Monday, April 3, 2017

Mutumin Delta ya auri mata 2 a tare


Wani Dan Neja-Delta ya bayyana dalilin sa na aure mata 2 a tare


 




Wani Ta’aliki ya auri mata har 2 kuma a rana guda kwanan a Jihar Deltan Najeriya. Wannan abu dai ba a saba jin sa ba musamman a irin wannan yanki na kudancin kasar.


Omamuzo Utomajiri wani mutumin Neja-Delta ne yayi wani abin da ba a saba gani ko ji a Yankin Neja-Delta ba inda ya hada mata 2 ya aure a rana guda abin sa. Utomajiri ya bayyana dalilin sa na yin hakan.

Wannan Bawan Allah kuma dan kasuwa da ke Uro-Irri na karamar hukumar Isoko kamar yadda mu ke samun labari yace ya auro mata 2 ne domin ya zama babu ruwan sa da mata a waje. Angon yace kuma suna son junan su.


Shi dai wannan mutumi yana sana’ar saida katako ne da kayan gini wanda kuma kowace mata ke kula da na ta barayin Inji wannan Angon na mata biyu. An dai daura auren ne a Ranar 26 ga watan Maris dinnan,



[NAIJ Hausa]

Dan wasa Neymar na Barcelona ya ajiye Tarihi

‘Yan wasan Real Madrid da Barcelona sun bar tarihi




– Neymar Jr. ya ci kwallon sa ta 100 a Barcelona


– Shekarar Neymar kusan 4 a Kungiyar Barcelona


– Haka ma Real Madrid ba a bar ta a baya ba




Dan wasan gaban nan na Barcelona watau Neymar Jr. ya jefa kwallon san a 100 a zaman sa a Barcelona jiya a wani wasa da su ka buga. Barcelona dsi ta lallasa Kungiyar Granada da ci 4- 1 a wasan na La-liga.

Hakan na nuna cewa da wuya dan wasa Neymar ya bar Barcelona bayan da ya ci kwallon san a 100 a cikin wasanni 177 rak bayan zuwan sa Kungiyar shekaru 4 da suka wuce. Neymar da Messi da Suarez dai sun addabi 'yan bayan Duniya




Haka kuma Real Madrid ta lallasa takwarar ta Alaves da ci 4-0 watau har da nema. Kusan dai Barcelona da sauran manyan Kungiyoyin kasar Spain sun gaza cin kungiyar Alaves a gida. Wasanni sama da 50 kenan a jere kullum sai Real Madrid ta jefa kwallo.

Ku na da labari cewa FIFA ta Duniya ta dakatar da babban dan wasan nan na kasar Argentina Lionel Messi da ke Barcelona. Dan wasan gaban ba zai buga wasanni 4 ba bayan an same sa da laifin fadawa Alkalin wasa maganganun da ba su dace ba.



[NAIJ Hausa]

Kare ya ceci mutane daga hannun Boko Haram


Ikon Allah: Wani kare ya hana a tada bam




kare yayi sanadiyar cecen rayuwar mutane masu dinbin yawa a Garin Borno inda ya hana wata yarinya tada bam a wani gidan biki

Sai ace ko karen nan yayi mutuwar shahada kenan inda ya rasa ran sa yana kokarin kare na Jama’a? Wannan kare dai yayi sanadin karin kwanan mutane masu yawa yayin da ya hana wata yariniya harba bam a wani gidan biki.

Mun samu labari cewa wannan kare na wani mai gida ne a kusa da inda wannan abu ya faru. Karen dai ya hana wata ‘yar yarinya kutsawa cikin Jama’a domin ta harba bam wanda da ya ga bayan mutane da dama a cikin wani gida da ake sha’anin biki.

Jami’an ‘Yan sanda su ka ce ko da karen ya hango wannan yarinya ta auka cikin Jama’a sai ya bi ta, nan fa aka yi ta kaya-kaya har bam din ya tashi, nan ne aka rasa wannan kare. Wannan abu dai ya faru ne a Garin Belbelo da ke Jihar Borno.



[NAIJ Hausa]

Sunday, April 2, 2017

Mutane 3 da suka fi kowa basira a Duniya


 Mutane 3 da suka fi kowa kwakwalwa a Duniya; Dan Najeriya ya taka rawar gani


Kwankwalwa dai baiwa ce kurum daga Ubangiji ba kokari bane ke bada ta. A kan auna kaifin kwakwalwa ne da mitar IQ. Yanzu haka dai an gano wadanda su ka zarce kowa kaifin basira a Duniya, a cikin jerin kuwa har da wani ‘Dan Najeriya.



