‘Riko da Amana’-Daga Bakin Imam Ustaz Dr. Sa’eed Yunus
Assalamu Alaikum wa Rahmatul
Lah,
Dukkan yabo da godiya sun
tabbata ga Allah SWT wanda yayi umarni da a rike amana. Ubangiji yayi mana hani
da yaudara da ha’inci. Allah yayi alkawarin azaba ga wadanda su ka ci amana.
Allah yana son Bayi masu rikon amana. Mu na shaidawa babu abin bauta da gaskiya
sai Allah. Ina shaida cewa lallai Annabi Muhammadu, Bawa ne kuma Manzom Allah.
Annabi ya kwadaitar da Mutane game da amana ya kubutar da su game da rashin
amana. Aminci su tabbata ga Annabi Muhammadu da wadanda su ka bi tafarkin sa.
Bayan haka:
Ku sani cewa mafi alherin aiki
shi ne littafin Allah da shiriyar Annabi SAW sannan kuma mafi sharrin al’amari
shi ne wanda aka kirkira. Duk abin da aka kirkira a cikin addini bidi’a, ne
kuma bidi’a bata ne, kuma bata na wuta. Allah ya kare mu daga wuta. Ya ‘yanuwa
Allah yayi umarni a cikin ayoyi masu yawa a Al-kur’ani a karshen Suratul
Baqarah da kuma Suratul Nisa’i bayan nan kuma Allah yayi magana a cikin Suratul
Anfali da har Suratul Ma’arij.
‘Yan uwa Al-Kur’ani yayi magana
game da wannan abu mai girma, ya kuma mutane su ke wasa da wannan abu da Allah
ya girmama shi. A cikin Suratul Ahzabi, Ubangiji ya fada mana cewa Sammai da
Kassai da Duwatsu sun gaza rike amanar da Allah ya bijira masu inda su ka ce ba
za su iya ba. Ku duba girma da nauyi da kuma karfin dutse amma ‘Dan Adam yace
ya ji zai iya rike wannan amana ta Allah. Ubangiji ya tambayi kowace sama da
kasa duk su ka ce ba za su iya ba. Shi kuwa ‘Dan Adam ya karba. Annabi Muhammad
a wani hadisi yana cewa ‘Ka bada amana ga wanda ya amince maka’ Ya tabbata
cikin sunnar Annabi cewa; ha’inci yana cikin halin Munafukai. Akwai hadisi daga
Anas Dan Malik da yake cewa Annabin Rahama SAW ba ya huduba face sai yayi magana
game da amana. Annabi ya kan ce: ‘Babu Imani ga wanda bai da amana, sannan kuma
babu addini ga wanda ba ya cika alkwari’.
‘Yan uwa ku dube mu ku gani
don Annabi yace maras amana bai da Imani, sai kowa ya dauki kan sa; ko a wace
Ma’aikata yake aiki.Yanzu mu na zamani a wani lokaci da ake kiran ‘Corruption’
yayi yawa. Zalunci yayi yawa har ta kai ana cewa wanda ya hana zalunci shi ne
azzalumi. Inalillahi wa inna ilaihi raji’un! Matsayin amana matsayi ne mai
girma ‘Yan uwa. Amana kamar yadda Malamai su kayi I’tifaki shi ne abin da Allah
ya daurawa Bawa kuma wanda ya tsayu da hakan ya bada amana. Allah yace kayi
sallah da azumi, ko kayi sallar? Ka yi azumi kamar yadda Annabi ya koyar? Don
Annabi ya bayyana yadda ake wadannan ibadu saboda haka hakika duk wanda ya ki
yin hakan ya cuci kan sa.
