Wednesday, November 2, 2016

A sauka lafiya, duk wanda zai bar Najeriya-Shugaba Buhari


Muna nan, sai mun gyara Kasar nan-Shugaba Buhari



Shugaba Buhari yace duk mai shirin barin Najeriya, ya sauka lafiya

 

Shugaba Buhari yace amma fa su suna nan, babu inda za su je, sai Najeriya tayi kyau

 

Shugaban Kasa ya fadi hakane lokacin da ya gana da Shugabannin Neja-Delta


Shugaba Buhari yace duk wanda yake ganin yana da wurin zuwa da ba Najeriya ba, to sai yayi tafiyar sa, ya sauka lafiya, amma fa su suna nan har sai sun gyara Najeriya. Mai magana da bakin Shugaban Kasar, Mallam Garba Shehu ya bayyana wannan jawabi na Shugaban Kasar.

Shugaba Buhari yayi wannan magana ne a lokacin da ya gana da Shugabannin Yankin Neja-Delta a jiya. An yi wannan tattaunawa domin ganin an samu wanzuwar zaman lafiya a Yankin na Neja-Delta. Shugaba Buhari yake cewa duk wanda yake da wata Kasa da ba Najeriya ba, sai ya fice, ya tafi can.


Shugaba Buhari kuwa yake cewa za su tsaya a Kasar har sai sun gyara ta, Shugaban Kasar ya koka da irin halin da ake ciki; yake cewa har ta kai Jihohi da dama ba su iya biyan albashin ma’aikatan su.


A Karanta cikakkun labarai a NAIJ Hausa

Tuesday, November 1, 2016

Katuwar tirela dauke da Garri ta kashe dalibai ‘yan makaranta

 Wasu dalibai 'yan makarantar FGGC Oyo sun yi hadari a mota wajen dawowa gida hutu


Wasu dalibai ‘Yan makaranta FGGC Oyo sun yi hadari  


Wata katuwar mota ta fado kan yara dalibai ‘Yan makaranta, inda ta latse wasu daga cikin su har lahira. Wannan abin takaici ya faru ne a hanyar dawowa gidan ‘yan makaranta domin hutun yada zango. Wannan katuwar gingimari tana dauke ne da Garri, tayi sandiyar mutuwar dalibai har guda hudu.

Wannan mummunan abu ya auka ne da dalibai ‘yan makaranta Sakandare ta mata watau FGGC Oyo. An rasa dalibai hudu da kuma direba daya a wannan mummunan hadari. The Nations ta rahoto cewa, wannan hadari ya faru ne a Ranar Lahadi daidai karfe 3:30 na Yamma a kusa da wata kasuwa da ke Garin Sabo da ke kusa da Garin Oyo.

Wata gingimari dauke da Garin rogo ta fada kan daliban ne inda ta kashe guda hudu nan take da kuma Direban motar. Daliban da suka rasa rayukan nasu su ne; John Olubukola, Giwa Taibat, Ladipo Mojisolo, Ibirogba Maryam; Daliban ‘Yan aji uku ne zuwa shida. Tuni dai aka bizne wadannan dalibai cikin kuka da jimami.

Sai dai guda biyar sun samu damar tsira da ran su, tuni dai ‘Yan Sanda sun kama direban wannan babbar mota.


A karanta labarai a shafin NAIJ Hausa

Shugaban Kasa ya tika rawa da mai dakin sa


Shugaban Kasa Barack Obama na Amurka ya sha rawa

 


Shugaban Kasa Barack Obama ya tika rawa da mai dakin sa

 


Barack Obama da Uwargidan sa Michele Obama sun cashe ne a Bikin Halloween

 

Sai ga Shugaban Kasa da Uwargida a Gidan White House su na rawar Micheal Jackson 

 

 


A abin da zai kasance Bikin Halloween din Shugaban Kasa Barack Obama na karshe a Gidan Shugaban Kasa na White House, Shugaban Kasa Barack Obama ya taka rawa da shi da mai dakin ta sa-Michele Obama. 

