Saturday, January 13, 2018

HUDUBAR JUMA’A DAGA MIMBARIN ITN-ZARIA


Dagewa wajen neman halal-Daga Bakin Imam Dr. Saeed Muhammad Yunus

 

 

Assalamu Alaikum wa Rahmatul Lah, 




Godiya ta tabbata ga Allah SWT tare da tsira da aminci ga Annabi SAW da Alayen sa da Abokan sa da dukkan wadanda su ka bi hanyar sa zuwa ranar karshe. Bayan haka, ‘Yan uwa mu sani cewa lallai addinin Musulunci, shi ne addinin bi. Duk wanda ya bi Musulunci ya dace da rayuwa wanda ba ta da tabbas. Wanda ya wayi gari cikin Musulunci shi ne ‘dan-gata! 

Musulunci ya kwadaitar da mu da aiki wajen neman halal, kuma duk inda Mutum zai tafi ya nemi kudi, ya yarda matukar ba Haram bane. An tambayi Manzon Allah game da hakan, sai yace ana iyawa. Ina maku wasiyya da kai na ‘Yan uwana, da mu ji tsoron Allah. Ni’imomin Allah daga ciki akwai Musulunci, ka daina ganin Musulunci karamin abu, babba ne! Da Allah ya so, da yanzu duk nan da mu ke Masallaci mu na gidan giya. Allah ka kiyaye! Allah mun gode maka. Allah kai ka gusar mana da damuwa na firgicin da mu ke ciki a kwanakin baya. Ya Allah Kai Ka sihirce mu daga al’aura kamar yadda Hadisin ka na Kudusi ya fada. Ubangiji, mun san mu na ta saba maka, da ka ga dama da Ka damke mu, amma Allah kace za ka jinkirta mana; Mun san Ka yi wa Annabin mu alkawari cewa za ka dagawa Al’ummar sa kafa ba kamar yadda ka yi wa Mutanen Annabi Lud ba, ba kamar yadda ka yi wa Mutanen Salihu ko yadda ka yi wa Mutanen Hudu ko Mutanen Fira’una ba. Allah ka dagawa Al’ummar Annabi Muhammadu kafa cewa su yi ta abin da su ka ga dama kuma kamu yana nan zuwa Ranar kiyama. Allah ka da Ka kamu da abin da ba za mu iya ba! 

‘Yan uwa mu sani cewa Musulunci ya shar’antar da mu rika biyayya ga shugabanni da masu karanatar da mu. Sun fada mana cewa lallai dukiya, abu ce wanda ake nema domin a ji dadi. Muslunci ya kuma kwadaitar da neman kudi da kuma yadda za ka batar na tsarin rayuwa. Daga ciki ne aka fitar da maganar zakka, amma Wawaye daga cikin mu, su na gani cewa zakka tana rage dukiya. Annabawa da Manzanni sun taru gaba daya cewa a tsarewa Mutane rayuwar su da dukiyar su da hankalin su da kuma mutuncin su bayan tsare masu addinin su. Wajibi ne kowa ya sani cewa dukiya kawa ce ta Duniya, cikin Al-Kur’ani, Suratul Kahfi tana cewa kudi da ‘ya ‘ya kawa ne na Duniya. Wanda ya ki bada hakkin Allah ya shiga uku ya lalace. 

Kudi abin kauna ne, Musulunci bai ki kudi ba, Musulunci yana kaunar kudi; inda za a nemo na halal a doron kasa a nemo na gina addini. ‘Yan uwa ku sani cewa mu na bukatar masu kudi da za su taimaki addini, su gaskata abubuwan da Ubangiji ya fada na cewa dukiya na d’aga al’amurra. Ubangiji na gyarawa da masu mulki abin da bai gyarawa da masu ilmi haka kuma kudi na shiga inda ilmi bai shiga ba yayi aiki na ban mamaki. Ku duba yadda Abubakar RA wanda ba shi aka ba Annabta ba, amma yayi aiki da kudin sa. Sai ga shi Ubangiji yana fadar martabar Sa a Al-kur’ani. Mu na bukatar masu dukiya; ku sani cewa dukiya makami ce, idan har ta shiga hannun mabarnaci zai ta kashe mutane ne. Idan kuma ta shiga hannun Bawan Allah kuma sai yayi ta gyara da ita kamar yadda Abubakar RA da Uthman RA da su Abdurrahman bin Auf RA su ka yi da dukiyar su. 

