Sunday, March 19, 2017

Ashe Dangote ya fi su Donald Trump kudi


Mai kudin Najeriya Alhaji Aliko Dangote ya fi shugaban kasar Amurka kudi


Arzikin Dangote ya fi jimilar abin da Trump da Oprah suka mallaka


Mujallar Forbes ta Duniya ta bayyana haka






Jaridar Forbes ta bayyana cewa arzikin mai kudin Najeriya da ma Afrika Alhaji Aliko Dangote ya fi abin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya mallaka. Trump dai kasurgumin attajiri ne tun tuni amma Dangote ya sha gaban sa nesa ba kusa ba.


Bari ma dai dukiyar Dangote ta fi ta Donald J Trump hada da na bakar ‘yar kasuwar nan Oprah Winfrey ta Amurka. Dukiyar Dangote a yanzu haka ta kai akalla Dala biliyan $11 wanda ya ribanya abin da Trump mai Dala biliyan 3.7 da Oprah mai Dala biliyan 3 suka mallaka.




Dangote dai ya taba shigowa cikin sahun mutane 25 da suka fi kowa arziki a Duniya shekaru 3 da suka wuce. Shekara 6 kenan dai har yanzu babu wanda ya kai Aliko Dangote dukiya a kaf Nahiyar Afrika.



[NAIJ Hausa]

Thursday, March 16, 2017

Tauraruwar ‘Yar wasar Hollywood ta musulunta



Shahararriyar Tauraruwar Hollywood Lindsay Lohan ta karbi musulunci





Shahararriyar ‘yar wasan nan ta Hollywood mai suna Lindsay Lohan dai ta karbi musulunci kuma har ta fara zurfi a cikin addinin

Akwai kishin-kishin din cewa shararriyar ‘yar wasan nan ta kasar Amurka Lindsay Lohan ta zama Musulma. Kwanakin baya ne dai aka yi ta yada wannan rade-rade kuma da alamu hakan gaskiya ne.



Tauraruwar Hollywood Lohan ta dai goge duk rubuce rubuce da ta taba yi a shafukan ta irin su Instagram kamar yadda muka samu labari daga Jaridar Daily Trust. Yanzu haka dai idan ka shiga shafin na Lindsay Lohon za ka ci karo ne da kalmar Assalamu Alaikum.

An dai ga Jarumar ta koma saka Hijabi a jikin ta sai ga shi a wancan makon da ya wuce Tauraruwar ta yanko wasu maganganu na Annabi Muhammadu SAW domin tunawa da Ranar mata na Duniya. Da alamu dai Lindsay Lohan ta karbi addinin Musulunci.


[NAIJ Hausa]

Wednesday, March 15, 2017

Tattalin arziki: Abubuwa sun fara gyaruwa a Najeriya


– A wannan hali Najeriya na fama da durkushewar tattalin arziki


Sai dai da alamu abubuwa za su yi kyau dan nan gaba


– Alkaluma su na bayyana cewa Najeriya na farfadowa





A halin yanzu dai Najeriya na cikin matshi na tattalin arziki sai dai yanzu abubuwan kyau suke karawa ba tabarbarewa ba idan muka yi la’akari da wasu abubuwa da dama. Tattalin arzikin Najeriya dai ya rugurguje a bara.

Jiya aka bayyana cewa an fara samun sauki wajen hauhawar farashin kaya wanda a da can dai kullum cikin tashi suke. Haka kuma jiimilar kudin kasar watau GDP yana ta kara yawa ne kamar yadda nazari ya nuna.




Yanzu haka dai kudin gangar mai ya tashi don haka Najeriya na kara samun kudin shiga baya ga cewa kuma an samu sauki a Yankin Neja-Delta daga tsageru masu fasa butatan mai. Wannan ya bada dama kasar ta samu rarar daloli har ake saidawa bankuna. Yanzu dai asusun kasar waje na kasar kara yawa kurum yake yi.

