Tuesday, January 24, 2017

Watakila yau a tabbatar da Magu



‘Yan Majalisun Kasar nan na shirin fara zama domin kasafin kudin wannan shekarar


Majalisar Dattawa za ta fara zama game da kundin kasafin kudi


Watakila yau Majalisar Dattawar ta tabbatar da Magu





Rahotanni daga Jaridar Daily Trust na nuna cewa yau Majalisar Dattawa za ta fara zama domin ta tattauna abin da ya shafi kundin kasafin wannan shekarar. Sanata Baba Garbai Kaka  wanda shine Shugaban Kwamitin irin wannan al’amura ya bayyana haka.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin a gaban Majalisar a karshen shekarar bara. Sai dai Majalisar ba ta ce komai ba tukun game da kundin har yanzu. Majalisar dai kwanaki tace tana da ayyuka da dama a gaban ta kamar su maganar rikicin Kudancin Kaduna da kuma haramta shigo da motoci, ga kuma kudirin PIB na bangaren mai.

Idan ba a manta ba kwanakin bayan ne Majalisar ta karkare batun takardun MTEF da kuma FSP da Shugaban Kasa ya kawo a baya. Zuwa wannan makon dai Sanatocin Kasar za su shiga tattauna game da kasafin bana wanda ya zarce Naira Tiriliyan 7.

Har wa yau kuma ana sa ran yau Shugaban Majalisar, Bukola Saraki ya kara karanto takardar shugaban kasa da ya ke nema a tabattar da Ibrahim Magu a matsayin Shugaban Hukumar EFCC. A kwanakin baya dai Majalisa ta kora Ibrahim Magu bisa wasu dalilai.





[NAIJ Hausa]

An nada mace a matsayin Mataimakiyar Shugaban kasa


Adama Barrow ya zabi Fatoumata Tambajang Mataimakiyar Shugaban kasa




Sabon Shugaban kasar Gambia, Adama Barrow ya nada Fatoumata Tambajang a matsayin Mataimakiyar sa. Halifa Sallah, mai magana da bakin Barrow ya bayyana haka a wani taro da aka yi jiya da manema labarai a Garin Banjul.

Fatoumata tayi kokari wajen sasanta abokan gaban siyasa a zaben bara. H. Fatoumata tayi aiki a matsayin mai bada shawara a kan harkokin mata da yara lokacin Shugaban Kasa Dawda Jawara. Ta kuma rike Shugaban Majalisar matan Kasar. Fatoumata dai tana da kyautar lambar girma bayan hidimar da tayi wa Kasar.

Kwanan nan Yahaya Jammeh ya sauka da karfi da yaji bayan dakarun ECOWAS sun dura cikin Kasar. Ko shi dai Mataimakiyar sa a lokacin mace ce, wanda tayi murabus daga kujerar da rikicin siyasar nan ta taso.



[NAIJ Hausa]

Monday, January 23, 2017

Fayose ba shi da hankali Inji Sanata Kashamu


Bai dace Ayo Fayose ya jagoranci PDP ba-Inji Sanata Kashamu




– Sanata Buruji Kashamu yayi raga-raga da Gwamna Ayo Fayose na Jihar Ekiti


– Sanatan yace bai dace a nada Ayo Fayose a matsayin Shugaban Gwamnonin PDP ba


 – Makon jiya aka nada Gwamna Fayose a matsayin Shugaban Gwamonin PDP na Kasar


Sanata Buruji Kashamu yayi tir da shawarar da Jam’iyyar PDP ta dauka na nada Gwamna Ayodele Fayose na Jihar Ekiti a matsayin shugaban Gwamnonin Jam’iyyar PDP. Fayose dai ya canji Gwamna Mimiko wanda wa’adin sa na daf da karewa.

Buruji Kashamu Sanata mai wakiltar Gabashin Ogun yace ko kadan Fayose bai dace da rikon wannan shugabanci ba. Kashamu yace hayaniya kurum ya cika kan na Fayose, babu ilmin komai. Kashamu ya kara da cewa Fayose yak an yi abubuwa kamar karamin yaro, yace da irin su aka nada a wannan matsayi.

Buruji Kashamu yace ya kamata ‘Yan PDP su nuna rashin amincewar su da wannan mataki da aka dauka. Kashamu yace babu abin da Fayose zai yi illa ya kashe Jam’iyyar PDP gaba daya don kuwa babu wanda zai yi aiki da shi.




[NAIJ Hausa]

An yankewa Dan Najeriya daurin rai-da-rai a Kasar waje


An kama wani Dan Najeriya da laifin kisa da fyade a Ingila


Tuni aka yanke masa hukuncin dauri


Dan Najeriyar dai dan manya ne a can ya kuma zo karatu ne




An samu wani Dan Najeriya da laifin fyade da kuma kashe wata mata a can Kasar Scotland. An dai kama wannan yaro ne da laifin yi wa wata mata mai-zaaman ka ta fyade, daga karshe kuma ya kashe ta.

Wannan yaro dai ya aikata wannan mummunan laifi ne jim kadan bayan zuwan sa Kasar domin karatu a Jami’ar Robert Gordon ta Birnin Abardeen. Mahaifin sa dai wakilin Najeriya ne a Kasar ta Scotland.

Bala Chinda mai shekau 26 dai yayi lalata da Jesica McGraa kafin ya kashe ta a shekarar bara ta 2016. Duk da ya karyata hakan, bincike ta na’urar daukar hoto na CCTV sun nuna cewa Bala ya ja Marigayiya Jesica zuwa dakin kwanan sa, wanda daga nan ba a kara ganin ta ba, sai gawar ta.

Kotu dai ta yankewa Bala Chinda hukucin daurin rai-da-rai bayan an gano cewa ya kashe wannan mata mai zaman kan ta. Watakila dai shake ta aka yi har ta mutu, ana kuma tunanin rikicin kudi ne ya hadu su.




[NAIJ Hausa]

An soke rajistar Jaridar Al-Mizan


– Kungiyar ‘Yan Jarida na Kasa ta soke rajistar Jaridar Al-Mizan


– NUJ tace tayi kuskure wajen rajistar Jaridar


– Jaridar Al-Mizan ta ‘Yan Shi’a ce




Kungiyar NUJ ta ‘Yan Jaridun Najeriya ta soke rajistar Jaridar nan ta Al-Mizan. Wannan mataki dai ya zo ba da bata wani lokaci ba kamar yadda Kungiyar ta bayyana bayan wani taron da tayi a karshen makon da ya wuce.

Sakataren Bangaren Kungiyar na Jihar Kaduna, Dauda Idris Doka ya sa hannu wajen matakin da aka dauka. Kungiyar ta bayyana cewa ta gano Jaridar ta ‘Yan Shi’a ce a zaman ta da tayi na zartarwa a Ranar 29 ga watan nan.

Kungiyar ta NUJ dai tace ba ruwan ta da wani addini, asali ma dai tana kokarin kare duk wasu Addinai da kuma Kabilu na Kasar ne. Kungiyar don haka tace tayi kusukuren ba Jaridar Al-Mizan lasisi a baya. Daga yanzu dai bai hallata  Jaridar ta ci gaba da aiki ba.

Jaridar Al-Mizan din da kuma ta Turancin ta watau Pointer Express ta Kungiyar IMN ce ta Shi’a. A baya dai NUJ ta hana Jaridu da dama lasisi saboda wannan dalilai.





[NAIJ Hausa]

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...