Wani bidiyo daga Gidan labarai na CNN ya nuna Shugaban Kasa Barack Obama da kuma uwar ‘Ya ‘yar sa, Michele Obama suna taka rawa abin su. Shugaban Kasa Obama na Amurka yayi rawar Marigayi Micheal Jackson a Wakar sa ta Thriller. Wannan ne zai kasance Bikin Halloween din na Iyalan Obama na karshe a Gidan White House.


An dai saba yin wannan biki na Halloween a karshen watan Oktoban kowace shekara. Shugaban Kasa Obama na Amurka ya gayyaci mutane fiye da 4000 zuwa wannan biki a Fadar Shugaban Kasa na White House. Za a zabi sabon Shugaban Kasa a Amurka wannan watan; tsakanin Hillary Clinton da Donald Trump.

Shugaban Kasa Obama ya gayyaci yara daga Makarantu 15 na Kasar da kuma Iyalan Sojojin Kasar, inda ya rabawa yaran alewa bayan ya kamala jawabi, ya ba mutane dariya. An dai Shugaban Kasa Obama yana rawar Thriller na Micheal Jackson da aka yi yayi shekaru fiye da 30 da suka wuce.

Abin Mamaki: wanda aka ba tsaro yayi sata





Kotu a Abuja ta kama wani mai gadi yayi sata

 


Kotun da ke Ubguwar Area I a Birnin Tarayya ta bada belin wanda ake zargi

 


court (1)



Wani Kotu da ke zama a Unguwar Karmo da ke Area 1 a Babban Birnin Tarayya Abuja, ta bada belin wani saurayi da ake zargi da laifin yayi sata. Ana zargin wannan saurayi da bai wuce shekaru 19 ba ya sace kayan ginin gidan da yake gadi a Garin na Abuja.

Alkalin Kotun na Area 1, Abubakar Sadiq ya bada belin wannan mai gadi mai suna Peter Gwaza Inji Jaridar Daily Trust. An bada belin na sa ne a kan kudi har N500,000 tare da kawo wanda zai tsaya masa. 


Kotun tace dole wanda zai tsayawa wannan mai gadi da ake zargi da lafin sata ya zama ma’aikacin Gwamnati, kuma wanda yake akalla mataki na 7 na aiki. Yanzu haka dai an daga shari’ar zuwa 10 ga wannan wata. An bayyana cewa dai wanda ake zargi ya bayyana cewa ya saci kayan da ake magana, har ma ya sayar da su tuni kan kudi N17,000.

Ku karanta cikakkun labarai a shafin NAIJ Hausa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya saba alkawari



Shugaban Kasa ya ce zai dauki matasa aiki amma shiru

 

Shugaban Kasa yayi alkawarin daukar matasa 200, 000 aiki kafin karshen watan Jiya, amma har yau ba labari-Inji Farfesa Farouk Kperogi 




Farfesa Farouk Kperogi da ke Jami’ar Jihar Kennesaw ta Kasar Amurka ya bayyana ta shafin san a Facebook cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karya alkawarin da yayi. Shugaban Kasa Buhari yayi alkawarin daukar matasa aiki kafin karshen watan Jiya, amma har an shiga sabon wata, shiru kake ji.

Farfesa Kperogi ya nuna damuwar sa da halin da ake ciki a mulkin Shugaba Buhari, ya kuma nuna takaicin ga yadda matasa da dama suke zaune ba aikin yi a Kasar nan. Kwanakin baya Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya tabbatar da cewa Gwmanatin Tarayya ta fara tantance matasa 200,000 da za ta samarwa aiki a Kasar.

Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce zuwa karshen watan Oktoba za a samarwa matasa 200,000 aiki a Najeriya, Farfesa Kperogi yace shin ina matasan da aka samawa aikin, ganin watan Oktoba ta kare?

Farfesa Kperogi ya bada labarin yadda wasu dubunnai suka rasa ayyukan su a Kasar. Yace ya samu sako daga wani cewa yana cikin mutane fiye da 1300 da aka kora daga aiki, Farfesa Kperogi yace wannan abu akwai takaici. Farfesa Kperogi yace dole Gwamnatin Tarayya ta zage dantse, a fara gani a kasa.


Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...