Thursday, December 8, 2016

Majalisa na nema a kafa Kotun Ikiliziya


Majalisa ta kawo kudirin kafa Kotun Kirista a Kasa




– Wani Dan Majalisa ya kawo kudirin kafa Kotun Kirista a Najeriya

 


– Yanzu har wannan kudiri ya tsallake mataki na biyu

 


– Hon. Gyang Dung na mazabar Plateau ya kawo wannan kudiri


 

Wani Dan Majalisa Wakilai ta Tarayya mai suna Hon. Gyang Dung daga Jihar Plateau ya kawo wani kudiri zuwa Majalisar Kasar inda yake nema a kafa Kotun Kirista a fadin Kasar nan. Watau dai wannan zai yi daidai da kamar Kotun Shari’ah na Musulunci.  

Yanzu dai haka wannan kudiri na kafa Kotun Ikilisiya ya samu tsallake mataki na biyu a Fadar Majalisar. Hon. Gyang Dung na PDP da ke wakiltar mazabar Plateau ne ya gabatar da kudirin tare da wasu ‘Yan Majalisa 8. 

Dan Majalisan yace idan har an kafa wannan Kotu, za ta zama tana aiki musamman ga abubuwan da suka shafi Addinin Kirista. Hon. Dung ya bayyanawa manema labarai cewa Kotun ba za tayi aiki a kan wanda bai yadda da Ikiliziya da Addinin Kirista ba. 

Sai anyi wa dokar Kasar nan garambawul dai kafin a shigar da wannan kudiri cikin dokar tsarin mulkin Kasa.

[NAIJ Hausa]


Wednesday, December 7, 2016

Anya Shugaba Buhari na iya zarcewa?

– Shugaba Buhari zai fuskanci babban barazana idan ya nemi zarcewa zaben mai zuwa

 

– Jam’iyyar APC mai mulki ta shiga cikin wani hali 

 

– Akwai yiwuwar a kafa sabuwar Jam’iyya a Kasar

 

2019: Shugaba Buhari na cikin matsala


Da alamu ana shirin kafa wata sabuwar Jam’iyyar gangami a Kasar, hakan dai ba karamin kalubale ne zai zama ga Shugaba Buhari idan har yana da shirin tazarce a zabe mai zuwa. Yanzu haka Jam’iyyar APC tana cikin wani hali. 

Tun farko dai Jam’iyyar ta samu matsala wajen zaben Shugabannin Majalisa, Shugaban Kasa yayi tsit har sai da abubuwa suka rincabe. An samu rikici tsakanin Bola Ahmed Tinubu da kuma Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki. Hakan ya kawo matsala tsakanin Majalisa da Shugaba Buhari.

Har wa yau ana ganin akwai wasu da ke kokarin katange Shugaba Buhari da Jama’an sa, musamman wadanda suka yi masu yakin neman zabe irin su Asiwaju Bola Tinubu. Ta wani gefen kuma wasu na kokarin hada fada tsakanin Shugaba Buhari da shi Bola Tinubu. 

Yanzu haka dai Manyan ‘Yan Siyasar Kasar irin su Bola Tinubu da wasu jiga-jigai na kokarin hada-kai su kafa sabuwar Jam’iyya. Ko da yake Tsohon Gwamnan ya musanya wannan magana. Amma ko ya abin yake, Siyasar Shugaba Buhari na cikin matsala.

[NAIJ Hausa]

Tuesday, December 6, 2016

Kotu ta sa a daure wani saboda satar batiri



– An kama wani bawan Allah da laifin satar batiri na mota a Garin Ibadan


– Alkali ya aika da shi Gidan Yari na Agodi domin ya dandana kudar sa 


– Mai laifin ya amsa da bakin sa cewa ya saci batiran mota





Wani karamin Kotu da ke Iyaganku a Garin Ibadan ya yankewa wani ta’aliki hukuncin dauri a Gidan Yari har na watanni 3 saboda ya saci batiri na mota guda biyu. Wannan mutumi dai ya saci batiri ne a wata mota da aka ajiye a kan hanya. 

