Tuesday, December 26, 2017

Download all WhatsApp status in few seconds



HOW TO DOWNLOAD WHAT’SAPP STATUS WITHOUT USING ANY APPLICATION


You don’t have to use any 3rd party to download all WhatsApp Status. They are right there in your phone. This method will even help you freeze your memory from unwanted data. My brother taught me this:

Now how do you do it?

I.                   Locate your WhatsApp storage folder (Most phones now use Internal memory).
II.                In your File Manager, turn on the ‘Show hidden files’ so all files appear visible.
III.             In the WhatsApp folder, go to the ‘Media’ folder then choose ‘.Statuses’
IV.             The sub folder ‘Statuses’ is hidden, so you have to make sure you follow Step II.
V.                Go to the folder, you have all viewed status; pictures, gifs, videos, etc. there.
VI.             Cut or move these files from the .Statuses folder to a desired location in your storage disc.
VII.          Go to your Gallery and you will find all the downloaded Status saved in a new folder.

You have to do this on time and frequently because the files may be temporary and this may help you clear your disc from accommodating your space unnecessary. 


Now don’t ask me to send any video again! It consumes too much data!

Follow me on Twitter: @Ya_waliyyi

Sunday, December 17, 2017

Chipping into the discourse on Islamic banking


Unraveling the mystery behind Islamic banking by Ahmad Mati




It is no more a new concept or news highlight, the practice of Islamic banking and finance. With the emergence of Jaiz Bank (though after a rumble raw) and later some Islamic insurance companies (takaful Insurance) it was currently augmented with the issuance of Islamic Bonds (Sukuk), for some people the word “Islamic” which keep appearing is not a welcome thought. The word Non-Interest might appear appealing and comforting. All things being equal, the understanding of the general principles supersede the long debated acronym of both.

The idea of equity in economy, social justice, equal opportunity for all should be the parameters which our collective thought and understanding should be channeled towards. Depending on the name you call it restructuring, true federalism, also depending on your understanding of the concept whether it means control of resources by state, regions, lopsided government appointment or even going back to the old system of regional government. Tentatively all boils down to the feeling of social justice, equal opportunity for all, equity in wealth distribution. Plethora's of debate and writings have continued to spur out from different angles, disciplines depending on the interest it want to protect. 

The poor man that finds it difficult to get two square meal a day, or the one who can’t afford taking his children to the expensive private schools, or those ones that only experience eating meat during Salah festival or Christmas celebration, majorly by the mercy of their neighbors or identified rich men in their community. Invariably that kind of person does not care about the concept you call it or the acronym you gave it. During the world saving day (Tuesday, 31 October), the International Institute for Islamic Banking and Finance Bayero University Kano organized a public lecture on Cooperative  in our societies majorly Kano, with the key speakers from both private sector and the academia, the audience where all enticed and moved with the wonderful and miraculous opportunities our communities stand to get if effectively applied and managed, I was thrilled and made to understand how if effectively managed, we can solve numerous of our countless problems as a society and a nation with sustainability and accountability. It was said Kano has more than 5 big major market, one of the speaker from the private sector made a rough analysis of how cooperative can strive in this market with little contribution ranging from one hundred Naira to one thousand naira daily, we were all in shock imagining the figures we saw which runs in billions monthly and how that can transform our people and our cities. As usual with Nigerian gatherings, everybody was apportioning blames to various quotas, but it was clear government need to put down the required laws and regulations in place, the government must be more visionary and pragmatic. We all left with the conclusion that as citizens we need to organize ourselves and be part of the solution rather than lamentation.

Looking at some of our compounding problems, ranging from economic and social, there must be a set framework or philosophy which as a country and people must be committed to achieving. The interesting reality is how countries like Singapore, Malaysia, Bangladesh and Europe in general are carefully utilizing some of this concept and principles which Islamic economics propagate. For example “Foundations” which are practiced in Europe and Waqf (Hubs) which was active in Islamic history, it also interest me how Europe understand complimenting the private and public sector through the voluntary sector in a way of NGOs and Foundations which is equivalent to Zakat, Waqf and Sadaqah Institutions in Islamic framework.

