Thursday, July 13, 2017

Har yanzu haihuwa na ke nema Inji mai yara 100


In so samu ne: In kara samun yara Inji mai 'Ya 'ya 100 



  • Wani mutumi 'Dan kasar Ghana ya haifi 'ya 'ya fiye da 100
  • Amma fa yace so samu ya kara samun wasu ‘ya ‘yan
  • Wannan ta’aliki yana da mata har 12 a halin yanzu




Gidan BBC tayi hira da wani mutumi 'Dan kasar Ghana da ya haifi 'ya 'ya fiye da 100 a Duniya kuma yace har yanzu bai gaji da samun yaran ba.

Kwanan nan aka yi bikin al'umma ta Duniya inda wannan mutumi mai suna Kofi Asilenu a wani Kauye cikin Kasar Ghana mai 'ya 'ya 100 da mata 12 yace shi fa har gobe in zai samu karin 'ya 'ya yana so.

Wannan mutumi yace bai da kowa a Duniya na Danuwa don haka ya dage wajen tara 'diya. Asilenu yace duk da shekarun sa 80 amma har yanzu da karfin sa don haka so ma yake ‘ya ‘yan na sa su wuce haka.


[NAIJ Hausa]

Wednesday, July 12, 2017

Osinbajo ya bayyana yadda su kayi da Buhari a Landan


Shugaba Buhari na murmurewa kwarai da gaske Inji Osinbajo



  • Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana yadda su kayi da Shugaban Kasa Buhari
  • Shugaban kasar na murmurewa kwarai da gaske Inji Farfesa Yemi Osinbajo
  • Sai dai Mukaddashin Shugaban kasar bai bayyana lokacin da Buhari zai dawo ba




Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana yadda su kayi da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Landan inda su ka hadu a jiya Talata.

Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyanawa ‘Yan jarida a fadar shugaban kasar cewa Shugaban kasar na murmurewa matuka. Haka kuma yace sun tattauna game da batun da su ka shafi kasar gaba daya kafin ya dawo daga Landan dazu.

Sai dai Mukaddashin Shugaban kasar bai bayyana takamamen lokacin da Shugaba Muhmmadu Buhari zai dawo ba yayin da aka tambaye sa. Osinabajo dai yace Shugaban kasar na cikin annurin gaske kuma ya kusa dawowa.


Wani Saurayi Musulmi ya auri 'Dan uwan sa


Duniya ina za ki da mu: Wasu Musulmai maza sun yi aure tsakanin su


  • Yanzu dai Duniya ta kai har an auren jinsi da jinsi
  • Wasu Musulmai ne dai su ka auri junan su a Kasar Birtaniya
  • Su ka ce za su nuna wa Duniya cewa Musulmai ma sun bi sahu

 



Abin da ba a gani ko ji a Kasar Ingila ba ga faru don kuwa wasu Musulmai maza ne su ka auri junan su hankali kwance a wata Unguwa da me Kasar Ingilar.

Jahed Choudhury ya auri Sean Rogan wanda wannan ne karo na farko a Garin da Musulmi namiji zai auri Dan Uwan sa Musulmi. Wannan ba wai bane don kuwa ta tabbata cewa wadannan mutane sun yi bikin auren gargajiya.

Jama'a dai da dama sun halarci wannan biki na saurayi Chodhury Dan asalin Kasar Bangladesh. Wannan saurayi dai an kore sa da dangin sa kuma an hana sa shiga Masallaci sai sai haduwar sa da Rogan bayan ya dawo daga aikin Hajj ta sa rayuwar sa ta canza.

Tuesday, July 11, 2017

A Kasar India kasar gini na nema ta fi gwal daraja


Kasa ta zama kayan gabas a Kasar India


  • Kasa fa yanzu a Kasar India na nema ta zama abin da ta zama
  • A Kasar India yanzu neman kasar gini ake yi ido rufe
  • Ana ma maganar kasa na nema ta fi gwal daraja a wannan wuri


Harkar gine-gine kamar yadda mu ka samu labari daga Al Jazeera ya sa kasa ta zama abin da ta zama a Kasar India da ke da dinibin mutane har sama da Biliyan guda.

Sai dai kasar gini yanzu na mugun wahala a India wanda ta so dole aka shiga neman kasar ta hanyoyin da ba su dace ba. Wasu ma dai sun gano hakan kuma sun maida wannan kazamar harkar sana'ar su.

Yanzu haka a India an koma satar kasa daga bakin rafi ko kuma inda jama'a ke shakatawa na gefen tafku. Ya zama dole dai ayi amfani da kasa wajen gini wanda shi ya zama dole domin muhalli amma kasar sai su wane da wane yanzu.



[NAIJ Hausa]

An yi wayar salular da babu ruwan ta da batiri


Sabon salo: Masana sun yi wayar da ke aiki da haske



  • Masana sun yi wayar da ke aiki da haske ba ruwan ta da batir
  • Idan kana da wannan waya ba ruwan ka da cajin batiri a wuta
  • Ana sa rai cigaban ba kuma ya dara haka nan gaba


Masana sun kirkiro wayar da ba ta aiki da batiri sam abin ta. In dai a irin su Najeriya ne da lantarki ya zama kayan gabas ai an more kuwa.

Ko da yake a ko ina ma dai ana kuka wajen yanayin aiki da batiri don haka ne aka kirkiro wannan waya da ke amfani da haske wajen aiki da kuma karfin sigina wanda ita ce ta farko da aka taba yi a Duniya wanda ko kadan ba ta aiki da batiri.




Shugaban wadanda su ka yi wannan nazari da aiki Farfesa Shyam Gollokota da ke Jami'ar Washington na kasar Amurka yace sun yi tunani ne su ka ga ya dace ayi wani abu game da wannan batu. Nan gaba da na dai za a kirkiro salular da ke aiki da iska ba mamaki!




[NAIJ Hausa]

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...