1.      Terrence Tao
Harsashe ya nuna cewa duk fadin Duniya babu mai kwanyar Mista Tao wanda rabi Ba’Amuruke ne kuma dayan barin sa Dan kasar Sin wanda aka haifa a Australia. Makin sa na IQ ya fi na kowa inda yake da 230. Tun yana shekara 20 ya gama Digiri na uku yanzu kuwa Farfesa ne tun yana dan shekara 24.

 2.      Chris Hirata
Christopher na da makin IQ har 225 shi ma wani dan baiwan ne wanda ya kammala Digiri na uku watau PhD tun yana dan saurayin sa. Yanzu haka Malamin Jami’a ne a Birnin Kalifonia.


3.      Kim Ung-Yong
Kim Injiniyan gina-gine ne kuma mutumin kasar Koriya wanda tun kafin ya shekara a Duniya ya fara magana. Yana da makin IQ 210 don haka kuwa yana cikin masu basirar Duniya





A cikin dai wannan jeri akwai wani Dan Najeriya da ya zo cikin sahun 10 na farko mai suna Philip Emeagwali. Emeagwali ba dai basira ba, an haife sa ne Garin Akure ko dai dai Inyamuri ne.



[NAIJ Hausa]


Saturday, April 1, 2017

HUDUBAR JUMA’A DAGA MIMBARIN ITN-ZARIA


HUDUBAR JUMA’A DAGA MIMBARIN ITN-ZARIA



Godiya ga ni’imar Allah daga Bakin Imam Sheikh S. S Abubakar


A’udhu BilLahi minasshaidan Ar-Rajim, BismilLahir Rahman Ar-Raheem,

Dukkan Godiya sun tabbata ga Allah SWT, shi ne mai karamci da baiwa ga bayin Sa. Muna godiya da yabo gare sa Madaukakin Sarki. Shi ne mai yin falala dabam-dabam ga bayin sa da kuma nau’o’i dabam-dabam na ni’ima. Muna shaidawa lallai babu abin bauta da gaskiya face Allah SWT, Shi kadai yake, babu abokin tarayya a gare Sa. Muna shaidawa lallai Shugaban mu, Annabi Muhammad SAW Bawan Allah ne kuma Manzon Sa ne.

Bayan haka:
Ya ku ‘Yan uwa mu ji tsoron Allah Madaukakin Sarki kuma mu gode maSa bisa ni’imomin da yayi mana, mu kuma sani cewa Allah ne kadai mai ni’ima kuma gare Sa muke fatar ayi mana ni’ima a Duniya da kuma lahira. Allah SWT yana cewa: Idan ku kace za ku kidaya ni’imomi na, ba za ku iya lissafe su ba. Lallai Allah mai yawan gafara ne mai kuma yawan jin-kai.

Saboda haka Bayin Allah ku gode masa bisa ni’imomin da yayi maku domin kuwa godiya na daga cikin dalilan su ke sa Allah ya kara kuma ya wanzar da ni’ima. Don saboda kafircewa ni’imar Allah kuma sai ya zama ni’imar nan ta tawaya ko kuma ta gushe gaba daya. Allah SWT yana cewa a Kur’ani: Idan ku ka gode, lallai Ni zan kara maku...Lallai kuma idan har ku ka kafirce, azaba ta tana da tsanani. Allah Mai tsarki yana dada fada a cikin Kur’ani inda ya bada misali da wata Al-karya Yake cewa tana cikin aminci da kwanciyar hankali da arziki, amma sai su ka kafirce daga ni’imomin Allah, sai kuwa aka dandana masu tufafin yunwa da tsoro saboda abin da suka kasance suna aikatawa na kafirci.