Ku duba yadda Musab ya fito daga gidan kudi saboda Kalmar shahada. Wanda ake cewa ‘Dan Lu’u’lu’u kamar yadda a wani zamani yaron Shugaban kasa ke cashewa cikin jirgi a sama. Musab yana cikin irin wadannan, amma da ya ji kiran Manzon Allah, ya watsar da wannan, sai ya dawo masallaci yana kwana. Sai ga Musab ya rasu a wajen jihadi ya dawo bai da linkafani. Annabi bai da inda zai ajiye Musab amma sai ga Musab ana saka masa ciyawa za a birne sa wanda Abdurrahman ‘Dan Auf da sauran Sahabbai su ka rika kuka. Ku duba Uthman RA wanda ya auri ‘Ya ‘yan Manzon Allah har 2, Annabi SAW yana cewa: Babu abin da Uthman zai kara mummuna a Duniya. ‘Yan uwa idan dukiya ta fada hannun mugun mutum sai yayi barna kamar yadda Allah ya fada a Al-Kur’ani yana cewa: ‘Ina amfanin wuta, mutum ya shiga wuta?’

‘Yan uwa mafi girma daga cikin Musulmi shi ne wanda yake jin magana idan an fada masa. ‘Yan uwa, kasala ba ta ga Musulmi ba. Musulunci ‘dan izza ne. ‘Yan uwa an ga albarkar noma a Kasar mu. Kowa ya koma yaje yayi noma, a nemi halal! Manzon Allah yana cewa a ci da halal kuma a nemi halal! A yi wa iyali hidima da halal, ka da a ci haram. Ka da kuma ka raina halal duk yadda ta ke. Manzon Allah SAW yace da Sa’ad bn Abi Waqqas da ya bar yaran sa da kudi ya fi ya bar su, su na roko. Manzon Allah SAW yace ka da a kuma wulakanta wanda ake ciyarwa. 

‘Dan uwa, wadanda ke cewa Musulmi bai dace da neman dukiya ba macuta ne. Karya ce! Allah yace babu wanda ya hana kawa ta Duniya. Allah yana so ka yi shiga mai kyau wanda idan ka fita cikin Abokai za a ce kayi kyau. Ka sa riga ta daukaka ta buwaya da kuma gidan ka mai kyau da abin hawan da ka ke da shi (keke ko babur) sannan iyalin ka ma su sa mai kyau. Wani Sahabi ya tambayi Annabi SAW ya kuma fada masa cewa wannan ba riya bane. Amma abin da Annabi SAW mai daraja ya fada shi ne duk wanda ya sa tufafi yana mai girman kai, lallai Allah SWT sai ya sa masa tufafi na kaskanci a gobe kiyama. ‘Yan uwa mu da iyalin mu, mu sa kaya masu kyau. Yara su fito cikin Hijabi. Allah yace ku je ku nemi kudi a doron kasa. 

