Friday, April 14, 2017

Tunawa da Sheikh Ja’afar Mahmud Adam


 
– A rana irin ta yau aka kashe Malam Ja’afar Mahmud Adam


– Wasu suka kashe babban Malamin yana tsakiyar sallar asuba


– Sheikh Ja’afar yana cikin manyan Malaman da aka yi a Arewa



Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam
A dalilin tunawa da Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam Daura da aka kashe shekaru 10 da suka wuce nayi wannan rubutu. An dai kashe Malam Ja’afar yayin da yake jagorantar sallar asuba a masallacin da yake Limanci.

Har yau dai ba a kama wadanda ke da hannu wajen kashe babban Malamin ba wanda ya ba addini rayuwar sa. An dai haifi Malam Ja’afar a Garin Daura a gidan Malamai, nan ya fara karatun addini daga nan ya koma Kasar Kano inda yayi almajiranci.

Daga nan ya kara karatun addini da boko a Garin Kano har ya samu nasara a gasar karatun Al-kur’ani. Daga nan Malamin ya samu wucewa Kasar Saudiyya inda ya Digiri a fannin Ilmin Al-Kur’ani a Jami’ar Madina.


Bayan ya kammala kuma ya zarce Kasar Sudan inda ya samu Digiri na biyu a fannin yaren larabci. A lokacin da aka kashe Sheikh Jafar yana digirin sa na uku a fannin addini Musulunci a Jami’ar Danfodiyo ta Sokoto.

Marigayi Ja’afar yana cikin malaman da suka kware wajen tafsirin Al-kur’ani da kuma iya bayani dalla-dalla ga Jama’a bisa koyarwar Sunnah ta Manzon tsira SAW. Malam Jafar ya koyar da al'umma ilmi da dama na Tauhidi da Hadisi da Sira da Fikihu na tsawon lokaci a fadin kasar nan. 

Allah ya jikan Malam Jafar Adam da Albani-Zaria ya karbi shahadar su. Ameen.



Muhammad Malumfashi ya rubuta wannan a shafin NAIJ Hausa jiya




Thursday, April 13, 2017

Real Madrid da Ronaldo sun kafa tarihi



Real Madrid ta ba Bayern Munich kashi


– An tashi wasa da ci 1-2 a filin Arianz Arena


– Dan wasa Ronaldo ya zuba kwallaye 2 a raga




Kungiyar Real Madrid ta doke Bayern Munich da ci 1-2 a gasar UEFA Champions league na zakarun Nahiyar Turai. Real Madrid dai ba ta saba samun galaba a kasar Jamus ba a gasar.

Dan wasa Cristiano Ronaldo ya jefa kwallaye 2 bayan Bayern Munich sun fara zurawa Real Madrid din kwallo guda. Ronaldo dai  ya kafa tarihi inda ya zama duk Duniya babu mai yawan kwallayen sa a Gasar.

Yanzu Ronaldo yana da kwallaye 100 a Gasar UEFA yayin da Real Madrid tayi wasanni 53 kullum sai ta jefa kwallo a ragar takwarorin ta. Yanzu dai Real Madrid ta gamu da Bayern a gidan ta a wani makon.



[NAIJ Hausa]

Wednesday, April 12, 2017

Kungiyar Juventus ta lallasa Barcelona



Champions league: Barcelona ta sha mugun kashi hannun Juventus har gida



Juventus ta biyo Barcelona har gida ta ba ta kashi


– An zurawa Barcelona kwallaye 3 da nema


– Dan wasa Dybala yayi tashe a wasan




Kungiyar Juventus ta ba Barcelona dan-karen kashi a gasar UEFA Champions league na zakarun turai da aka buga jiya. Juventus ta biyo Barcelona ne har gida kasar Spain ta zuba mata kwallaye 3 a raga.

Barcelona dai ta gagara maida ko kwalla guda duk da irin tabuka abin kirkin da tayi a wasan. Dan wasa Dybala ne dai ya zura kwallaye 2 tun kafin wasan yayi nisa, daga baya kuma dan baya Chiellini ya kara ta 3.