Ya ku ‘Yan uwa na addini, daga
cikin amanar da Allah yake so a rike shi ne kadaita Allah babu shirka da guru
da laya da hake-hake da shan jini watau amanar Tauhidi. Kuma idan za kayi abu
kayi don Allah, ban da riya. Abu na biyu kuma shi ne rike Sunnar Annabi
Muhammad sawu da kafa (ba da baki ba) watau a gani-a kasa. Duk wanda ka ke so
kayi biyayya a gare sa kuma ba biyayya ta shirme ko kirkirar abubuwa ba. Idan
ka na son Manzon Allah sai a gani a kasa wajen tsayawa bin sa tsayin daka. Wani
Sahabi ya zo da sandar sa, ya tsaya wajen wata bishiya yace shi ma sai yayi
irin yadda Annabi SAW yake yi da sandar sa a lokacin yana da rai. Wannan ita ce
madarar soyayya ta Manzon Allah, ba rawa ba, kuma ba kida ko raye-raye ba, ko
mata su fito su na shirme ba! ‘Yan uwa ku sani cewa bidi’a bata ce kuma ha’inci
ne ga Annabi Muhammad. Duk wani ‘Dan bidi’a sai ya kawo lasisin aikata abin da
ya aikata a Ranar lahira. Malamai su na cewa duk wanda yayi wata bidi’a yana
tuhumar cewa Annabi bai isar da wani sako bane, kuma ta tabbata Annabi ya
kammala cikar da sakon Musulunci. Duk wanda yake bidi’a sai ya shirya abin da
zai fadawa Allah a gobe kiyama.
Abu na gaba shi ne hukunci da
shari’ar Allah, idan aka samu inda ake hukunci da shari’ar da ba ta Allah ba,
to sai ka ki ta. Yanzu mu na lokacin da ake da wasu da ake kira ‘Lawmakers’
wadanda ke tsara dokokin kasa. Wadannan mutane da Alkalai da ake da su Musulmai
ne har yanzu kuma ka da wanda ya kafirta su gaba daya. Sai dai ya kamata su ji
cewa hukuncin Allah shi ne hukunci. Allah yana cewa: Hukuncin jahiliyya su ke
so? Su wa su ka fi masu bin hukuncin Allah ne? Me bin hukunci na Allah shi ne mafi
biyayya ga hukunci mai kyau. ‘Dan uwa idan har ka samu kan ka a cikin Majalisa
ku na cikin masu tsara dokokin kasa, to ka sani cewa hukuncin Allah ya fi. Amma
abin bakin ciki, sai ka ga Musulmi ya tafi Kotun Musulunci an yi masa shari’a
da littafin Allah amma ya tafi yana kiyayya yana zage-zage.
Duk abin da na fada ya shafi
bangare ne na akida, yanzu zan yi magana ne a kan ibada. Ibada gaba dayan ta
amana ce a wuyar Musulmi namiji da mace. Sallah da alwala da wanka da zakkah da
aikin Hajji duk amanar Allah ce. Dole a aikata yadda Ananabi ya koyar, Annabi
yace ku koyi aikin hajjin ku daga gare ni. Idan ka saki wannan abubuwa to ka
sani cewa ka ci amanar Allah.
Yanzu an samu shugabanci na
gaskiya a Kasa sai kuma abin mamaki wasu ‘yan uwan mu su na kiyayya ga wannan
tafiyar ko kuma wadanda aka jawo su kusa su na ta ha’inci ga Allah da kuma
shugaba da al’umma, sai dai ku sani cewa kun ha’inci kan ku ne don kuwa
Ubangijin ka yana nan a madakata. Zumunci, hakuri, ‘yanuwantaka da sauran su
duk amana ne, haka nan kuma duk abin da ya shafi karya da ha’inci da wauta da
girman kai da zina da barayi (na biro da na dare da sauran su) duk su na cikin
cin amanar Allah kuma lokaci kurum Ubangiji ya ke jira. Allah ya shiryar da mu!
Daga cikin abubuwan da Allah ya nemi mu kiyaye Jama’a, mu san cewa akwai
kiyayar baki daga ‘giba’ watau gulma, rada da annamimanci. Sannan mu kiyayi
karya da hassada da kulli a cikin zuciya. Allah ya shirya mu ya sa mu cikin
Bayi nagari.
