dai aka kama mutane 3 da ke da hannu wajen shigo da makaman daga ciki akwai wanda ya shigo da su cikin Kasar Oscan Okafor da kuma wasu; Mahmud Hassan da Sadique Mustafa.


[NAIJ Hausa]







Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...