Wednesday, May 10, 2017

Ka taba ganin matan Gwamnonin Arewa


Uwargidan Gwamnonin Arewa da inda su ka yi karatu [Cikin Hotuna]



– Mafi yawan Gwamnonin Arewa su na da ofisihin Uwargida na iyalan su


– Sai dai wasu Gwamnonin ba su jefa matan su cikin harkar shugabanci ba


– Ga dai kadan daga cikin matan Gwamnonin Arewa maso yamma



Mun kawo maku hotunan matan Gwamnonin Arewa. Irin su Gwamna Ibrahim Geidam dai ba a san matar sa ba. Don wasu Gwamnonin ba su bari matan su su shiga cikin sha’anin mulki


1.      Matar Gwamnan Jihar Adamawa: Hajiya Maryam Muhammad Umar Jibrilla



Matar Gwamnan Jihar Adamawa ‘yar gidan Sani Zangon-Daura ce wanda fitacce ne a Katsina da Najeriya. Tayi karatu har Digir-gir a Kasar Birtaniya.



2.      Matar Gwamnan Jihar Bauchi: Hajiya Hadiza Mohammed Abubakar


Abin da zai burge ka shi ne tun shekarar 1979 ta auri Mijin ta wanda yanzu ya zama Gwamna. Tayi Digiri har 2 a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya.



3.      Matar Gwamnan Jihar Borno: Hajia Nana Kashim Shettima


Ana mata lakabi da Uwar Marayu ita ma tayi karatu a Jami’ar Maiduguri kamar dai Mijin ta Kashim Shettima.


4.      Matar Gwamnan Jihar Gombe: Hajia Adama Dankwambo



Uwargidar Mai girma Gwamna Dankwambo na Jihar Gombe kuma tana bakin kokari wajen dafawa Mijin ta.




[NAIJ.com]

UCL: Kungiyar Juventus ta kai wasan karshe


Champions League: Juventus ta karasa zagayen karshe


 – Kungiyar Juventus ta karasa zagayen karshe a gasar Uefa Champions League


– Sau 2 kenan cikin shekaru 3 Juventus din tana kai wannan matsayi


– Ko wannan karo za a dace a Birnin Cardiff?





Monaco ta kara shan kashi a hannun Juventus a Gasar zakarun Nahiyar Turai. Dani Alves ya nuna cewa har yanzu akwai sauran ta a kafar sa a wasan. Matashin Dan wasa Mpape ya zurawa Buffon kwallo a raga.

Kungiyar Juventus ta kasar Italiya ta isa zagayen karshe a gasar UEFA Champions League na zakarun Nahiyar Turai bayan ta doke Monaco ta Faransa da ci 2-1. A zagayen farko Juventus tayi nasara da ci biyu da nema.




Dan wasa Madzukic da Dani Alves ne su ka fatattaki Monaco yayin da Dan wasan ta Mpape ya zama mai mafi karancin shekarun da ya taba cin kwallo a wannan zagaye na Gasar. Juventus za ta kara karawa a wasan karshe da Kulob din Madrid a Birnin Cardiff.


[NAIJ Hausa]

Tuesday, May 9, 2017

Chelsea na daf da zama zakarun Ingila


 Na gaba yayi gaba: Chelsea ba za ta tsaidu ba

 
 – Kungiyar Chelsea na daf da daga kofin firimiya na Ingila


– Yanzu nasarar wasa guda kurum Chelsea ke bukata


– Hakan ya zo bayan Chelsea ta lallasa Kungiyar Middleborough




Yanzu dai Chelsea ta kama hanyar lashe gasar Firimiya. Kungiyar Chelsea na neman maki uku ne rak domin zama zakara. ESPN ta rahoto Dan wasa Nemanja Matic yace har yanzu ba za su ce sun ci gasa ba.

Chelsea za ta iya lashe gasar Firimiya na shekarar bana daga ta samu maki uku kacal cikin wasannin da su ka rage. Tottenham Hotspur ne dai ke bin Kungiyar sau-da-kafa a baya sai da alamu ba za ta kamu ba.

Hakan ya zo ne bayan Chelsea ta ba Kungiyar Boro kashi a wasan da su ka buga jiya da dare. Chelsea ta doke Boron ne da ci uku da nema wanda duk Fabregas ne ya haddasa su. Chelsea za ta kara da Wes Brom Ranar Juma’a.


[NAIJ Hausa]

Wednesday, May 3, 2017

UCL: Ronaldo ya tarwatsa Atletico Madrid



Champions league: Real Madrid na shirin kafa tarihi a Turai
 

– Kungiyar Real Madrid ta doke makwabtan ta Atletico Madrid a gida


– Real Madrid tayi nasara da ci uku da nema


– Hatsabibin Dan wasa Cristiano Ronaldo ya kara jefa kwallaye 3




Wannan karo ma dai kuma babban Dan wasa Ronaldo ya kara zura kwallaye 3 a Gasar UEFA Champions league.

Real Madrid ta doke Kungiyar Atletico Madrid 3-0 a zagaye na farko na wasan na-kusa da karshe.
Monaco za ta fafata Kungiyar Juventus.

Zakarun UEFA Champions league Kungiyar Real Madrid na iya kafa tarihi idan su ka kara daga kofin a bana. Babu wanda ya taba daukar kofin dai sau biyu a jere tun da aka sauya Gasar na zakarun Turai.




Dan wasa Ronaldo dai ya kafa tarihi inda ya zama Dan wasan da ya jefa kwallaye 3 a wasanni biyu a jere a Gasar. Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo ne ya jefa kwallaye 3 duk shi kadai a wasan su da Bayern Munich haka kuma ya kara yi a wasan jiya.

Ana fara wasan Ronaldo ya jefa kwallo guda a raga. Bayan wasan yayi nisa kuma ya kara daya, kafin dai a tashi su ka zama uku. Real Madrid da musamman Ronaldo sun raina Kungiyar Atletico inda ya zura masu kwallaye kusan 20 a ragar su shi kadai.




[NAIJ Hausa]

Tuesday, May 2, 2017

Dalilai 3 da su ka sa har Boko Haram tayi karfi


Abubuwa 3 da su ka sa ‘Yan Boko Haram su ka gagara


 


– Ana kan nasara wajen murkushe ‘Yan Kungiyar Boko Haram


– ‘Yan ta’addan sun kashe dinbin mutane a Yankin kasa da Nahiyar


– Ko ya aka yi suka yi wannan karfi haka a Duniya?





Wani Marubuci mai suna Theophilus Abbah ya zayyano dalilan da su ka sa Boko Haram tayi karfi. Duk da sakacin Hukuma akwai wasu dalilai da har su ka kawo Kungiyar tun farko. Na tsakuro daga ciki: 





1.      Jahilci da rashin aikin yi
Boko Haram tayi amfani da Jahilcin Matasa da kuma rashin sana’a inda aka nuna masu cewa aikin Allah su ke yi dama can ba su da wani aikin kuma ba su san Allah ba. Ko da wasu kadan cikin su na da karatu.


2.      Makamai
Boko Haram ta samu makudan kudi na sayen makamai da kuma makaman kan su daga wurare da dama. Ciki dai har da ta Arewacin Nahiyar bayan da Kasar Libya ta fadi daga hannun Marigayi Shugaba Moumar Gaddafi.

3.      Kashe makiya Kafirai
Ko da akwai rikicin siyasa tsakanin kungiyar sai dai sun yi tarayya wajen ganin bayan Kafirai da wadanda su ke kira Dagutu. Wajen su ko da an mutu wajen wannan gaba ta kai mutum.



[NAIJ Hausa]

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...