Ya ku ‘yan uwa ya ake godewa Allah da ni’imomin sa? Wannan yana cikin dagewa wajen bin umarnin Ubangiji Ta’ala muddin aka ce Allah yayi umarni a aikata kaza ko a bari sai mutum yayi iyawar sa ya aikata ko ya bari in dai har wannan umarni ya zo daga Littafin Allah ko bakin Annabin Sa SAW. Lallai fa mai sabon Allah ba mai godiya bane ga Ubangiji ko da ya ta furta cewa ‘Na godewa Allah.’ Ina amfanin mutumin da ke fada da harshe cewa yana godiya alhali yana ta sabawa Allah? Ko shin wannan mutumi ba ya tsoro a ce da shi karya ka ke yi. Allah SWT da ya tashi sai ya hallice ka mutum kuma mai hankali, sannan kuma ya ba ka musulunci da sauran ni’imomi, don haka Ubangiji ya cancanci godiya. Mu sani dai cewa mafi girman ni’ima kenan shiriya zuwa ga Musulunci. A yayin da ku ke Musulmai masu imani wasu na can suna dimuwa; wasu na cikin fushin Ubangiji na take sani, wasu kuma na cikin duhun Jahilci ba su ma gane wanene Ubangiji ba. Saboda haka duk wanda Allah ya azurta da Musulunci ya samu abu biyu; sanin gaskiya da kuma biyayya gare ta. Wannan ya bambanta mutum da Yahudu da su ka take sani da kuma Nasara da ba su san gaskiya ba su ke cikin duhun jahilci.

Manzon Allah SAW ya nuna mana yadda ake godiya ga Allah SWT ban da irin Salloli da yake yi, duk wani karamin abu sai Manzo SAW ya godewa Allah. Sai mu tambayi kan mu kamar yadda Annabi SAW yake tsayawa Sallar Nafila cikin dare, shin kai raka’a nawa kayi jiya cikin dare domin nuna godiyar ka ga Allah? Manzon Allah ya kan yi addu’ar godiya ga Allah da ya raya sa kuma bayan ya tashi daga barci. Kai ko jiya da ka farka ka fadi haka? Ko ba ka san cewa ni’ima ba ce da Ubangiji Ta’ala ya farkar da kai bayan ka kwanta. Ko da ka shiga ban-daki ka yi uzuri ka fito cikin sauki kayi irin abin da Annabi SAW yake yi? Annabi SAW yana addu’ar godiya ga Allah da ya samu damar kawar da abin da ke cikin jikin sa. Sannan Manzon Allah SAW ya kasance idan ya ci abinci (duk da Annabi SAW ba ya cin wani abinci sosai) yana godiya ga Allah iri dabam-dabam. Kai yau bayan ka karya kumallo da safe mai ka fada na godiya, watakila har da gyatsa kayi. Ko ba ka dauka cewa kokon da kosai da ka samu ni’ima bane? Wani bai samu ko kokon da ka samu ba domin ya sha, wani kuma ga kokon amma bai isa ya sha ba saboda wani hali na rahin lafiya ko aminci. Haka kuma Manzon Allah SAW yake yi idan zai kwanta barci cikin yini, watau dai kullum Manzon Allah cikin godiya yake. Shin mu haka muke? Ya kamata muyi koyi da Manzon mu Annabi SAW. Mu sani cewa duk wata ni’ima daga gare sa ta ke; babu mai badawa ko hanawa face shi. Idan har ka rasa wata ni’ima ta Duniya ka da ka zargi kowa kana cewa ‘Wane ya hani ni’, Allah Madaukaki ne bai ga dama ba. Haka kuma idan Allah Madaukaki ya ba ka kar ka butulce masa kana ‘Wane ya bani’, ba kowa bane shi face dan-aike. Allah SAW yana cewa a Kurani cewa: Duk abin da ku ka gani na ni’ima daga Allah ne, don kar ka dauka wani ya isa ko dabarar mu ce!

Allah ka ba mu fahimtar Addini ya sa ya amfane mu gaba daya. Allah ya karba mana ya tseratar da mu daga azabar wuta mai radadi, ya shigar da mu cikin gidan ni’ima. Allah yayi dadin tsira ga Annabin mu Muhammad SAW da Iyalan Sa da Sahaban Sa musamman Khalifofin Sa shiryayyu.

Allah ka taimaki Musulunci da Musulmai ka kuma kaskantar da Kafirci da Kafirai. Allah ka kare mu daga wata fitina da damuwa. Allah ka kara mana ni’imar ka da samun yardar ka. Allah ka tara mu a kiyama tare da Annabawan ka da kuma zababbun bayin ka.

Allah ka taimaki kasar mu ka taimaki shugabannin mu; ka kama hannayen su ka wanzar da al’amurar su. Allah ka shiryar mana da su ga abin da kake so kuma ka yarda da shi.


Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga Masallacin I.T.N-Zaria.
Muhammadmalumfashi@gmail.com          
Twitter: @Ya_waliyyi



Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...