It is pertinent for our people to have the right mind-set and attitude which consequently translate to economic development and prosperity. It is high time we acknowledge the flows that come with capitalism, as the popular saying goes “the rich get richer and the poor get poorer”. As community we must not encourage laziness and exploitation at the same time we must reward hardworking and honesty. Economic benefit should come from putting effort in adding value rather than manipulating or outsmarting the system. Well I am still going back to my acronym “Islamic economics” has a unique and sustainable solutions to many of our compounding problems, therefore looking at the concept (subject matter) from the application point of view will make us appreciate, and consequently spark real development with minimal fluctuations of Booms and recessions, of Inflation, stagflation and deflation.
“The reform of an economy must first and foremost begin with the analysis and understanding of...its people. This is because it is only the people that can reform an economy. An economy per se cannot reform the people...” Prof. Aluko


Ahmad Mati is a graduate student of Islamic banking & finance

Saturday, December 16, 2017

Hudubar Juma’a daga Mimbarin ITN-Zaria



‘Riko da Amana’-Daga Bakin Imam Ustaz Dr. Sa’eed Yunus

Assalamu Alaikum wa Rahmatul Lah, 

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah SWT wanda yayi umarni da a rike amana. Ubangiji yayi mana hani da yaudara da ha’inci. Allah yayi alkawarin azaba ga wadanda su ka ci amana. Allah yana son Bayi masu rikon amana. Mu na shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah. Ina shaida cewa lallai Annabi Muhammadu, Bawa ne kuma Manzom Allah. Annabi ya kwadaitar da Mutane game da amana ya kubutar da su game da rashin amana. Aminci su tabbata ga Annabi Muhammadu da wadanda su ka bi tafarkin sa. Bayan haka:

Ku sani cewa mafi alherin aiki shi ne littafin Allah da shiriyar Annabi SAW sannan kuma mafi sharrin al’amari shi ne wanda aka kirkira. Duk abin da aka kirkira a cikin addini bidi’a, ne kuma bidi’a bata ne, kuma bata na wuta. Allah ya kare mu daga wuta. Ya ‘yanuwa Allah yayi umarni a cikin ayoyi masu yawa a Al-kur’ani a karshen Suratul Baqarah da kuma Suratul Nisa’i bayan nan kuma Allah yayi magana a cikin Suratul Anfali da har Suratul Ma’arij. 

‘Yan uwa Al-Kur’ani yayi magana game da wannan abu mai girma, ya kuma mutane su ke wasa da wannan abu da Allah ya girmama shi. A cikin Suratul Ahzabi, Ubangiji ya fada mana cewa Sammai da Kassai da Duwatsu sun gaza rike amanar da Allah ya bijira masu inda su ka ce ba za su iya ba. Ku duba girma da nauyi da kuma karfin dutse amma ‘Dan Adam yace ya ji zai iya rike wannan amana ta Allah. Ubangiji ya tambayi kowace sama da kasa duk su ka ce ba za su iya ba. Shi kuwa ‘Dan Adam ya karba. Annabi Muhammad a wani hadisi yana cewa ‘Ka bada amana ga wanda ya amince maka’ Ya tabbata cikin sunnar Annabi cewa; ha’inci yana cikin halin Munafukai. Akwai hadisi daga Anas Dan Malik da yake cewa Annabin Rahama SAW ba ya huduba face sai yayi magana game da amana. Annabi ya kan ce: ‘Babu Imani ga wanda bai da amana, sannan kuma babu addini ga wanda ba ya cika alkwari’.
‘Yan uwa ku dube mu ku gani don Annabi yace maras amana bai da Imani, sai kowa ya dauki kan sa; ko a wace Ma’aikata yake aiki.Yanzu mu na zamani a wani lokaci da ake kiran ‘Corruption’ yayi yawa. Zalunci yayi yawa har ta kai ana cewa wanda ya hana zalunci shi ne azzalumi. Inalillahi wa inna ilaihi raji’un! Matsayin amana matsayi ne mai girma ‘Yan uwa. Amana kamar yadda Malamai su kayi I’tifaki shi ne abin da Allah ya daurawa Bawa kuma wanda ya tsayu da hakan ya bada amana. Allah yace kayi sallah da azumi, ko kayi sallar? Ka yi azumi kamar yadda Annabi ya koyar? Don Annabi ya bayyana yadda ake wadannan ibadu saboda haka hakika duk wanda ya ki yin hakan ya cuci kan sa. 

