Wednesday, March 1, 2017

An yi kira ga Musulmai su rike Al-Kur’ani


Wasu Malamai daga kasar Saudiyya sun yi kira ga Musulmai suyi riko da littafin Al-Kur’ani mai girma domin su rabota a nan Duniya da lahira.



Wasu Malaman addini da suka taso tun daga kasar Saudiyya sun yi kira ga Jama’a suyi riko da Littafin Al-Kur’ani mai girma. Malaman suka ce riko da littafin Allah ne kadai zai kai Jama’a ga shiriya Duniya da kuma Lahira.

Malaman dai sun taso ne daga Jami’ar Ummul-Qura ta cikin Birnin Makkah da ke Kasar Saudiyya inda suka zo Najeriya kuma Jihar Kaduna. Sun zabi wurare inda suka yi wa’azi a Jihar daga ciki akwai masallacin ITN da ke Zangon-Shanu Zaria.



Dr. Ahmad Al-Furaih da kuma Dr. Ahmad Al-Huraisi da ke Jami’ar Birnin Makkah suka ce dole a komawa Littafin mai tsarki  domin a samu cigaba a nan da ma gaba. Daya daga cikin Malaman yace idan har makarantun Kur’ani suka lalace to al’umma ta lalace koda yake dai mutanen Najeriya suna da kokarin karatun Al-kur’ani.

Dr. Al-Huraisi yayi kira da Jama’a su yi koyi da darussan da ke cikin Al-Kur’ani irin na kisosshin Annabawa. Riko da littafin dai bai tsaya a karatu ba kurum, ya hada har da aiki da shi Inji Malaman kamar yadda mutanen da su gabace mu suka yi.




[NAIJ Hausa]

‘Yar Najeriya ta kafa tarihi a UN



Kwanakin baya ne Majalisar Dinkin Duniya ta dauke Ministar Buhari, yanzu haka har an rantsar da ita a matsayin mataimakiyar shugaban majalisar a Birnin New York da ke Amurka.


Majalisar Dinkin Duniya watau UN ta rantsar da ‘Yar Najeriyar nan kuma tsohuwar Ministar kasar Amina J. Mohammed jiya a matsayin mataimakiyar shugaban majalisar a ofishin Majalisar da ke Birnin New York na kasar Amurka. 

Shugaban Majalisar Antonio Gutierrez ne da kan sa ya rantsar da Amina Muhammad inda yace suna mai matukar farin ciki da ta shigo cikin tafiyar ta su. Jim kadan bayan rantsar da Amina ta shiga gudanar da wani aikin tare da bayyana muradun ta.

Antonio Gutierrez wanda ya zama Shugaban Majalisar na 9 a Tarihi, ya nada Amina J. Mohammed a matsayin Mataimakiyar sa tun watan Disamba sai dai ba ta fara aiki ba sai kawo yanzu saboda tana rike da ofishin Minista a Najeriya inda ta ke kokarin kammala wasu ayyuka.  

Amina ce dai ‘Yar Afrika ta biyu a tarihi da ta taba rike wannan matasayi a Majalisar dinkin Duniya. Amina Muhammad ta zama wata abin koyi ga matasa masu tasowa. Tun ba yau ba dai ta fara aiki da Majalisar dinkin Duniyar watau UN ta kuma taka rawar-gani.


[NAIJ Hausa] 

Ko ka san ganga nawa ake hakowa a kullum?



– Yawan man da Najeriya ke samu ya kara yawa


Da alamu an rage samun fasa bututun mai daga yankin Neja-Delta


– A cikin ‘yan kwanakin nan dai har Naira ta tashi




Kamfanin man Najeriya na NNPC ya bayyana cewa man da kasar nan ke hakowa a kowace rana ya kara yawa. NNPC tace a kullum Najeriya na samun gangar mai sama da miliyan 2. Ko da yake dai ba bayyana dalilin karin ba.