Sayyidina Umar RA ya taba fitowa sai ya ga wasu mutane sun zauna a gindin wata bishiya bayan Sallar Juma’a. Da yace su wanene wadancan, sai su kace: Su masu tawakalli ne kuma Allah Madaukaki kawai su ke jira ya ba su. Sayyidina Umar yana da wata sanda da yake yawo da ita, sai ya bi ta kan su, ya kwala masu, yace ku fita ku nema arziki, Musulunci ba ‘dan wulakanci bane. Umar yace ba ku ji Kur’ani yace bayan Sallar ku, ku fita ku je ku nemi arziki ba. Ahmad ‘Dan Hambali (Allah yayi masa rahama) bai yarda wani yayi dogaro da Allah ya tashi zuwa Garin Makkah ba. ‘Dan Hambali yace ka fara neman guziri, sannan ka kama hanya, amma idan guzuri ya kare, sai ka dogara da Allah. Sayyidina Umar ya hana ka zauna kace Allah zai kawo arziki, yana cewa ai ka san sama ba ta ruwan zinari!

Huduba ta biyu bayan godiya ga Allah da yabo ga Annabi SAW wanda ya sa mu ka zama mafificin Al’umma. Allah ka kara masa daraja da wasila da fadila, Allah ka samu cikin haunin sa a gobe kiyama. ‘Yan uwa ku sani cewa Musulunci ba addini bane na lalaci. Duk wanda ya samu dukiya, amma bai yi abin da aka ce ba, ya lalace yayi asara. Tir da wannan dukiya da ta kasance an sa ta inda ba ta dace ba. Malamai su na cewa komai kankantar dukiya da aka yi abin da bai dace ba, an yi almubbazaranci. 

‘Yan uwa mutane da yawa a yau sun rabu dabam-dabam; akwai masu zaman benci su na gulmar shugabanni, idan Malami mai arziki ya wuce a duba rigar sa. Idan wani Kamsila ko wani ya wuce, su yi tayi da shi. Ba su da aikin yi sai zagin mutane. Wadannan mutane ba su da komai sai zunubi. Annabi SAW yace a Ranar Kiyama, za a nemi irin wadannan mutane su bada hakkin Majalisi. Huduba tana kiran Samari da Dattawa cewa za a karbe ladar su, a ba wadannan, idan har ta kama, sai a dauki aikin banzan wannan mutumi, a jefa maka. Wadannan mutane ba su fita nema, su na ganin wani aikin bai dace da su ba; ba zai iya yin faskare ko yayi dako ba, ba zai iya zuwa kasuwa ba, amma da kudi za su cika Masallacin nan, da su na gaba. Irin wadannan mutane ne sai ka ji su na cewa da za su samu kudi, da sai sun fi wane-da-wane kirki. Al-Kur’ani a Suratul Taubah ya fada mana ba haka ba. A cikin su akwai wanda Allah ya jarabce sa yayi kudi na ban mamaki, amma da aka saukar da ayar zakkah, sai yace domin sa aka saukar da ayar. 

‘Yan uwa yau da yawa daga cikin masu kudi su na kiyayya da zakkah. Wani ma da aka yi masa lissafin zakkah sai yace ba gaskiya bane, wani kuma yana cewa dubarar Malamai ce. Masu kudi ku sani cewa kun zo Duniya ba ku da komai. Ina kiran ku Wallahi ku bada hakkin Allah, za ku bar baya da kura. ‘Yan kasuwa da masu sufuri na fatauci da masu saida fetur da Jami’an hanya da Ma’aikatan Gwamnati da mai saida taki a ji tsoron Allah. Kowa ya san irin abin da yake yi; duk dukiyar da ka nema ko ka tara ba ta halal ba, kuma duk dukiyar da ka matsawa Musulmi ka samu, ba za tayi albarka ba. 

