Sunday, December 11, 2016

Wani Sarki ya rasu a hadarin mota

– Sarkin Ijio na Kasar Oyo ya samu rasuwa ta hanyar hadarin mota

 


– Mai martaba Amunijio na Ijio ya afkawa wata Gingimari ne yayin da yake tuki

 


– Kwanan ne dai aka kai Sarki Okunade Adegoke kara Kotu

 

 



Hadarin mota yayi sanadiyyar mutuwar wannan Oba


Mai Girma Sarkin Ijio ya rasa ran sa bayan da ya hadu da wani hadarin mota. Sarkin yana tafiya ne inda zai koma Fadar sa cikin dare. Sarki Okunade Adegoke ya kasance shi kadai ne a cikin motar sa yana tuki yayin da wannan abu ya faru. 

Mai Martaba yayi karo da wata gingimari ne a Ranar Larabar nan cikin dare, kimanin karfe 10:00. Ko da mutane suka kawo dauki, an samu Sarkin ya cika. Wadanda suka ga abin, sun ce Sarkin ya aukawa wannan katuwar gingimari ne yayin da yake kokarin kaucewa wata motar. 

Kwanan nan ne dai aka kai karar Sarkin Kotu, inda ake kukan yana yi wa Talakawa kwacen gonaki da gidaje. An zargi Sarkin da karya kasuwancin Jama’a da dama ta hanyar turo ‘yan ta’adda su karya mutum.

A watan Jiya ne kuma Gwamnatin Jihar Edo karkashin Tsohon Gwamna Adams Oshiomole ta tsige wani daga cikin masu Sarautar Kasar, An tunbuke Sarki Anselm Eidenojie. Mai Girma Anselm Eidenojie shi yake rike da Kasar Uromi da ke Yankin Arewacin Esan na Jihar Edo. Ana zargin mai martaba da yi wa wata mata shegen duka.

[NAIJ Hausa]

Saturday, December 10, 2016

Hudubar Jumu’a daga Masallacin I.T.N

NEMAN HALAL A DUNIYA DOMIN LAHIRA

 

Hudubar Jumu’a daga Masallacin I.T.N Zangon-Shanu, Zaria


 

Daga Bakin Sheikh Salihu S. Abubakar

 

 

BismilLahir Rahmanir Rahim.

