Friday, October 28, 2016

Ina tare da mai gida na-Aisha Buhari





Hajiya Aisha Buhari, matar Shugaban Kasa tace tana tare da Maigidan ta, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

 



Matar Shugaban Kasar ta bayyana haka ne yayin da ta kai ziyara Jihar Borno

 



Aisha Buhari ta je Garin Benisheik da aka karbe daga hannun Boko Haram, tace ta ji dadin ganin haka



Hajiya Aisha Buhari, matar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tace tana tare da Mai gidan nata da kuma kokarin ganin nasarar Gwamnatin sa. A kwanakin baya dai Hajiya Aisha Buhari ta ba duniya mamaki, inda tace idan fa mai gidan nata bai canza salo ba, to ba da ita nan da 2019. Aisha Buhari tayi wannan maganar ne a Gidan BBC da ke Landan.

Matar Shugaban Kasar tace yanzu dai tana tare da mai gidan ta, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, domin kuwa ya fara cika wasu alkawuran da ya dauka lokacin yana neman takarar Shugaban Kasa. Matar Shugaban Kasa, Aisha Buhari tayi wannan bayani ne lokacin da ta kai ziyara Garin Benisheik da ke Borno, da aka karbe daga hannun ‘Yan Kungiyar Boko Haram. 

Matar Shugaban Kasar ta raba kayan agaji ga wasu daga cikin matan yankin. Matar Gwamnan Jihar Borno, Nana Shettima ce ta tare Matar Shugaban Kasa, Aisha Buhari da tawagar ta; ta matan hafsun Sojojin Kasar da wasu matan ‘Yan Siyasa.

Aisha Buhari ta bayyanawa mutanen Garin Kaga cewa tayi farin cikin ganin an fatattaki Boko Haram daga yankin kamar yadda mai gidan ta yayi masu alkawari. Tace tana tare da maigidan nata a nan don kuwa mutumin kwarai ne, mai fada ya cika.

Za tayi shekaru kusan 100 a Gidan Yari




An yankewa wata mata ‘Yar Enugu hukuncin shekaru 90 a Gidan Yari bayan an kama ta da laifi

 


Hukumar EFCC ta kai karar Miss Chika Amsy Charles bisa zargin laifuffuka akalla 30

 


Yanzu wannan mata za tayi shekaru 90 a Gidan Yari bayan ta tabbata ta yaudari wasu mutane



Wani Kotu a Garin Enugu ya yankewa wata mata hukuncin shekaru 90 a Gidan Yari bayan an kama ta da laifin zamba. Wannan mata Chika Amsy Charles ta cuci wasu yara kudi har Miliyan 5.6 da sunan za ta sama masu makaranta ta wani Kamfanin ta na bogi.

Chika Amsy Charles ta cuci wasu yara har uku cewa za ta shigar da su Jami’ar fasaha ta Jihar Enugu. Daya daga cikin wadannan yara ya kai kara Hukumar EFCC, wannan abu ya faru ne tun a shekarar 2007. Yanzu haka dai, Babban Kotun Tarayya na Kasar da ke Enugu ta yankewa wannan mata daurin shekaru 90 a Gidan Yari. 


Karanta cikakken labari a nan...

Thursday, October 27, 2016

Na je neman kudin bude shagon aski ne inji dan Kungiyar shan jini


Wani dan Kungiya shan jini da aka kama ya bayyana abin da ya shiga cikin Kungiyar 

 

Yace jarin kasuwanci yake nema shiyasa ya shiga wannan Kungiya

 

Yanzu haka ‘Yan Sanda sun kama wannan mutumi



Jami’an ‘Yan Sanda sun kama mutane 12 da ake zargi ‘Yan Kungiyar Shan jini ne a Unguwar Apo da ke Birnin Abuja. An kama wadanna mutane da bindigogi, da adda da wukake Inji Jaridar Punch. Ana zargin wadannan mutane suna cikin wata Kungiyar shan jini mai suna Norsemen.

Kowane daga cikin wadanda aka kama ya bayyana dalilin da ya sa ya shiga wannan Kungiyar shan jini. Wani daga cikin su mai suna Fidelis Ogabor yace ya shiga Kungiyar shan jini ne domin karbar bashin kudi, Mista Ogabor yace yana neman kudi N200, 000 ne domin ya bude shagon gyaran gashi.