Wallahi Tallahi kila ka taba jin wannan maganar, gobe za ka tsaya gaban Allah. Ba za ka iya cin abin da ba rabon ka ba. ‘Yan uwa ku duba yadda aka rika kama Jama’a a cikin Kasar nan sun saci dukiya. A kasar nan an rika kama beraye wanda su ka saci dukiyar al’umma. Har iyaye mata da aka sani da rikon amana sun samu mukami, su kayi cin amanar da ba a taba yi ba a tarihin wannan kasar. Dukiya ana neman ta ne domin rufawa kai asiri amma ba ko ta wani hali ba. A lokacin da Sahabban Manzon Allah su ka samu kudi, wasu sun rika kuka, su na cewa bala’i ya zo! Akwai lokacin da bayan Sallah sai aka ga Annabi SAW ya fita a guje yana taba kafadun mutane. Sahabbai su na ta mamaki, sai yace wata dukiya ce ya manta bai ajiye ta inda ya kamata ba, sai ya kawo ya rabawa Jama’a. 

‘Yan uwa ace kullum kai ke nan maganar masu mukami, alhali kai ka gaza rike na ka mukamin da aka ba ka. A kan abin da aka ba ka, za ayi maka tambaya a gobe kiyama. Ka da ka raina abin da ka ke samu, ka zama mai godiya. Allah yayi alkawarin ba kowa bane zai yi kudi don yace zai budawa wasu sannan kuma ya kuntatawa wasu, duk wanda ba a ba sa ba, ya ciyar da daidai karfin sa. ‘Yan uwa ‘Yan Najeriya, yau haram ta zama abin ado, an samu lokacin da yanzu wani yace: Wanda ya hana zalunci ma Azzalumi ne! Wannan mummunan kalma ce! Annabin Rahma yace a nemi haram. Ko me yake damun wadanda ke sa abinci su yi tsada? Ko wadanda aka ba amana su ci ta? Me ke sa kananan yara su na satar kayan iyayen su? Samari sun ki karatu sun buge da sata? Me ya sa mata ke sata a gidajen biki? Me ke damun al’umma ta rude? Ko ina za a je ne? Ko ba mu bane al’ummar Annabi. Mu ne fa mu kace Allah ya canza mana kuma ga shi ya canza. Ko har mun gaji ne? Inalillahi wa Inna ilaihi Raji’un. 

‘Yan uwa ku kara naziri game da tafiyar Najeriya kamar yadda Saudiyya ta ke Garin Mutanen Annabi Muhammad. Allah Mai Girma duk zai yi masu hisabi a gobe kiyama, Allah kuma ba ya kallon daraja ko launin ko sai zuciyar ka. Kowa so yake ya samu dama a Najeriya. Jini ya zama jinin sata, jijiya ta zama ta barayi; Jami’an tsaro na jira ayi hadari su fara leka aljihun Jama’a. Kowane mataki ka shiga na karatu, za ka samu Malamai da wannan hali. Wani yana Allah-Allah ya samu wata dama ya dauke kayan ‘Dan uwan sa. Annabi yace: Babu ruwa na in ga wani a gobe kiyama da akuyar sata. Ko karfen Masallacin nan ka sace, gobe sai ka zo da shi filin kiyama. 

‘Yan uwa mu bi a hankali, hanzarin yayi yawa don kiyama ta kusa. Kiyama ta dosa amma mutane su na cikin gafala. Annabi yace kiyamar nan ta kusa. Mu roki Allah ya kara mana son Manzon Allah da zama cikin hakuri da tanadi da neman halal. Allah kuma ya karawa masu dukiyar kirki albarka. Allah ya sa su ciyar da hakkin ka. Allah ka sa mu zauna lafiya kayi mana maganin Barayi a kowane mataki. Allah ka sa masu satar dukiya su daina ko ka canza mana su da wasu. Allah ka wahalar da wanda yake so ‘yan kasa su wahala. Allah ka zaunar da mu lafiya. Allah ka kawo mana karshen rikicin Benuwe da nan Kaduna da Jihohi dabam-dabam. Allah mun tuba da laifin mu. Allah ka daidaita tsakanin Malaman Jihar Kaduna da Gwamnan su. Allah ka jikan wadanda su ka riga mu gidan gaskiya. Allah ka sa kabarin mu ya zama dausayin Aljannah. Ameen!





Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga Masallacin I.T.N-Zaria.
Muhammadmalumfashi@gmail.com          
Twitter: @Ya_waliyyi








Sunday, January 7, 2018

How Argetina had 5 Presidents in less than 2 weeks in 2001


History: The time Argentina had 5 Presidents in 13 days

 




It did happen after the political crisis caused by the devaluation of the peso on November 2001 by then president Fernado de la Rua. It was a little more than a week and these were the 5 presidents, back in 2001


1) Fernando de la Rua, Argentina's president, resigned on December 20, 2001 after devaluing the peso and restricting withdrawals from banks.

2) As the vice-president had already resigned, the president of the Senate, Ramon Puerta, while Congress decided on the new president.

3) Congress decided to name Adolfo Rodriguez Saa as interim president.

4) He resigned on December 31, leaving the President of the Chamber of Deputies, Eduardo Camaño,
 as interim president.

5) On January 2nd, 2001, Eduardo Duhalde was named president by the Congress.


Source: Quora

Monday, January 1, 2018

List of forgotten Friday Sunnan



A Compilation of Some Neglected Sunan

- By Shaykh Al-Albaani


 




Here are some abandoned Sunan that are missing among many people of today. Consider them carefully and try to practice them in order to get the rewards in this life and the next:


1. Salaatud-Dhuhaa: and especially during the time when the sun is very hot. Allaah’s Messenger (صلى الله عليه وسلم) said: The prayer of those who are penitent is observed when your weaned camels feel the heat of the sun.[Muslim]

2. Lengthening the time of uplifting after Rukoo’ and the time of sitting between the two prostrations. This is clear in the hadeeth narrated by Anas (radiAllaahu ‘anhu) who said: “I spare no effort to make the Salaat of the Prophet (صلى الله عليه وسلم) amongst you and (teach) you (to) offer it as I saw him offering it amongst us.“ He (Anas) said: “The Prophet (صلى الله عليه وسلم) did something which is missing amongst you. He used to stand after the bowing for such a long time that one would think that he had forgotten, and he used to sit in between the prostrations so long that one would think that he had forgotten the second prostration.“ [Bukhaaree]

3. Performing the Iq’aa (setting up one’s feet (on the toes) placing the buttocks on the heels) while sitting between the two prostrations. It is narrated from Abee Zubair that he heard Tawoos saying: We asked Ibn ‘Abbaas (radiAllaahu ‘anhumma) about Iq’aa, and he said: “This is the Sunnah.” [Muslim]

This Iq’aa is different from the one warned against, wherein the man sits placing his buttocks on the ground and setting up his feet on the toes.

4. Du’aa after the final Tashahud and before the (Tasleem) salutation ending the prayer. It is desirable to do so, invoking for what one wishes of the good of this life and the next. The Messenger of Allaah (صلى الله عليه وسلم) said to his Companions when he taught them how to say the Tashahud: “Then he (the one praying) may choose what pleases him of supplication and offer it.” [Muslim]

5. Offering Salaatun-Nafl at home. This Sunnah is proved by the hadeeth of Ibn ‘Umar (radiAllaahu ‘anhumma) who said: The Messenger of Allaah (صلى الله عليه وسلم) said: “Offer some of your prayers (Nawafil) at home, and do not take your houses as graveyards.” [Bukhaaree]

Ibn al-Qayyim (d. 751H, rahimahullaah) said in his book Za’adul-Ma’aad: “And he (the Prophet) would offer all of the Sunan and the voluntary prayers at home, especially the two Rak’at of Maghrib which he was not reported to have done in the mosque.”

6. Offering the voluntary prayers on the horse back (this nowadays includes the car and all the modern means of transportations). ‘Abdullaah Ibn ‘Umar would offer the voluntary prayer during travel on his horseback. Wheresoever it went (in whatever the direction the horse went), he would make an indication with his head (indicating ruku’s, sujood, etc.). He (Ibn ‘Umar) said that the Messenger of Allaah (صلى الله عليه وسلم) did the same.