Bayan haka:
Huduba ta biyu tana godewa
Allah, da kuma yabo ga farin jakadar Allah, tana cewa mu ji tsoron Allah wajen
amanar mu. Allah zai tambaye mu game da amanar da ya ba mu; za a tambayi kowa
game da gidan sa (ka daina kallon shugabanni kurum) Hadisi na ‘Dan Umar RA
wanda ya ke cikin Bukhari da Muslim cewa kowanen mu abin tambaya ne. Mu sani
cewa ilmin da ake koyo a a zaure da Boko da Islamiyya duk amana ne. Malamai
masu karantarwa ku fadawa Jama’a gaskiya haka kuma Dalibai ku rike amana. Ka da
a samu shaidar zir (na ba kayi karatu ba sai ace kayi) kamar yadda ake samu a
yau daga sama har kasa. Iyaye da yara su na satar jarabbawa, lallai an ci
amana. Malami (ko da na Akida ne ko na Tauhidi) ka san cewa idan ‘Dalibai su ka
dauki mummunar dabi’a daga gare, ka ci amana kuma sai ka biya a lahira. Jami’an
tsaro na Sojoji da ‘Yan Sanda da masu gadi ka da ku cin hanci a kowane matsayi
kake don kuwa ana biyan ka albashi. Duk motar da ta wuce, amana ce aka baka, kuma
Allah zai tambaye. Duk wanda ya bari aka shigo da wata barna a wata Jiha ko
Karamar Hukuma a Najeriya ya ci amanar kasa kuma ka ci amanar Allah. Ya kai mai
sakin masu laifi saboda dangantakar ka da su, ka sani cewa Allah ba ya
gyangyadi. Haka kuma idan ka sa wa wani laifi alhali bai yi ba, sai Allah ya
tambaye ka. Idan ka danne gaskiya a matsayin karya ka dauki gaskiya ka daura a
matsayin karya duk sai Allah ya tamabaye ka, ka duba Suratul Nisa’i. Ya ku ‘yan
jarida ku sani sai Allah zai tambaye ku, ka da ku rikita mana al’amarin kasa.
Lokaci da yarunta da karuciya da karfi duk amana ce da za ayi tambaya a kai. Ji
da gani da sauran gabobi duk amana ne. Ubangiji bai ba ka baki don ka rika
zagin Jama’a ba ko kuma sukar nagaba da kai don gobe kiyama kana kallo sai su
wuce Aljanna saboda alhakin da ka dauka, za ayi maka wasoso Ranar kiyama.
Ku sani cewa zamantakewa na
aure da gida duk amana ce tsakanin maigida da matar ka, da zarar kaci amana za
a kama ka. Manzon Allah yace a kiyayewa mata hakkin su. Ya ku masu cin amanar
mazajen su; masu yi wa maza sihiri don Ubangiji sai ya barke wannan layyar.
Annabi Muhammad SAW yace: ‘Ya ‘ya amana ne; wajibi ne yara su yi biyayya ga
iyaye kuma iyaye su biya hakkin yaran su na karantun zamani da boko. Ku duba
yadda kasar mu ta lalace kuma mutane ke nema a cigaba da zama a haka A fadawa
yara su zama cikin masu gaskiya, ka duba inda ‘dan ka ya ke kwana, ka san su
wanene abokan yaran ka don za a tsare ka a gobe kiyama. Annabi yace a gobe
kiyama sai wani ya zo wucewa sannan sai a ce a tsare sa don kuwa yana da sauran
tamabaya.