Alkali mai shari’a, Patricia Adetuyibi tace ganin an kama wannan mutumi da laifi, kuma yana cikin wani yanayi, ya kamata ya shiga Gidan maza domin ya dandana kudar sa ko yayi hankali. Don haka yanzu wannan mutumi zai share watannin shida a Gidan Yarin Agodi da ke Garin. 

Wannan barawo mai suna Akinpade Kehinde ya kasance kuma gawurtaccen dan shaye-shaye a Yankin. Wani Jami’in ‘Yan Sanda, Philip Amusan ne ya kama sa bayan ya saci batiri mota guda biyu wadanda kudin su ya kai N70, 000. 

Akinpade ya amsa cewa lallai ya saci batiri a Ranar 23 ga watan Nuwamba da ta wuce da safe. Bayan nan kuma an kama sa da laifin kai hari ga wani da adda, hakan ta sa aka kara masa zaman watanni uku a Gidan Yari.

[NAIJ Hausa]

Ana shirin hana amfani da Hijabi

– Ana yunkurin haramta sanya dogon Hijabi a Kasar Jamus

 

– Shugaban Kasar Jamus na kokarin haramta amfani da Hijabi 

 

– Hakan zai kawo raguwar Musulmai a Kasar 



Jaridar Daily Mail ta rahoto cewa ana yunkurin hana amfani da dogon Hijabi da ake kira burqah a Kasar Jamus. 

Shugaban Kasar Jamus, Angela Merkel tace Jamus Kasar Kirista ce don haka bai dace ace ana amfani da dogon Hijabi ba watau burqah. Shugaban Kasar ta bayyana haka ne a wajen wani Taron Jam’iyyar su ta CDU da aka gudanar. 

Shugaban Kasar tace za tayi kokarin hana Musulmai dindirinzo zuwa Kasar Jamus din. Tace ba za a maimaita irin abin da ya faru a Kasar ba shekarar bara lokacin da Musulmai suka yi ta Hijira suna shigowa Kasar. 

Jam’iyyar CDU ta su Angela Merkel ta fadi zaben Jihohi da aka yi saboda matsayar ta game da Musulmai da suke shigowa Kasar. Kusan Musulmai 890,000 suka shigo Kasar Jamus da ke Tsakiyar Turai shekarar bara.


[Daga NAIJ Hausa]

Kwastam ta haramta shigo da motoci


– Gwamnatin Tarayya ta haramta shigo da motoci ta Kasa cikin Najeriya

 

– Kwastam tace duk mai mota a bakin iyaka ya shigo da ita kafin sabuwar shekara mai zuwa

 

– Daga karshen watan nan, babu damar shigo da motoci kowace iri sai ta iyakar teku




Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bada umarnin hana shigo da motoci fadin Kasar nan ta iyakar Kasa. Gwamnatin Kasar dai tace haramcin ya shafi sababbi da tsofaffin motoci zuwa cikin Kasar ta Najeriya.

Hukumar Kwastam tace daga Junairun shekara mai zuwa, babu damar shigo da motoci ta kan iyakar Kasa. Za a bari ne a rika shigo da motoci kawai ta iyakar ruwa. A Watan Afrilun shekarar nan ma dai aka haramta shigowa da shinkafa ta iyakar Kasa. 


Jami’in sadarwa na Hukumar Kwastam din, Mista Adeniyi Wale ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar da kuma sa hannun Shugaban Kwastam din na Kasa, Hameed Ali. An nemi duk wani mai motoci a kan iyaka ya shigo da su kafin karshen wannan watan na Disamba. 

Kwanakin baya Majalisar Dattawa ta fara kokarin hana shigo da motocin da ba sababbi ba cikin Kasar.

[NAIJ Hausa]

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...