Kungiyar OPEC na kasashen Duniya masu fita da mai ta bayyana cewa Najeriya tana cikin sahun kasashen da yawan man da suke hakowa ya kara yawa a watan Jiya watau Fubrairu. Yanzu dai Najeriya na hako sama da ganga miliyan 1.6.



Buhari ya gana da Gwamnan CBN jiya


Muna da labari cewa darajar Naira ya karu a farkon makon nan a kan kusa kowane kudin kasar waje. Nairar dai ta kara daraja akan Dalar Amurka da kuma Pounds Sterling na Ingila da kuma Dalar EURO ta kasashen Turai.

Har wa yau Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tayi abin da zai sa Ma’aikatan N-Power murmushi inda ta amice da karin N4500 a albashin kowane Ma’aikaci. An kara wannan kudi ne saboda Ma’aikatan su samu daman sayen na’urar da za ta taimaka wasu wajen aiki.



Tuesday, March 14, 2017

Ta kashe kan ta kuma ta haska a Facebook


Wata Budurwa ta kashe kan ta inda ta dauki bidiyo


Wannan yarinya mai shekaru ta saka mutuwar ta kai tsaye a Facebook


Mahaifiyar wannan yarinya tayi da na sani





Wata Budurwa mai suna Nakia Caze ta kashe kan ta har lahira inda ta kuma dauki Bidiyo ta haska a shafin Facebook kai tsaye. Mahaifiyar wannan yarinya dai ta dauko da farko abin wasa ne kurum na yara inda a karshe ta ciza yatsa.
Wannan mata Gina Caze da farko da ta ga Bidiyon tayi tunani wasa ne kurum na yara domin jan magana ashe dai wannan yarinya da gaske lahira ta hara da gaske. Matar tace wa Diyar tata a Facebook cewa idan ta mutu za a bizne ta kamar ba ayi ba don haka ta komawa littafi ta ji da karatun ta.

Wannan yarinya dai ba ta tare da uwar ta tun bayan da aka samu wani sabani tsakanin su a baya. Uwar ta bada yarinyar inda tace ba ta son ta saboda halin banzan ta na rashin son makaranta da shan giya, asali ma dai ta saba yin tatul da giya. 

Nakia dai ta haska bidiyo na kusan sa’a biyu inda aka ga tana kashe kan ta da kan ta. ‘Yan Sanda dai sun iske wannan Budurwa cikin kewaye a mace ta zama gawa.



[NAIJ Hausa]

Cristiano Ronaldo ya kafa tarihi



Ronaldo yayi abin da ba a taba yi ba a kasar Spain


Babban dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya bar tarihi a Duniya


– Duk kasar Spain babu dan wasan da ya kai Ronaldo zura kwallaye ta kai


– Haka kuma Ronaldo ya fi kowa jefa kwallaye a Filin Santiago Bernabeau




Zakaran Duniya Cristiano Ronaldo ya kafa tarihi a Duniya inda ya zama Dan wasan da ya fi kowa zura kwallaye a raga da kai. A karshen wannan makon ne Ronaldo ya kara jefa kwallo da kai a wasan su da Real Betis.

Yanzu haka Ronaldo yana da kwallaye 46 da ya ci da kai tun zuwan sa kasar Spain. Duk kasar dai ba a taba samun wanda ya ci irin wannan kwallaye a tarihi ba. Dan wasa Aritz Aduriz ne dama can ya fi kowa inda ya ke da kwallaye 45.


Haka kuma Ronaldo ne Dan wasan da ya fi kowa kwallaye a gida watau filin Santiago Bernabeau. Cristiano Ronaldo ya buge tsohon Dan wasan Kungiyar Santillana mai kwallaye 209 a filin wasan inda shi ya zarce haka. 

Yanzu haka dai Real Madrid tayi gaba a Gasar La-liga bayan ta doke Real Betis a Ranar Lahadi. Sergio Ramos ne ya ci kwallon karshen a wasan.


[NAIJ Hausa]

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...