Dukkan Godiya ta tabbata ga Allah, Shine wanda ya kammala mana addinin mu, kuma ya cika mana ni’momi. Muna godiya da yabo gare Shi Madaukakin Sarki, Shine yayi mana wata babbar baiwa ta hanyar aiko da Mafificin ta’likai duka-Shugaban mu, Annabi Muhammad SAW. Muna shaidawa cewa lallai babu abin bautawa da gaskiya face Allah, shi kadai ya ke, ba shi da abokin tarayya. Shi kuma Allah, yayi alkawari ga masu tsoron sa cewa zai saka su cikin Gidan Aljanna-Gida na Aminci. Muna shaidawa lallai Shugaban mu, Annabi Muhammad SAW Bawan Allah ne, kuma Manzon sa, wanda yake mai Madaukakin daraja da kuma mafi daukaka na mukami.
Bayan haka:
Ya ku ‘Yan uwa, lallai Allah SWT, tsarki ya tabbata gare sa tare da daukaka, ya fadi a cikin Littafin sa mai girma. Allah SWT yace: ‘Lallai, Hakika, A gare ku akwai kyakkawan abin koyi a cikin tafarkin Annabi Muhammad SAW, ga duk wanda yake fatan samun yardar Rahamar Allah da kuma Ranar Lahira...’ Saboda haka, babu makawa gare mu, lallai ne mu yi duk abin da za mu iya saboda mu yi koyi da irin halayen sa da dabi’un Sa, Shi Manzon Allah SAW. Shi ne abin koyi, Shi ne jagora da ya kamata mu bi. Kuma babu lokacin da muka fi bukata muyi koyi, kuma mu siffantu da dabi’un sa kamar wannan lokaci da muke ciki. Shi SAW ne ya karantar da mu abin da wannan Duniya ta ke ciki gaba daya. Shi SAW ne ya fada mana cewa Duniyar nan Halittar Allah ce, kuma Allah ya kawo mu wannan Duniya domin jarrabawa, kuma za mu koma gare sa. Shi SAW ne ya mana bayanin menene manufa a cikin wannan rayuwa ta duniya, Shi ne yayi mana bayanin tafarkin da ya kamata mu bi a cikin rayuwar mu ta Duniya. Saboda haka, duk wanda yayi koyi da irin shiriyar Sa ya rabota, ya kuma yi nasara. Wanda kuma ya aikata sabanin haka, ya bata, kuma ya halaka. 
Shi Annabin mu, SAW ya karantar da mu cewa ita rayuwar Duniya tana da Manufofi wadanda suke guda 2. Manufar farko ita ce Bautar Allah, sannan manufa ta biyu ita ce mu rayar da wannan samuwa watau mu raya wannan Duniya baki daya. Ko da yake wannan manufa ta biyu, bangare ne na wancan na farko. Ma’ana; aikin da za muyi wajen raya duniya, duk wani bangare ne na Aikin Bautar da Allah SWT ya wajabta mana. Allah ya fada cikin Al-Kurani cewa: ‘Ban halicci mutane da Aljani ba, sai don su bauta mani’. Kuma shi Allah Madaukaki SWT ne yace; shi ne wanda ya tsirar da halittar ku daga cikin Kasa, kuma ya sa ku raya ta. Watau ku za ku raya ta, ku gyara ta, ita Duniya.
Allah SWT ya umarci Dan Adam yayi riko da sababi a cikin rayuwa, wanda za su zama daukaka ga Al’ummar mu da kuma gyara rayuwar mu ta duniya domin ta zama matakala zuwa Lahira.  Kuma wannan Addinin na mu kamar yadda Manzon mu Annabi Muhammad SAW ya karantar da mu, ya hana mu shantakewa da lalaci da ragwanci. Saboda ba zai yiwu ba a cin ma abin da Allah yake so a ban Kasa da lalaci da kuma ragwanci. Allah Madaukakin Sarki ya fada mana cewa: ‘Shi Allah ne wanda ya sanya Kasa ta zama horarriya, saboda haka, kuyi ta yawatawa cikin sasannin ta, kuma ku ci daga cikin arzikin Allah, kuma gare sa za ku taru.’
Saboda haka Musulunci ya karantar da duk abin da ake bukata wajen rayar da Duniya, ta wannan hanyar ne kuma za a samu gina lahira. Musulunci ya kuwa kwadaitar da cewa a yawata a cikin Kasa, a zurfafa cikin sasannin Kasar wajen samun arziki mai albarka wanda yake cikin tudu da kuma ruwa. Tare da kuma karfafa gwiwa da Musulunci yayi a kan a tashi ayi aiki tukuru, ya zo a cikin Hadisin da Miqdam ya ruwaito cewa: Annabi SAW yace: ‘Babu wani abinci da daya daga cikin ku zai ci, da ya fi abin da mutum ya aikata da hannun sa, ya samo...’ Sai Annabi SAW ya cika da cewa kuma Lallai Annabi Dawud AS, ya kasance yana ci ne daga aikin hannun sa. 
[Imamul Bukhari ya kawo wannan Hadisi.]
Saboda haka shi Musulunci, wanda Manzon Allah SAW ya zo mana da shi, kira ne baro-baro da cewa duk wanda ya yarda da Musulunci ya tashi yayi aiki tukuru domin tabbatar da Duniya da raya ta, ta yadda za a jawo Alheri ga dukkan Duniya. Shi Musulunci ya girmama al’amarin aiki tukuru, ya kuma sa hakan ya zama hanya da zai kai mutane ga cigaba da daukaka a nan duniya, kuma ya zama ibada.
