Wednesday, August 30, 2017

Darajar Ranar 9 ga Watan Dhul Hajj 'Arafah'


Falalar azumin Ranar Arafah a Musulunci


  • Ranar 9 ga wannan wata ce Ranar nan ta Arafah a Addinin Musulunci
  • Allah Madaukaki ya rantse da ranakun Watan da kuma ta Ranar Arafah
  • Ana karbar addua da kuma 'yanta bayin Allah a wannan Rana ta musamman




A cikin al kurani Ubangiji ya rantse da wannan rana ta Arafah da ake taruwa na musamman a Suratul Buruj.

Daga cikin darajar wannan rana akwai cewa:

  1. A wannan rana ne aka cika sakon Addinin Musulunci inda har Aya ta sauka a cikin Suratul Ma'ida
  2. Kuma a wannan rana ne ake 'yanta bayin Allah da dama kamar yadda Hadisi ya zo a littafin Sahih Muslim
  3. Har wa yau kuma babu ranar da Ubangiji yake karbar addua kamar wannan rana wanda shi ma ya zo a littafin Silsilal hadith na Sheikh Nasir Deen Albany.
Duk wani Mahajjaci a wannan rana ya dukafa ana kuma neman rahamar Allah. Ana son azumi ga wadanda ba su je Hajji ba wanda ke kankare zunuban shekara biyu. Azumin ranar Arafah na yafe zunuban shekarar bara da kuma shekarar bana da ake ciki inji Manzon Allah SAW.


Dr. Isa Ibrahim Ali Pantami yayi wannan jawabi a wani karatu da yayi

Monday, August 28, 2017

Hukuncin Sallar Juma'a a Ranar Idin Sallah


Ina hukuncin zuwa sallar Juma'a a ranar Sallah?


  • Mun tattaro maganar Malamai game da faduwar idi a ranar Juma'a
  • Wasu na ganin idan hakan ta faru babu wajibcin zuwa Sallar Juma'a
  • Har wasu manyan Malaman ma na ganin cewa Sallar Azahar ta fadi


A daidai lokacin da ake shirin bikin babban idi mun tattaro maganar Malamai game da faduwar idi a ranar Juma'a kamar yadda za ta kama wanna karo daga wani darasi na babban Malamin musulunci Sheikh Muhammad Sani Rijiyar Lemu.

  1. Magana ta farko
Malaman Malikiyyah sun tafi a kan cewa dole ne ayi sallar Juma'a ko da ta fadi a ranar idi don haka Allah Madaukaki yayi umarni a Qurani asali.

  1. Magana ta biyu
Malaman Shafiiyah na ganin idan hakan ta faru babu wajibcin zuwa Sallar Juma'a ga wadanda su ka fito daga kauyukan nesa amma mutanen gari za su yi Juma'a.

  1. Magana ta uku
Akwai 'yan mazhabar Hanabila da su ka tafi akan cewa idan hakan ta faru to sallar idi ta dauke Sallar Juma'a.

  1. Magana ta hudu
Akwai Malamai irin su Imam Shawkani da ke ganin idan Idi ya fado a Juma'a to har sallar Azahar ta fadi amma wannan magana na sa rauni.


Magana mafi inganci inji manyan Malamai irin su Ibn Taymiyyah ita ce za a yi sallar idi sannan kuma mustahabbi ne Liman yayi sallar Juma'a ga masu niyya amma ba dole bane don kuwa wata idin ta dauke wata. 


[NAIJ Hausa]

Thursday, August 24, 2017

Dan wasa Cristiano Ronaldo ne gwarzon UEFA na 2017

UEFA ta zabi Ronaldo a matsayin babban Dan wasan Turai

 

  • Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ne gwarzon UEFA a bana
  • Yanzu nan UEFA ta zabi Ronaldo a matsayin babban Dan wasan Turai
  • Sauran 'Yan Real Madrid din sun ciri tuta a wajen fitar da gwani da ake yi


 Labari ya iso mana yanzu nan cewa UEFA ta zabi Cristiano Ronaldo a matsayin babban Dan wasan Turai na shekarar nan.

Babban Dan wasan na Real Madrid Cristiano Ronaldo ne gwarzon UEFA mai kula da kwallon kafan Turai a shekarar nan ta bana. Dan wasan ne kuma aka zaba gwarzon Dan wasan gaba na wannan shekarar. Fitaccen Dan kwallon Ronaldo dai ya tashi da kyaututtuka yau dinnan.

Har wa yau sauran 'Yan wasan Real Madrid din irin su Sergio Ramos sun ciri tuta. An zabi Ramos a matsayin Dan bayan da tauraruwar sa ta ke haskawa bana. An kuma zabi Luka Modric a matsayin gwarzon Dan wasan tsakiya na shekarar nan ta 2016.

Dan wasan gaban na Real Madrid ya lashe Gasar UEFA Champions league da UEFA SuperCup na bana da bara da Kungiyar sa ta Real Madrid ya kuma jefa kwallayen da su ka fi na kowa.



[NAIJ Hausa]

Wani mutumi ya tikawa Matar sa saki ta WhatsApp


An fara sakin aure ta sakon WhatsApp  


  • Yanzu cigaba fa ya kai inda ya kai a Duniyar sadarwa
  • Wannan ya sa yanzu har aure kan mutu ta kafafen zamani
  • Mutumin ya jibgawa Matar saki bayan tayi banza da shi





Mun samu labari cewa wani mutumi ya saki matar sa ta kafar sadarwa na zamanin nan na WhatsApp. Cigaba dai ta kai ana sanin idan an karanta sako a WhatsApp.

Wani Balarabe ne dai ya dankarawa Matar sa saki har 3 ta WhatsApp din a kan kurum yayi wa matar ta sa magana amma ba ta ba sa amsa ba. Abin da ya bata masa rai shi ne ta karanta sakon na sa amma tayi bakam ta kyale shi kamar ba ayi komai ba.

Yanzu cigaba ya kai inda ya kai a Duniyar sadarwa inda a kan nemi aure har ma a rabu a kafafen zamani. Sai dai akwai ta cewa wajen sakin na sa ganin ya rubutawa matar cewa ya sake ta har sau uku. Wasu dai na ganin cewa saki uku a lokaci daya ya sabawa Addinin Musulunci.


Mun samu wannan labari ne daga shafin Life in Saudi

Wednesday, August 23, 2017

Dan kwallon Ingila Rooney yayi ritaya


Babban Dan wasan Ingila ya ajiye kwallo a gida

  • Wayne Rooney yayi sallama da takawa kasar sa leda
  • Dan kwallon yace lokacin yayi da zai bar wa yara fage
  • Kyaftin din Ingila mai shekaru 31 da ya ajiye kambu

Dan wasan gaban nan Wayne Rooney yayi sallama da takawa kasar sa leda dazu nan. Dan wasa Rooney yayi ritaya yana shekara 31.

Babban Dan kwallon yace lokaci yayi da zai bar wa yara fage bayan yayi shekara 14 yana bugawa Kasar Ingila wasa. Kyaftin din na Ingila mai shekaru 31 dai ya ajiye kambu bayan tattaunawa da Kocin kasar Ingilar da kuma Kocin Kungiyar Everton.

A kakar bana ne dai tsohon Dan wasan nan Manchester United ya koma Kungiyar sa ta gida watau Everton inda yanzu har ya jefa kwallaye biyu. Dan wasan yace ba abu ne mai sauki barin Kulob din ba kuma yanzu ya ajiye kwallo a Kasar sa don ya maida hankali da kyau.



[NAIJ Hausa]

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...