7. Reciting Soorat al-Ikhlaas and al-Kafiroon in the optional Fajr (the two rak’ahs before the obligatory Fajr prayer). Aboo Hurairah (radiAllaahu ‘anhu) said: “The Prophet would recite during the two rak’ah of Fajr: Say (oh Muhammad to them): Oh disbelievers…(Soorat al-Kafiroon) and Say (oh Muhammad to them): He is Allaah, The One…(Soorat al-Ikhlaas).“

8. Offering two-rak’ah prayer by the one who returns back from a journey and before he meets his family.

Jaabir ibn ‘Abdullaah (radiAllaahu ‘anhumma) reported: “The Messenger of Allaah (صلى الله عليه وسلم) bought a camel from me. When he came back to Madina, he ordered me to come to the mosque and observed two rak’ah of prayer.“

Imaam Nawawee (d. 676H, rahimahullaah), explaining this hadeeth, said: “This hadeeth encourages for offering two rak’ah in the mosque immediately after arriving from a journey.“

9. Offering prayers between Maghrib and ‘Ishaa:

It is narrated from Hudhaifah (radiAllaahu ‘anhu), who said: “I came to the Prophet (صلى الله عليه وسلم) and offered the Maghrib prayer with him, and then he continued praying untill ‘Ishaa.” [Saheeh Ibn Hibbaan]

10. Going to bed after making the ablution:
It is narrated from Abu Hurairah (radiAllaahu ‘anhu), who said: The Prophet (صلى الله عليه وسلم) said: “He who goes to bed Taahiran (pure; purified from ritual impurities by means of wudu` or ghusl) after making ablution, then an angel shall sleep under his quilt invoking Allaah: ‘Oh Allaah: Forgive the sins of your servant so-and-so, for he slept pure.‘ The angel would do so at any moment the sleeping person wakes up during his sleep.“ [The Hadeeth is Hasan, as-Silsilah as-Saheehah no. 2539]

11. Offering prayers with one’s shoes on:

This is a neglected sunnah that can hardly be seen nowadays, and not to mention that if you see someone doing so, you might (sadly, ignorantly) disapprove of what he did.

It was narrated from Shaddaad bin ‘Aws that the Prophet (صلى الله عليه وسلم) said: Act differently than the Jews, for they do not offer prayers with their shoes and slippers on. [The Hadeeth is Saheeh, Saheehul-Jami' no. 3210]

In this Hadeeth, the Prophet (صلى الله عليه وسلم) commanded his Companions and then us to offer prayers with shoes on.

It was also narrated from Sa’eed Ibn Zaid (radiAllaahu ‘anhu) that he said: I said to Anas Ibn Malik (radiAllaahu ‘anhu): Did the Prophet (صلى الله عليه وسلم) offer prayers while he had his shoes on? He (Anas) said: “Yes.” [Bukhaaree]

12. Not to offer the nafal (the voluntary prayer) after the obligatory prayer except after he speaks or changes his place.

Mu’aawiyyah (radiAllaahu ‘anhu) narrated: The Prophet (صلى الله عليه وسلم) ordered them not to attach a prayer to another until they speak or leave (their place).[Reported by Muslim]

Abu Hurairah (radiAllaahu ‘anhu) narrated: The Messenger of Allaah (صلى الله عليه وسلم) said: When it is Friday, the Angels stand at every door of the mosque and write down the names in the order of their arrival. When the Imaam sits on the pulpit for delivering the Khutbah, they fold up their sheets (record book) and listen to the Dhikr. The early comer is like one who offered a she-camel as a sacrifice, the next like one who offered a cow, the next a ram, the next a chicken, the next an egg.[Saheeh Muslim (7/406)]
  

Source: From an article by Imaam al-Albaanee titled “Sunan Mahjooran,”

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...