Ya ku ‘Yan uwa na addini, daga cikin amanar da Allah yake so a rike shi ne kadaita Allah babu shirka da guru da laya da hake-hake da shan jini watau amanar Tauhidi. Kuma idan za kayi abu kayi don Allah, ban da riya. Abu na biyu kuma shi ne rike Sunnar Annabi Muhammad sawu da kafa (ba da baki ba) watau a gani-a kasa. Duk wanda ka ke so kayi biyayya a gare sa kuma ba biyayya ta shirme ko kirkirar abubuwa ba. Idan ka na son Manzon Allah sai a gani a kasa wajen tsayawa bin sa tsayin daka. Wani Sahabi ya zo da sandar sa, ya tsaya wajen wata bishiya yace shi ma sai yayi irin yadda Annabi SAW yake yi da sandar sa a lokacin yana da rai. Wannan ita ce madarar soyayya ta Manzon Allah, ba rawa ba, kuma ba kida ko raye-raye ba, ko mata su fito su na shirme ba! ‘Yan uwa ku sani cewa bidi’a bata ce kuma ha’inci ne ga Annabi Muhammad. Duk wani ‘Dan bidi’a sai ya kawo lasisin aikata abin da ya aikata a Ranar lahira. Malamai su na cewa duk wanda yayi wata bidi’a yana tuhumar cewa Annabi bai isar da wani sako bane, kuma ta tabbata Annabi ya kammala cikar da sakon Musulunci. Duk wanda yake bidi’a sai ya shirya abin da zai fadawa Allah a gobe kiyama. 

Abu na gaba shi ne hukunci da shari’ar Allah, idan aka samu inda ake hukunci da shari’ar da ba ta Allah ba, to sai ka ki ta. Yanzu mu na lokacin da ake da wasu da ake kira ‘Lawmakers’ wadanda ke tsara dokokin kasa. Wadannan mutane da Alkalai da ake da su Musulmai ne har yanzu kuma ka da wanda ya kafirta su gaba daya. Sai dai ya kamata su ji cewa hukuncin Allah shi ne hukunci. Allah yana cewa: Hukuncin jahiliyya su ke so? Su wa su ka fi masu bin hukuncin Allah ne? Me bin hukunci na Allah shi ne mafi biyayya ga hukunci mai kyau. ‘Dan uwa idan har ka samu kan ka a cikin Majalisa ku na cikin masu tsara dokokin kasa, to ka sani cewa hukuncin Allah ya fi. Amma abin bakin ciki, sai ka ga Musulmi ya tafi Kotun Musulunci an yi masa shari’a da littafin Allah amma ya tafi yana kiyayya yana zage-zage.
Duk abin da na fada ya shafi bangare ne na akida, yanzu zan yi magana ne a kan ibada. Ibada gaba dayan ta amana ce a wuyar Musulmi namiji da mace. Sallah da alwala da wanka da zakkah da aikin Hajji duk amanar Allah ce. Dole a aikata yadda Ananabi ya koyar, Annabi yace ku koyi aikin hajjin ku daga gare ni. Idan ka saki wannan abubuwa to ka sani cewa ka ci amanar Allah.
Yanzu an samu shugabanci na gaskiya a Kasa sai kuma abin mamaki wasu ‘yan uwan mu su na kiyayya ga wannan tafiyar ko kuma wadanda aka jawo su kusa su na ta ha’inci ga Allah da kuma shugaba da al’umma, sai dai ku sani cewa kun ha’inci kan ku ne don kuwa Ubangijin ka yana nan a madakata. Zumunci, hakuri, ‘yanuwantaka da sauran su duk amana ne, haka nan kuma duk abin da ya shafi karya da ha’inci da wauta da girman kai da zina da barayi (na biro da na dare da sauran su) duk su na cikin cin amanar Allah kuma lokaci kurum Ubangiji ya ke jira. Allah ya shiryar da mu! Daga cikin abubuwan da Allah ya nemi mu kiyaye Jama’a, mu san cewa akwai kiyayar baki daga ‘giba’ watau gulma, rada da annamimanci. Sannan mu kiyayi karya da hassada da kulli a cikin zuciya. Allah ya shirya mu ya sa mu cikin Bayi nagari. 