Wancan makon ne dai Kungiyar Malaga ta doke Barcelona a wasan La-liga da ci har 2-0. Wannan makon kuma Barcelona za ta kara da Real Madrid kuma dan wasan gaban nan Neymar Jr. ba zai samu buga wasan na El-Clasico ba. 




Hakanan wasu bam har 3 sun tashi a gefen titi a kasar Jamus. Wannan abin tashin hankali ya faru ne a lokacin da ‘Yan kungiyar Borrusia Dortmund na kasar ke shirin buga wasan su na zakarun Turai. Dan wasa Bartar ya samu rauni an kuma daga wasan. 

An jima ne dai Real Madrid za ta gwabza da Bayern Munich. Madrid ta kasar Spain na shan wahala a Kasar Jamus tun fil-azal. 





[NAIJ Hausa]

Tuesday, April 11, 2017

An kama masu bara fiye da 400 a Kano



Gwamnatin Jihar Kano ta damke mabarata da dama


– Gwamnatin Jihar Kano ta kama masu bara fiye da 400 a Jihar


– Hukumar Hisbah ce dai tayi wannan aiki a fadin Jihar


– Dama Sarki Muhammadu Sanusi II yace Arewacin Najeriya sun fi ko ina talauci



Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama masu bara da roko a Jihar Kano da dama cikin watan jiya da shekaran jiya kamar yadda mu ke samun labari yanzu haka. An dai kafa dokar da ta haramta bara a cikin Garin Kano.

Shugaban Hukumar Hisbah Malam Musa Tsangaya ya bayyanawa manema labarai wannan  kwanan nan. Tsangaya yace an kama masu bara a cikin Jihar wanda ya saba doka. Cikin dai wanda aka kama akwai manyan mutane kusan 200 yayin da sauran kuma dai kananan yara ne.

Mafi yawan wadanda aka kama dai ‘Yan asalin Jihar Kano ne yayin da sauran kuma su ka fito daga Jihohin Kaduna da Jigawa masu makwabtaka da Kano. Cikin wadanda aka kama dai har da maras hankali.

Kwanan nan Sarkin Kano ya bayyana cewa Arewacin Najeriya sun fi ko ina talauci a wani taro da aka yi a Kaduna. Akwai Almajirai sama da miliyan 3 a Jihar Kano kurum.





[NAIJ Hausa]

Sunday, April 9, 2017

Yadda Dino Melaye ya karbi Satifiket din sa


Karshen tika-tika; tika; Dino ya karbi Satifiket din sa a A.B.U 


– A Ranar Juma’a Dino Melaye ya karbi takardar shaidar karatun sa a Makarantar sa


– An hurowa Sanatan wuta cewa bai kammala Jami’ar ba


– Sai dai shugaban Jami’ar ya wanke Sanatan daga baya





A karshen tikewa dai Sanata mai wakiltar gabashin Kogi Dino Melaye ya karbi takardun shaidar karatun sa na Digirin farko a Jami’ar Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya bayan an ta ce-ce-ku-ce a shekaran jiya Jumu’a da rana.

An tasa Sanatan a gaba inda aka ce bai kammala karatun sa ba, sai dai shugaban Jami’ar ta A.B.U Farfesa Ibrahim Garba ya wanke sa a gaban kwamitin Majalisar. Bayan nan ne Sanatan yace zai karbi satifiket din na sa wanda bai karba ba tun tuni idan ya zo darasi makon gaba don kuwa yanzu yana karatun wani Digiri na uku a Jami’ar.




Dino Melaye bai samu zuwa ba wancan makon saboda ana hutun rabin zango a Jami’ar. Sai wannan mako ne ya samu karbar takardun na sa. Na zagaya har gaban ofishin Jami’ar na Senate inda matasa su ka yi cincirindo suna jiran gwanin na su.

Dino Melaye ya karbi takardar sa ya kuma zagaya ya ga shugabannin Jami’ar irin su Rajistra Mal. A.A Kundila. A karshe dai ya karbi takardar satifiket din sa inda yace ‘yan bakin ciki sun sha kunya.





[NAIJ Hausa]

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...