Ayoyin Qur’ani sun kwadaitar da karfafa gwiwa wajen tashi da yin aiki tukuru a wajen al’amarin rayuwa da kuma abin da zai kawo abinci da tufafi da sauran bukatu na mutum da iyalan sa. Saboda haka ne Allah SWT yayi umarni da Sallar Jumu’a, bayan Sallar kuma yayi umarnin a bazu cikin Kasa domin a nema daga cikin falalar Allah. Allah Madaukakin Sarki yace: ‘Idan an gama Sallar Jumu’a, ku bazu a cikin Kasa, ku nema daga cikin Rahamar Allah, amma ku rika tuna Allah ko ku samu babban rabo.’ Wannan umarni ne Allah, kamar yadda aka yi umarni da azo Masallaci ayi Sallar Jumu’a, haka aka yi umarni da a yadu a ban Kasa, a nema daga cikin falalar Allah bayan an tashi daga Masallacin.
Hakika wannan Addini na mu na Musulunci yayi mana bayani cewa duk wanda yayi ta kokari domin neman abincin sa da na ‘ya ‘yan sa ta hanyar halal, yana daidai da darajar wanda ya mutu shahidi a wajen yaki ko kuma wanda aka sa gadi ya tare kofofin da abokan gaba za su kawo hari. Saboda haka, yana daya daga cikin wadanda suka yi aiki ta hanyar daukaka kalmar Allah. Akwai Hadisi daga Ka’ab Dan Ujrah RA yace; Wani mutum ya wuce ta gaban Manzon Allah, sai Sahabbai suka ga irin kirar jikin sa da kuma kuzarin sa, wannan abu ya ba su sha’awa, sai suka ce da RasululLah SAW cewa dama ace wannan mutumi yayi amfani da kuzarin sa cikin tafarkin Allah. Sai Manzon Allah SAW yace ai in dai yana kokari ne domin nemawa kan sa da iyalin sa; kananan yara, abinci ne, to yayi cikin tafarkin Allah. Yace idan kuma ya fita ne domin samun abin da Mahaifan sa-da suka tsufa za su ci, shi ma duk cikin Tafarkin Allah ne. Manzon Allah SAW yace idan har ya fito ne domin samun abin da zai ci, ya kare kan sa daga fadawa sharri, to wannan duk cikin tafarkin Allah ne. Amma idan ya fito ne domin ya samu abin da zai yi alfahari da shi, ko ya tara arziki, to wannan yana cikin Tafarkin Shaidan. Imamul Tabarani ya fito da wannan Hadisi.
Shi kuma Musulunci bai ma tsaya ga karfafa mana gwiwa kawai ba, ya kuma neme mu da muyi aiki da kyau; babu magudi da ha’inci. Wannan shi ne abin da Manzon Allah SAW ya koyar da mu-kyautata aiki. Wannan saboda mu samu soyayyar Allah da kuma Rahamar sa. An sami Hadisi daga Aisha RA tace: Manzon Allah yace: Lallai Allah mai girma SWT yana so idan mutum zai yi wani aiki, ya tsaya yayi sa za-kyau. Allah SWT da kan sa yana fada mana cewa: Ku kyautata domin Allah yana son masu kyautatawa.
‘Yan uwa ina so ku rike wannan daga cikin Hudubar; Idan za mu rike Addinin mu da kyau, mu rika biyayya kuma mu tashi muyi aiki tukuru; don babu wani aiki na Duniya-wanda yake dabam da na Lahira, wannan ba karantawar Addinin Musulunci bane. Kowane aikin Duniya, ana yin sa ne domin neman Lahira, ko da a zahiri za mu ga cewa an ci moriya a Duniya, ana aikin ne domin Lahira. Duk wanda ya dauka cewa akwai wani aikin neman Duniya da kuma na Lahira, bai fahimci Addinin Musulunci ba. Wane lokaci ne na Allah, wane lokaci ne kuma na mutum? Duk lokacin ka na Allah SWT ne; daga kasuwanci, aikin Gwamnati, zuwa noma dsr. Duk aikin da mutum yake yi, idan har ka tsaya kayi aiki yadda Allah yace, to wannan aikin ibada ne kuma zai ba mutum matsayin shahidi, haka wannan lamari yake. Saboda haka, ya kamata kowa ya fahimci wannan, muddin muka fahimci wannan, za mu gina rayuwa mai kyau a nan Duniya da kuma Lahira.
Allah ya bamu fahimtar AlQurani mai Girma, ya amfane mu gaba daya da abin da ke cikin sa na Ayoyi masu wa’azi da hikima. Allah ya tserar da mu daga Azabar sa mai radadi. Allah kayi dadin tsira ga Annabin Ka SAW da iyalan sa kamar yadda ka yi dadin tsira ga Sahabban Manzon Allah SAW da wadanda suka bi bayan su bisa tafarki madaidaici. Allah ka kama hannuwan wadanda ka Shugabantar da su a matakai dabam-dabam zuwa ga abin da kake so ka yarda shi.



Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga Zaria.

Samari fiye da 14,000 suke fama da Kanjamau a Benue

– Dubunnan Samari ke dauke da kwayar cutar Kanjamau a Jihar Benue

 

– Bincike ya nuna cewa matasa sama da 14,000 ke tare da wannan mugun cuta

 

– Shugaban masu Kanjamu ya bayyana haka

 

Shugaban Kungiyar masu cutar Kanjamau ya bayyana cewa samari da ‘yan mata fiye da 14,000 ke fama da cuta Kanjamau-watau HIV/AIDS a Jihar Benue. Shugaban masu Kanjamau din ya bayyana haka ne wannan makon a Garin Makurdi.

Shugaban masu Cutar sida yayi wannan jawabi ne a Ranar Kanjamau ta Duniya wanda aka yi kwanan nan. Yake cewa abin yayi yawa kwarai, Shugaban yake cewa ana shirin samar da magunguna ga ‘Ya ‘yan Kungiyar domin kawo saukin cutar.

Shugaban Kungiyar, Fabian Tor yace idan aka samu magani, shi zai kawo sauki ga masu cutar. Darektan Kungiyar UNAIDS na Cutar Kanjamau a Kasar, Dr. Camara Bilali yace Jihar Benue na cikin Jihohin da suka fi kowa fama da cutar Kanjamau. 

Kungiyar UNAIDS ta Majalisar Dinkin Duniya mai kula da Kanjamau tace ya zama aikin mu gaba daya mu tashi tsaye wajen yakar wannan cuta. Kwanan ne a aka gano cewa mutane kusan 10,000 ke dauke da kwayar cutar ta Kanjamau a Jihar Legas.


[NAIJ Hausa]







Friday, December 9, 2016

Celebrating Maulud of Rasul SAW

CELEBRATING THE BIRTHDAY 'MAULUD' OF PROPHET MUHAMMAD (PBUH).





At this time of the year Muslims all over the world are celebrating birthday of Prophet Muhammad (PBUH) 'Maulud', in some countries like ours it's a national holiday.
All Islamic scholars agreed to the fact that Maulud festivals are innovations, not practiced during the time of the Prophet neither his companions. In other words the period Prophet Muhammad PBUH described as best of generation. (Tirmidhi, Sahih Bukhari & Muslim)

The question is should we, still celebrate Maulud?
Some Scholars however believe that Maulud as an Innovation, is a good one...
All innovations are misguidance- Tirmidhi
Some might still say NO, like in the works of Usman D. Fodio he said that innovation (Bidi'a) can be categorized into good, bad, recommended etc. This classification itself is another bidi'a as it's not known in the early Islam era. While others are on the side that Bidi'a means aberration not innovation, but to understand this famous Hadith above, another Hadith from Nana Aishat (RA) explains more:
“Whoever introduces something new into this matter of ours that is not from it will have it rejected.” - Bukhari & Muslim
In another narration:
“Whoever does an act that is not in accordance with this matter of ours will have it rejected.”-Muslim 

This not only counter the proof that Bidi'a means something 'new' but also shows the Prophet was referring to the religion of Islam when he said 'this matter of ours', once he told his companions you know more than I, when it comes to your ‘dunya’ (this world).
To even make mention of wearing jeans today, having a Facebook account, flying in an airplane etc., as bidi'a is no point. When you travel for Hajj by Dana air how much reward have you more than one who flies Mangal air? Do you expect 10 rewards wearing jeans trouser over one who wears not? When Aishat (RA) said the Prophet mentioned that 'He will have that which he brought to the religion rejected', she was referring to acts of worship. 