Bayan haka:
Huduba ta biyu tana godewa Allah, da kuma yabo ga farin jakadar Allah, tana cewa mu ji tsoron Allah wajen amanar mu. Allah zai tambaye mu game da amanar da ya ba mu; za a tambayi kowa game da gidan sa (ka daina kallon shugabanni kurum) Hadisi na ‘Dan Umar RA wanda ya ke cikin Bukhari da Muslim cewa kowanen mu abin tambaya ne. Mu sani cewa ilmin da ake koyo a a zaure da Boko da Islamiyya duk amana ne. Malamai masu karantarwa ku fadawa Jama’a gaskiya haka kuma Dalibai ku rike amana. Ka da a samu shaidar zir (na ba kayi karatu ba sai ace kayi) kamar yadda ake samu a yau daga sama har kasa. Iyaye da yara su na satar jarabbawa, lallai an ci amana. Malami (ko da na Akida ne ko na Tauhidi) ka san cewa idan ‘Dalibai su ka dauki mummunar dabi’a daga gare, ka ci amana kuma sai ka biya a lahira. Jami’an tsaro na Sojoji da ‘Yan Sanda da masu gadi ka da ku cin hanci a kowane matsayi kake don kuwa ana biyan ka albashi. Duk motar da ta wuce, amana ce aka baka, kuma Allah zai tambaye. Duk wanda ya bari aka shigo da wata barna a wata Jiha ko Karamar Hukuma a Najeriya ya ci amanar kasa kuma ka ci amanar Allah. Ya kai mai sakin masu laifi saboda dangantakar ka da su, ka sani cewa Allah ba ya gyangyadi. Haka kuma idan ka sa wa wani laifi alhali bai yi ba, sai Allah ya tambaye ka. Idan ka danne gaskiya a matsayin karya ka dauki gaskiya ka daura a matsayin karya duk sai Allah ya tamabaye ka, ka duba Suratul Nisa’i. Ya ku ‘yan jarida ku sani sai Allah zai tambaye ku, ka da ku rikita mana al’amarin kasa. Lokaci da yarunta da karuciya da karfi duk amana ce da za ayi tambaya a kai. Ji da gani da sauran gabobi duk amana ne. Ubangiji bai ba ka baki don ka rika zagin Jama’a ba ko kuma sukar nagaba da kai don gobe kiyama kana kallo sai su wuce Aljanna saboda alhakin da ka dauka, za ayi maka wasoso Ranar kiyama. 

Ku sani cewa zamantakewa na aure da gida duk amana ce tsakanin maigida da matar ka, da zarar kaci amana za a kama ka. Manzon Allah yace a kiyayewa mata hakkin su. Ya ku masu cin amanar mazajen su; masu yi wa maza sihiri don Ubangiji sai ya barke wannan layyar. Annabi Muhammad SAW yace: ‘Ya ‘ya amana ne; wajibi ne yara su yi biyayya ga iyaye kuma iyaye su biya hakkin yaran su na karantun zamani da boko. Ku duba yadda kasar mu ta lalace kuma mutane ke nema a cigaba da zama a haka A fadawa yara su zama cikin masu gaskiya, ka duba inda ‘dan ka ya ke kwana, ka san su wanene abokan yaran ka don za a tsare ka a gobe kiyama. Annabi yace a gobe kiyama sai wani ya zo wucewa sannan sai a ce a tsare sa don kuwa yana da sauran tamabaya. 

