Saturday, December 2, 2017

HUDUBA TA MURNAR HAIHUWAR ANNABI




MURNAR HAIHUWAR ANNABI MUHAMMAD S.A.W

 
Hudubar Jumu’a daga Masallacin I.T.N Zangon-Shanu, Zaria
Daga Bakin Sheikh S.S Abubakar


Dukkan godiya ta tabbata ga Allah da ni’imar fiyayyen halitta kuma ya sanya yin roko da shi. Muna godiya da yabo da tuba ga Allah da neman gafarar sa da neman tabbata cikin Sunnar Annabi Muhammad SAW. Muna shaidawa da gaskiya cewa lallai babu abin bauta da gaskiya face Allah mai girma, shi kadai yake bai da abokin Tarayya gare sa. Shi ne Masanin sirri da boye kuma mai tsinkaya game da niyyoyi na Bayin sa. Muna shaidawa cewa lallai Shugaban mu Annabi Muhammad SAW Masoyin mu mai girman dabi’a da daraja da halaye na kwarai ya kuma kubuta daga kaskanci, ya kuma isar da amana da sako tare da jihadi don daukaka Kalmar Allah da isar da fitilar haske ga Duniya. 

Bayan haka:
Allah Madaukaki a cikin Al-Qur’ani yayi gargadi da jin tsoron Allah tare da cewa ka da a mutu face ana Musulmai. Bayin Allah, Allah shi ya zartar da hukunci na cewa zai canza abin da yake doron kasa tare da tarihin Dan Adam a lokacin da Allah ya haskaka Duniya duka da hasken shiriya ta Annabi SAW. Wannan haske ya shiga cikin sasannin Duniya duk inda ‘Dan Adam yake. Allah ya bayyanar da wani Alfijir na wani sabon zamani. Duk wasu hankula da aka yi wa takunkumi da dabaibayi na jahilci da al’ada da camfe-camfe sai da Manzon Allah ya zo da almakashi domin su samu ‘yanci. Annabi kuma ya tserar da ‘Yan Adam daga halin da su ke ciki na jahilci. An haife shi a Litinin a Ranar 12 ga Watan Rabi’ul Auwal irin ta yau bisa magana ta mafi rinjayen Malamai. 

Allah yayi mana wata matashiya a cikin Al-Kur’ani inda yace: Hakika Allah yayi wata baiwa ga Muminai da ya aiko wani Manzo mai daraja daga cikin su wanda yake koya masu ayoyin Allah tare da tsarkake su da kuma karantar da su littafi da hikima (Hadisin sa) wanda kafin nan, su na cikin bata mabayyani. Lallai, duk wadanda su ke ma’abota imani na gaskiya su na samo shiriyar su ne daga al’amarin Manzon Allah. Kuma abubuwa ba za su daidaita ba, har sai al’amuran Musulmai sun kasance a kan haka. Bisa ga shiriyar Annabi ne ya kamata duk wani Musulmi ya shiryu kuma bisa hasken sunnar sa ne ya kamata duk wani Musulmi ya rika tafiya. Idan har ba ka da fitilar da za ta haska maka hanyar ka, sai ka tambaya a haska maka. Mabubbugar mare-mari na Annabtar sa ne wurin shan duk Musulmi har ya koshi a ko yaushe. A karkashin tutar Shugaban mu Annabi SAW ya kamata a rika yin duk wata gwagwarmaya. 

Saboda haka, haihuwar sa, ta zama tamkar wata sanarwa ce ta bayyanar Alfijir na tabbatar gaskiya a doron kasa don saboda ba za a gushe ba a ban kasa sai an samu wasu Bayin Allah masu son su taimaki tafarkin Allah da kuma Manzon sa, komai yadda abubuwa su ka lalace su na tinkarar barna yayin da su ka tsimu da shirya ta Annabi, ko da ma’abota barna sun fi su a yawa, kuma komai girman mabarnata ba za a rasa wadannan Bayin Allah da za su yi wannan aiki a ban kasa ba har tashin kiyama. Kuma duk wulakancin da za ayi, irin wadannan mutane ba za su dukawa wani mabarnaci ba, amma idan aka je lahira kuwa, babu wanda zai daga kan sa irin su, yayin da mabarnata su ke cikin kunya da kaskanci. 

Shi Manzon Allah shi ne abin koyi da misali ga duk Duniya baki daya duk da banbancin matsayin su. Duk wanda Allah ya dankawa mulki a hannu yayin da yake musulmi, to zai samu abin misali daga Annabi na tabbatar da daula ta adalci da siyasa ta talakawa. Don haka duk wanda ya samu shugabanci, ya nemi a fada masa yadda Annabi ya tafiyar da siyasar al’umma. Wani Mawaki yace: Manzon Allah yana sassautawa a inda ya dace tare kuma da yin sanyi a lokacin da ya dace. Haka kuma duk wanda yake Malami ko mai kira ga Allah zai samu abin koyi a al’amarin Manzon Allah wajen sadaukarwa da isar da sako cikin hikima tare da hakuri da juriya na daukar duk wata cutarwa da zargi na mai cutarwa da mai zargi, tare da yin koyi da saukakawa da tausasawa na Manzon Allah. Su ma masu arziki da wadata su koma tarihin Manzon Allah domin jin irin dabi’ar sa ta ciyarwa da kyauta cikin tafarkin Allah. Wadanda su ka ce za su yi jihadi sai su duba yadda yayi gwagwarmaya ya canza tarihin Duniya cikin shekaru 23, wanda har kasa ta nade Duniya ta canza a dalilin sa. Haka kuma Samari da ‘Yan mata duk su na da rawar takawa da gudumuwa a kan wannan tsari na Annabi. Duk wani mai gida da ‘yan cikin gida kuma ya kamata su tambayi yadda Annabi ya zauna da Iyalan sa domin kuwa wajen sa kadai za a samu wannan shirya. Wannan shi ne kamannin zababbe cikin Bayin Allah wanda aka daukaka al’amarin sa aka fifita sa cikin ta’alikai ya zama babu kamar sa. Allah ya sanya kaskanci da wulakanci ga wanda ya saba masa har zuwa tashin kiyama. 

Ya ku ‘Yan uwa ku sani cewa girmama shi (Annabi SAW) da darajanta shi yana cikin ayyukan ibada. Sai dai mu sani cewa mu soyayyar mu da Manzon Allah wanda ba mu da kamar sa, ba dangantaka ce da za ayi ta wani biki ko ayi ta ambaton mu’ujizozin sa ba kurum. Mu irin dangantakar mu kakkarfa ce wanda ta ke a dukkan lokaci da halin da za mu samu kan mu har mutuwar mu. Allah yace a cikin Manzon Allah akwai abin koyi kyakkyawa ga duk wanda yake neman ya samu rahama kuma yake so ya rabota. Allah yana cewa da Annabi SAW: Idan har ku na son Allah, to ku bi ni!

Allah ya gafarta mana ya kuma bamu ikon fahimtar AlKurani mai Girma da aiki da shi. 



Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga Zaria
Twitter: @Ya_waliyyi

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...