Tuesday, December 6, 2016

Za a Hukunta El-Zakzaky-Gwamnatin Kaduna



– Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana ‘Yan Kungiyar IMN a matsayin ‘yan tawaye


– Gwamnati tace za ta hukunta Shugaban Kungiyar Ibrahim El-Zakzaky


– Za a kama El-Zakzaky da laifin mabiyan sa

 


Ta tabbata cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana Kungiyar IMN a matsayin ‘yan tawaye. Wannan yana cikin bayanin da Gwamnatin Jihar ta fitar da shi bayan bincike da aka gudanar na dogon lokaci. 

Takardar da aka fitar jiya ta bayyana cewa ‘Yan Kungiyar IMN din ‘yan tawaye ne masu tada zaune-tsaye don haka dole a dauki mataki game da su. Haka kuma takardar ta nuna cewa dole a Hukunta Ibrahim El-Zakzaky.

Takardar da Gwamnatin Tarayya ta fitar ya nuna cewa ‘Yan Kungiyar IMN din suna bin El-Zakzaky dari-bisa-dari, hakan ta sa ya kamata a kama sa da duk laifin da suka aikata. A rikicin Shi’ar da Soji da ya faru a bara, an hallaka ‘yan shi’a fiye da 300 a Garin. Gwamnatin Jihar tace za ta bar Gwamnatin Tarayya ta Hukunta Sojojin da ke da laifi.

Shugaban Kungiyar ta IMN, Ibrahim Yakub El-Zakzaky yana can a daure, kwanan ne dai wani Babban Kotu ya bada izinin a sake sa da gaggawa.


[NAIJ Hausa]

Monday, December 5, 2016

Za a fara daure masu yin kaciya


A Kasar Egypt za a fara kama masu yi wa mata kaciya


 

– Kasar Masar za ta dauki mataki mai tsanani ga masu yi wa ‘ya ‘ya mata kaciya

 


– Za a daure duk wanda aka kama na shekaru 15 kamar yadda  Majalisa ta amince

 


– Za a rika lura da kowane Asibiti ganin an hana kaciya ta mata



A Kasar Egypt, yanzu an kafa doka mai tsanani ga duk wanda aka kama yayi wa diya mace kaciya. Sabuwar dokar da aka sanya kwanan nan za ta sa a daure mutum na shekaru da dama a gidan kaso idan aka kama sa da laifi. 

Kasar Egypt din dai tayi garambawul ga dokokin Kasar inda yanzu za a iya jefa mutum yari na shekaru 15 idan har aka kama sa da laifin yi wa yara mata kaciya. A Ranar Talata da ta wuce ne dai Majalisar Kasar ta saka hannu kan wannan doka. 

Ma’aikatar Lafiya ta bada sanarwar cewa daga yanzu, Gwamnati za ta rika bibiyar duk Asibitocin Kasar ganin an kawo karshen kaciya da ake yi wa mata, watau abin da ake kira FGM. Ko a baya dai an taba kame wani Likita bayan da yayi wa wata yarinya kaciya. 

An saba yi wa mata kaciya musamman a Kasashe irin su Masar, wasu na ganin dai hakan yana da illa ga ‘ya mace. Sai dai yanzu an fara samun sauki Inji Hukumar UNDP.


[NAIJ Hausa]


Sunday, December 4, 2016

Abin mamaki: ‘Yar shekara 10 ta haihu


 
Wata yarinya mai shekara 10 a duniya ta zama uwa




– Wata Yarinya mai shekara 10 ta haihu a Kasar Kenya

 


– Wannan yarinya ta zama ‘yar autan uwaye a bara

 


– Ko shin ta ina ta samu juna biyu?


Wata karamar yarinya mai shekara 10 da haihuwa a duniya ta haifi wata itama. Wannan abin al’ajabi ya faru ne a Kasar Kenya a shekarar bara watau 2015.

Wannan yarinya mai shekara goma a duniya. Gladys Chelagat ta kafa tarihi, inda ta zama uwar da ta fi kowace karanci shekaru a duniya. 

Likitoci dai sun ce Gladys ta sauka lafiya, inda ta haifi jariri mai nauyin kusan kilo uku. Sai dai da aka yi aiki, sannan aka samu cire jaririn da aka samu. An yi wannan aiki ne a wani Asibiti a Kasar Kenya. 

Wani mutumi ne dai mai shekara 60 yayi wa wannan karamar yarinya ciki, wannan mutumi ya kasance mai kula da ita tun tana ‘yar karama. Wannana abu dai ya ba kowa mamaki kwarai da gaske. Wannan abu ya faru ne a Watan Yunin bara.


[NAIJ Hausa]

Wani Dalibi daga Najeriya ya ciri tuta a Ingila

Wani Dan Arewa ya taka rawar gani

– Wani dalibi daga Arewa ta Najeriya ya taka rawar gani a Kasar Ingila

 


– Marzuq Ungogo ya gama da mataki na farko a karatun digirin san a biyu

 


– Haziki Marzuq Ungogo ya kammala digirgir a Jami’ar Glasgow

 

 

Wani dalibi dan Arewa ya ciri tuta a can nesa Kasar Ingila. Marzuq Ungogo ya gama da matakin farko wajen karatun Digirin sa a Jami’ar Glasgow ta Kasar Birtaniya.

Marzuq mutumin Kasar Kano ne, kuma yayi Digirin sa a Jami’ar nan ta Ahmadu Bello ta Zariya, inda ya karanta Ilmin likitan dabbobi. Ko a Digirin na sa na farko dai, Marzuq ya ciri tuta a Jami’ar, inda ya ko kammala da matakin farko watau ‘first class’ a shekarar 2014.

Wannan haziki ya samu shaidar karantar Ilmin da ke lura da yadda magunguna ke aiki a jikin halittu watau ‘Clinical Pharmacology’ a Jami’ar Glasgow da ke Kasar Birtaniya. 

Kwanaki ma dai an samu wani gwarzo dan Arewa mai suna Adamu Tilde da ya taka rawar gani a wata Jami’ar Kasar Hungary. Shi ma Tilde, ya kware ne a fannin ilmin dabbobi. 

Allah ya kara mana irin su.

Wayoyin Salula za su daina whatsapp

Za a haramtawa wasu salula whatsapp



– Miliyoyin wayoyi za su daina amfani da whatsapp


– Daga karshen shekarar nan, za a haramtawa wasu salula whatsapp


– Wayoyi na kirar Android, Windows da IOS za su gamu da matsala

 

Wayoyin salula da dama irin na zamani za su gamu da cikas zuwa karshen wannan watan na Disamba. Za a haramtawa wayoyi da dama amfani da kafar sadarwa ta whatsapp kawo karshen wannan shekarar. 

Gidan Facebook ne dai suka saye kamfanin whatsapp a kwanakin baya, Miliyoyin mutane dai kuwa suna amfani da kafar whatsapp wajen aika sakonni. Sai dai masu wayoyi irin na da; kamar su Windows, Android da IOS ba za su samu damar cigaba da amfani da whatsapp ba.
 
Whatsapp din tace tsofaffin wayoyin ba za su iya cigaba da amfani da manhajar ba, watakila har sai nan da zuwa shekarar mai zuwa. Wayoyi irin su Apple da tsofaffin Android za su bar whatsapp. 

Haka nan ma kuwa, masu wayar Blackberry da Nokia za su gamu da babban cikas na amfani da manhajar whatsapp har sai nan da tsakiyar shekara mai zuwa. An dai dade ana amfani da whatsapp wajen aika sakonni.



Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...