Shugaban Kamfanin na NNPC Maikanti Baru ya bayyana haka yayin da ya zanta da ‘Yan jarida a Abuja. Mista Baru yace ana sa ran zuwa karshen shekara a rika samun sama da ganga miliyan 2.2 a kowace rana.

Da alamu dai rikicin yankin na Neja-Delta yayi kasa don kuwa kwana biyu ba a fasa wani bututun mai ba. Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Osinbajo dai yayi ta ziyarar yankin kwanki domin kawo karshen rikicin.

Shugaban OPEC M. Sanusi Barkindo yace yayi mamakin yadda Najeriya ta tsira daga kangin da aka shiga na tattalin arziki bayan da mai yayi kasa. Barkindo yace yanzu haka an yi mai wuyar don kuwa farashin mai ya daga a duniya.

[NAIJ Hausa]

Kocin Arsenal Wenger zai tashi?




Da alamu kwanakin Kocin kungiyar Arsenal Arsene Wenger sun zo karshe. Wata majiya tace har an fara kishin-kishin din wanda zai maye gurbin na sa.

Dama can Kocin Kungiyar Arsenal watau Arsene Wenger na fuskantar barazana da kalubale tun bayan da Kungiyar sa ta kwashi kashin ta a hannun Bayern Munich makonnin baya. Bayern Munich din dai ta koyawa Arsenal darasi da ci 5-1 a Gasar Champions League.

Kocin Juventus Massimiliano Allegri ya fadawa abokan sa a kasar Italiya cewa zai wuce Arsenal a karshen kakar bana domin ya karbi Koci Arsene Wenger. Da alamu kuma dai hakan za ayi watau Allegri zai bar Juventus din da yake horaswa.

Allegri dai ya dade yana horaswa a Italiya har ya kuwa ci kofin gasar Seria A tare da AC Milan da kuma Kungiyar Juventus. Koci Arsene Wenger dai yace ko zai bar Arsenal ba zai bar aikin horaswa ba sai nan gaba.

Wasu suna ganin ya kamata Kocin ya tattara kayan sa ya bar Kulob din don kuwa duk shekara Arsenal din ba ta kai ko ina. Shekaru fiye da 20 kenan Wenger ya kwashe a Arsenal.




[NAIJ Hausa]

Izala ba ta yarda da yunkurin Sarkin Kano ba


– Sarkin Kano Sanusi II yace za a hana talaka yawan aure a kasar sa


–Malamin nan na Izala Sheikh Jingir yace idan aka yi haka ba a yi daidai ba


– Sheikh Jingir yace Al-Kur’ani ya bada damar auren mata 4





Shugaban Majalisar malamai na Kungiyar nan ta Jama’atul Izalatul bidi’a wa iqamatus sunnah watau JIBWIS yace sam bai dace Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II yayi maganar cewa za a hana talaka tubus kara auren mata a kasar sa ba.

Malamin yace hakan ba daidai bane don kuwa Al-Kur’ani ya ba maza damar auren mata har 4. Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bayyana haka ne yayin da yake magana da manema labarai a Garin Jos. Shehin ya nemi Sarkin ya gana da Malamai domin shawo kan matsalolin aure.




Jingir yace a irin wannan lokaci da ake da zaurawa da dama, auren su zai kara wahala idan har aka kafa wannan doka. Malamin ya kuma nemi Jama’a su ji tsoron Allah a gidajen auren su. Sarkin ya bayyana yadda ya rika samun koke-koke daga mata game da yadda tsofaffin mazajen su ke watsi da kula da ‘ya ‘yan da suka haifa yace aikin sa ne ya dauki mataki. 

Babban malamin Duniya mai fatawa Sheikh Ismail Menk shi kuwa ya goyi bayan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a game da maganar. Babban Shehin yace ko da cewa aure Sunnah ne mai karfi, amma ko Manzon Allah SAW cewa yayi wanda yake da hali yayi, wanda kuma ba sa da shi sai ya hakura, ina kuma maganar karawa.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II dai yace wannan mataki ya zama dole dalilin yadda iyaye maza ke watsi da tarbiyyar 'ya 'yan na su.



[NAIJ Hausa]

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...