Zama da mu ke yi Majalisa na
dumama benci inda za ka ga Dattawa da su kayi ritaya ko aka yi masu su na zaune
har zuwa karfe 11:00 na dare kafin ya dawo cikin iyali, tun kafin ayi masa
ritaya yake haka. Allah yana cewa yana kawo maku mai gargadi watau furfura. Sai
ka ga Dattawa na Sallah a gidan karta kuma wai su ne manya a gari. Allah ya
kiyaye! Ubangiji yana kallon abin da su ke batawa na lokaci. Allah zai yi
tambaya game da iyalin ku; hijabin matar ka da kunyar ta da kuma raba ta da
miyagu duk amana ne. Sannan ki yi wa Mijin ki wa’azi game da zina (amma da yawa
na mata sun gwammace mazajen su su yi zina a maimakon yin kishiya). Allah ya
halarta aure (ba dole bane), idan mutum yana da hali, sai ya raya sunnar Manzon
Allah. Ba daidai bane ka ga Matar ka na mu’amala da mutane kuma ka kyale ta don
Annabi yace maras kishi ba zai shiga aljanna ba. Wannan ba shi ke nufin kuma mata
ba za tayi aiki ba don Allah yace idan za a fita ayi wanda Allah yake so.
Dukiyar da ke Baitul-Mali amanar Allah ce kuma duk wanda ya ci amana zai biya.
Wasu Barayin kasa na nan sun sace kudi sun gaza kai wa banki, su sani cewa
Allah yana nan sane. Wadanda su ka saci kudin Jama’a sun gaza barci amma ga wanda
bai ko sisi har da minshari. Hankalin barayin nan ba zai kwanta ba a Duniya har
lahira kuma kabari na jiran ku. Duk wanda yake ganin ya ci banza, bai ci banza
ba.
‘Yan uwa ku sani cewa a wannan
zamani idan ka na so ka nuna cewa ka ci gaba to kurum ka zama mai amana watau a
gani a kasa kamar yadda aka gani ga Sahaban Manzon Allah da wasu a yanzu. Kuma
don kana mai gaskiya ba za ka taba rasa Makiya ba, kuma ba wai wata Jam’iyya
bace ake shiga domin a zama mai gaskiya, ko wace Jam’iyya ana iya samun mai
gaskiya. Al-kur’ani da Sunnah ne za su gyara Najeriya ba wai Jam’iyya ba. Riko
da amana ne mabubbugar alheri kuma wannan ne zai sa a ci nasara. Duk wanda ya
rike amana, Allah zai sa a so shi. Babu kasar da za ta cigaba sai ta rike amana
kuma babu kasar da za ta wulakanta sai ta rabu da amana. Babu mu’umalar da za a
ci amana, face sai an ji kunya. Mu duba sunan da ake kiran Manzon mu tun kafin
Annabta. Haka kuma aka kira Annabi Musa da wasu Annabawan. Umaru dan Khattab
amintacce ne sannan ga Babba watau Abubakar Sadiq, Allah ya jikan Maza. Uthman
da sauran su har gobe masu amana ne.
Annabi yace za a dauke amana a
karshen zamani, tamkar Annabi na da rai a yanzu. Za ayi ta neman masu amana
amma sai ace a tafi wuri kaza. Sai ka ga mutum da kyakkyawar riga da gida da
mota amma ba amana, ka ga wani da mummunan yanayi amma bai da amana. A ina za a
samu amana? Maras lafiya ba lafiya, Likita ba lafiya, Malamar asibiti ba
lafiya, mai jinya ba lafiya, ina za a samu lafiya? Allah ya kiyaye! Mutum zai
yi barci sai a dauke amanar gidan sa; ta tafi wani wuri! Mutane za su yi ta
ciniki babu amana, kuma za a rika shugabantar da jama’a ba tare da amana ba.
Sai mu yi alfahari da wannan Annabi. Ko za kayi farin ciki a je lahira, sai
wannan Annabi yace: Juya, ba ka cikin mu! Annabi yace idan ka ga an wulakanta
amana, tashin kiyama ya zo. Mu duba wannan Magana ga rayuwar mu. Cin amana ya
shiga ko ina na lungu da sako. Allah ya kubutar da mu!
Sannan Huduba tay addu’a da salati
ga Annabi Muhammad SAW.
Muhammad Malumfashi yayi aikin
wannan huduba daga Masallacin I.T.N-Zaria.
Twitter:@Ya_waliyyi
No comments:
Post a Comment