Zama da mu ke yi Majalisa na dumama benci inda za ka ga Dattawa da su kayi ritaya ko aka yi masu su na zaune har zuwa karfe 11:00 na dare kafin ya dawo cikin iyali, tun kafin ayi masa ritaya yake haka. Allah yana cewa yana kawo maku mai gargadi watau furfura. Sai ka ga Dattawa na Sallah a gidan karta kuma wai su ne manya a gari. Allah ya kiyaye! Ubangiji yana kallon abin da su ke batawa na lokaci. Allah zai yi tambaya game da iyalin ku; hijabin matar ka da kunyar ta da kuma raba ta da miyagu duk amana ne. Sannan ki yi wa Mijin ki wa’azi game da zina (amma da yawa na mata sun gwammace mazajen su su yi zina a maimakon yin kishiya). Allah ya halarta aure (ba dole bane), idan mutum yana da hali, sai ya raya sunnar Manzon Allah. Ba daidai bane ka ga Matar ka na mu’amala da mutane kuma ka kyale ta don Annabi yace maras kishi ba zai shiga aljanna ba. Wannan ba shi ke nufin kuma mata ba za tayi aiki ba don Allah yace idan za a fita ayi wanda Allah yake so. Dukiyar da ke Baitul-Mali amanar Allah ce kuma duk wanda ya ci amana zai biya. Wasu Barayin kasa na nan sun sace kudi sun gaza kai wa banki, su sani cewa Allah yana nan sane. Wadanda su ka saci kudin Jama’a sun gaza barci amma ga wanda bai ko sisi har da minshari. Hankalin barayin nan ba zai kwanta ba a Duniya har lahira kuma kabari na jiran ku. Duk wanda yake ganin ya ci banza, bai ci banza ba.

‘Yan uwa ku sani cewa a wannan zamani idan ka na so ka nuna cewa ka ci gaba to kurum ka zama mai amana watau a gani a kasa kamar yadda aka gani ga Sahaban Manzon Allah da wasu a yanzu. Kuma don kana mai gaskiya ba za ka taba rasa Makiya ba, kuma ba wai wata Jam’iyya bace ake shiga domin a zama mai gaskiya, ko wace Jam’iyya ana iya samun mai gaskiya. Al-kur’ani da Sunnah ne za su gyara Najeriya ba wai Jam’iyya ba. Riko da amana ne mabubbugar alheri kuma wannan ne zai sa a ci nasara. Duk wanda ya rike amana, Allah zai sa a so shi. Babu kasar da za ta cigaba sai ta rike amana kuma babu kasar da za ta wulakanta sai ta rabu da amana. Babu mu’umalar da za a ci amana, face sai an ji kunya. Mu duba sunan da ake kiran Manzon mu tun kafin Annabta. Haka kuma aka kira Annabi Musa da wasu Annabawan. Umaru dan Khattab amintacce ne sannan ga Babba watau Abubakar Sadiq, Allah ya jikan Maza. Uthman da sauran su har gobe masu amana ne.

Annabi yace za a dauke amana a karshen zamani, tamkar Annabi na da rai a yanzu. Za ayi ta neman masu amana amma sai ace a tafi wuri kaza. Sai ka ga mutum da kyakkyawar riga da gida da mota amma ba amana, ka ga wani da mummunan yanayi amma bai da amana. A ina za a samu amana? Maras lafiya ba lafiya, Likita ba lafiya, Malamar asibiti ba lafiya, mai jinya ba lafiya, ina za a samu lafiya? Allah ya kiyaye! Mutum zai yi barci sai a dauke amanar gidan sa; ta tafi wani wuri! Mutane za su yi ta ciniki babu amana, kuma za a rika shugabantar da jama’a ba tare da amana ba. Sai mu yi alfahari da wannan Annabi. Ko za kayi farin ciki a je lahira, sai wannan Annabi yace: Juya, ba ka cikin mu! Annabi yace idan ka ga an wulakanta amana, tashin kiyama ya zo. Mu duba wannan Magana ga rayuwar mu. Cin amana ya shiga ko ina na lungu da sako. Allah ya kubutar da mu!
Sannan Huduba tay addu’a da salati ga Annabi Muhammad SAW.



Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga Masallacin I.T.N-Zaria.
Muhammadmalumfashi@gmail.com          
Twitter:@Ya_waliyyi

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...