"In the Bounty of Allah, and in His Mercy -therein let them rejoice." That is better than what (the wealth) they amass. Yunus: 58
The mercy in the above verse refers to Prophet Muhammad (PBUH) according to most exegetists, as so Maulud should be celebrated for the love of Muhammad (PBUH). No doubt his coming was a blessing to all humankind and should be rejoiced! The question is, how do we rejoice? And the answer is in the companions of the final Prophet himself, whom the Qur'an was revealed at their time and they had the best teacher in the world to learn from.
Could it be possible those that lived over 600 years after revelations have stopped, understood this verse more the companions that were present at the time of revelations? More than the Abdullah bn Abbas (The Prophet himself often pray to his Lord): "O Lord, make him (Bn Abbas) acquire a deep understanding of the religion of Islam and instruct him in the meaning and interpretation of things."
O Messenger of Allah, you are more beloved to me than everything except for myself.” The Prophet said, “No, by the one in whose Hand is my soul, until I am more beloved to you than yourself.” Umar said, “Indeed, now I swear by Allah that you are more beloved to me than myself.” The Prophet said, “Now you are right, O Umar.”-Bukhari
Hadith from Umar showing his love for the Prophet, yet never celebrated Maulud. Umar was the caliph (Ameer-el-Muminin) but neither in his time nor the time of the other rightly guided caliphs was Maulud celebrated! Despite the unrivaled, unequivocal and unconditional love these men had for their Prophet.
..Those of you who live long after me shall witness great differing. So upon you is (to follow) my Sunnah, and the Sunnah of the rightly-guided Caliphs, hold tightly to it and bite onto it with your molar teeth.
-Sunan Abi Dawud

I've seen in writings that since there's no any clear prohibition on Maulud then there's no problem with it. Going as far saying 'All that's not haram (prohibited) It is halal (allowed)'. Again, it's not haram, that's why it's bidi'a.
And whatever the Messenger gives you, take it, and whatever he forbids you, leave it. And fear Allah: truly Allah is severe in punishment. 59:7
You can understand from the above verse that you take only what the Prophet gives (don't innovate which he didn't), and leave whatever he forbids.
It's bidi'a to celebrate it because it was never done at the early period of Islam not only that it wasn't known at the time of Prophet Muhammad (PBUH) himself.  
Early Scholars said this about Bidi'a:
"Indeed the most detestable of things to Allaah are the innovations."-Ibn Abbas
"Innovation is more beloved to satan than sin, since a sin may be repented for but innovation is not repented for...”-Sufyan Thauri

All matters of religion are strictly dictated and prescribed in the Shari’ah. Now how do you celebrate Maulud? A lot of questions arise from this. By God, there is no act of Religion which the Prophet hasn’t told his people about, By Allah only no even which will benefit his Ummah by the weight of wool.
Hadrat Ismaila Hiqqi, A Darika Sufi said Maulud is a tribute to beloved Prophet... and should be clear of evil things.
The last question, is the Maulud celebrations of today free of evils? So what even if they are?
..This day I have perfected for you your religion and completed my favor upon you and have approved for you Islam as religion...-Quran 5:3 

May the soul of Malik bn Abbas rest in peace, who said 'whatever wasn't part of the religion on that (day the verse above was revealed) will never be part of the religion….About 500 years after his statement Maulud was introduced as part of this Deen! Allahu Akbar!  

No doubt the Companions of the Prophet SAW and their Companions RA and the Companions of the Companions; who Rasul SAW said are the best of generations, never were narrated of them practicing it. Then the best is to refrain from such acts. These were the people who stayed and lived with Rasul-Lah SAW. Is following the pious generation not worthy of emulation?

We should not only celebrate the Prophet a day or an overnight, but all our lives. In the day and night, at home and abroad, in our homes and workplaces, young and old, dressing, eating, drinking, saying and writing. The best way to celebrate the best of mankind is by following what he commands us and refraining from that which he forbids. 

Allah ka kara mana son Manzon Tsira Annabi Muhammad SAW.
Amin.

 

This Article was published last year by Muhammad Malumfashi
M. Malumfashi is on twitter @ya_waliyyi
This Ya-waliyyi is not a Sufi.




Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...