Mista Ogabor yace an kore sa ne daga wurin aiki, hakan ta sa ya shiga wannan Kungiyar shan jinni. Bayan ya nemi taimakon kudi daga wani Mista Williams, sai yace masa sai da ya shiga Kungiyar shan jini na Norsemen idan yana bukatar a taimaka masa. 

Fidelis Ogabor yace ya samu aron kudin bayan ya shiga Kungiyar shan jini, sai dai da ya gaza biyan bashin, ‘Yan Kungiyar shan jini sun tura ‘yan iskan gari suka likida masa dan-karan duka. Bayan nan ne ‘Yan Sanda suka kama sa, aka ce yana cikin ‘Yan Kungiyar shan jini.


Ya saki Amaryar sa bayan ya gan ta babu kwalliya



Wani mutumi ya kori Amaryar sa bayan ya gano mummuna ce 

 

Wani Balarabe ya rabu da ‘Yar Amaryar sa jim kadan bayan daura aure

 


Angon yace ya gano ashe Amaryar ta sa ba ta da kyau idan ta cire kwalliya

 




Wani Balarabe ya saki ‘Yar Amaryar matar sa jim kadan da yin aure bayan ya gan ta ba tare da kwalliya ba a karo na farko. Dakta Abdul Azeez Azif Asaf mai shekara 34 ya rabu da amaryar sa ‘Yar shekara 28 bayan da ya ga fuskar ta ba tare da kayan shafa ba.

Dakta Abdul Azeez Azif yace Amaryar ta yaudare sa da kayan shafe-shafe. Asalin abin da ya wakana dai shine, ango Abdul Azeez ya kai matar sa teku domin wasa da ruwa, ko da ta shiga ta fito sai ya ga abubuwa sun canza, ba dai kamar yadda ya saba ganin ta ba. Yace bayan ruwa ya wanke mata fuska sai ya ga kamar ba ita ba.
 
Abdul Azeez Azif yace ashe Amaryar ta sa tana sanya gashin ido da girar karya ne sannan kuma an yi mata aiki domin a rikida mata siffa kafin tayi aure. Yace sam bai gane Amaryar ba ko da ta shi ga ruwa ta fito.

Likitan wannan Amaryar yace tayi niyyar fadawa mijin ta abin da ya faru, sai dai ta makara. Yanzu haka dai sun rabu, mijin yace fau-fau ba zai yarda ba. 

[Daga GULF news]


Ta sayar da jinjirin da ta haifa N450,000




‘Yan Sanda sun kama wata mata ta saye jinjiri dan wata biyu



Jami’an ‘Yan Sanda sun kama wata Tsohuwa ta saye jinjirin wata biyu da haihuwa

 



Yanzu haka Miss Ross Edward na nan a tsare wajen Hukuma

 



Uwar wannan Jinjiri ta  sayar da shi N450, 000 saboda talauci

 

Jami’an ‘Yan Sanda sun kama wata mata mai suna Miss Ross Edward dauke da jinjiri dan wata biyu. Wannan mata ta bayyanawa Jami’an ‘Yan Sanda cewa ta saye wannan jinjiri ne daga hannun mahaifiyar sa kan kudi N450, 000

Cordelia Mani Nwanwe, Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Akwa-Ibom, ya tabbatar da faruwar wannan abu, ya kara da cewa akwai wani likita mai suna Dakta Eneyo Nyang da aka hada kai da shi wajen sayar da wannan jinjiri. Jami’in ‘Yan Sandan na Jihar yace za su cigaba dayin iyaka kokarin su wajen aikin kare rayuwkar jama’a a Jihar.

 
Mahaifiyar wannan jinjiri tace babu ce ta sa ta sayar da diyar da ta haifa, uwar jinjirin Miss Comfort Effiong tace ba ta da kowa; uwar ta tana fama da rashin lafiya, sannan kuma mijinta ya rasu. Wannan mata tace ta rasa yadda za tayi a duniya, hakan ta sa ta sayar da jinjiri dan wata biyu domin samun kudi. 

Wannan mata watau Miss Ross Edward tace tana da sha’war da, shiyasa ta saye wani jinjiri. Mahaifiyar jinjiri tace dai ba ta da wanda zai kula da yaron ko ya zauna hannun ta, shiyasa ta sayar N450000.

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...