Saturday, November 18, 2017

Hudubar Juma’a game da Malaman Makaranta





Hudubar Juma’a daga Mimbarin ITN-Zaria

 

‘Hudubar Juma’a game da harkar Ilmi a ban kasa da Jihar Kaduna -Daga Bakin Imam Ustaz Sa’eed Yunus.

 

 

Assalamu Alaikum wa Rahmatul Lah, 

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah SWT, tsira da amincin Allah su tabbata ga wanda babu Annabi bayan sa, Shugaban mu, kuma Annabin mu, farin Jakadar Allah; Annabi Muhammadu SAW, tare da iyalan sa da Sahaban sa tare da duk wadanda suka bisa da kyautatawa zuwa har Ranar karshe.
Bayan haka, mu sani cewa mu na cikin wani lokaci da mu ka shiga cikin wani hali a ban kasa. Babu abin da ya jawo wannan sai rashin karatu da neman ilmi. 

Ilmin da ya kamata a maida hankali a kai sun hada da: Na farko, dole a komawa Al-Kur’ani, ayi aiki da shi ana tadabburi kuma tare da haddacewa kamar yadda Allah ya fada. Sannan kuma ilmin fassara Al-Kur’ani watau Hadisan Manzon Allah SAW. Sannan kuma ilmi na Akida wanda ke fitar da mutum daga sharrin shirka. Sannan kuma da ilmin nan na Fikihu. ‘Yan uwa masu girma ilmi yana da yawa; daga ciki har da ilmi na harshen larabci wanda za ayi magana da shi a gobe kiyama gaban Allah SWT. Da yaren larabci aka saukar da Al-Kur’ani. Daga cikin ilmin da ya kamata a ba muhimmanci akwai ilmin kimiyya, tattali da kuma shari’a da kuma ilmi na koyan Malanta. Duk wani ilmi ya kamata ace an samu Musulmi a wannan wuri. Daga cikin ilmi masu amfani kuma akwai ilmi na aikin Soja wanda za a juya duk wani makami wanda za a kare addini kamar yadda Al-Kur’ani yake cewa ku yi tanadi na kare kai! Ana bukatar masu tare wurare na harba bam domin kare addini a kuma kare kasa da manyan kasa. Yanzu wadannan mabarnata masu garkuwa da mutane a kasa, ya kamata ace an samu ilmin da zai kawo karshen su. 

Huduba tana kuma kira gare ku da a samu ikhlasi watau tsarkin niyya. Idan aka ce kai Injiniya ne, to ka zama Musulmin Injiniya, ko kuma ace kai Musulmi ne kuma Likita ko kuma Soja ko Malamin Makaranta ko kuma Makanike ko mai aiki a Kamfani amma Musulmi. Kuma don Allah duk wadanda za su rubuta wani abu da Dalibai su ke amfani da shi su ji tsoron Allah. Wallahi idan har ka sa abin da kuma zai bata tarbiyyar yara za kayi bayani a Ranar tashin kiyama ka gane kuren ka. Ku san irin Makarantun Bokon da za ku sa yaran ku; wasu iyayen su na jefa yaran su cikin tabo sannan kuma su na cewa ka da yaran su jike, wannan hauka ne! Sai ka ga mutum ya dauki diyar sa ya kai wurin wadanda ba Musulmi ba. Saboda haka yana da kyau mu gyara don kuwa za a tambaye ku a gobe kiyama. 

Sannan kuma Malaman Makaranta ku ji tsoron Allah don ku na da hakki da kuma abin da za su ku fada. Hudubar yau tana jinjinawa Malamai, ina gaishe ku Malaman Makaranta. Malaman Makarantar Gwamnati ba wanda yake koyarwa a Makarantun kasuwa ba. Ni ina ce maku ‘Salamu Alaikum’ don kun cancanci gaisuwa, ku ne Malamai na gaskiya kuma na san aikin da ku ke yi. Kun cancanci a ba ku tukwuici a duk matakin da ku ke na firamare ko sakandare balle ma kuma Jami’a uwa-uba.

Amma kuma abin bakin ciki sai aka samu irin wannan tafiyar a yau ta tabarbare. An samu wasu da su ka je su ka koyi karatu daga kwaleji ko FCE kuma su ke karantarwa da kyau. Wasu kuma sun shiga hakkin yara; ba a shiga aji ba kuma a kula da yara. Malamai ku ji tsoron Allah, wannan abin shi ya jawo bala’in da aka shiga a Jihar Kaduna, Allah kadai ne zai yi hukunci gobe a kiyama, wannan abun bakin ciki ne. Allah shi kadai ne mai cikar kamala don babu wanda za ayi wa jarrabawa a ce sai ya ci dari-bisa-dari, amma kun ci amanar kasar ku gaba daya. A makarantun na fa kitso ake yi da sayar da atamfa, kungiyoyi su yi ta kawo tallace-tallace. Sai yara su tafi Makaranta amma ba ayi masu komai ba! Shekara nawa aka yi ana wannan abu? Wallahi ya fi shekaru 30 ana haka! Wadanda su ka sani sun sani, wadanda ba su sani ba, sun jahilta. Wannan itace al’adar Malamai (ba na Jihar Kaduna ba kurum). Idan aka ce a Kaduna kadai ake wannan an zalunci Malaman Jihar, kusan kaf Najeriya ta Arewa shekaru 30 da su ka wuce Malamai kan yi wasa da aikin su. Sannan kuma aka samu Gwamnoni da su ka rika daukar mutanen da su ka cancanta da wadanda ba su cancanta ba, an maida karantawar kamar bola. Lokaci ya kai ana kawo wadanda ba Malamai ba amma su na koyarwa ba tare da sun san komai ba su na karanatar da yara!

‘Yan uwa ku ba ni labarin wadanda aka kama bayan shigowar Gwamnatin Shugaba Buhari su na da ‘ya ‘ya a gida amma ana ba su albashi. Sai ka ga mutum da matan sa 4 da ‘ya ‘ya 24 amma kowane yana samun albashi a karshen wata. Tsakani ga Allah ba canji ku ka nema ba? Kun nemi canji sai Allah ya kawo maku, sai kuma ku ce ba ku yarda ba? Ka na bakin ciki don an kama ‘Dan uwan ka da laifi ba ya shiga aji? ‘Dan uwan ka ya ci amanar hukuma, ba gara ya zama an kama sa tun a Duniya ba a kafin ya isa lahira ya ji kunya? Saboda haka ku ji tsoron Allah, abin da baki ya fada zai iske shi a gobe kiyama. 

Annabawan Allah sun yi gwagwarmya; Annabi Musa AS yayi fama da Fir’auna; Bani Israila sun kai kuka cewa ana kashe su har Allah ya kashe Fir’auna, sai ga shi wadannan mutane sun kuma nemi a kera masu gunki. Annabi Musa AS yace wadannan mutane ba su fahimci abubuwa ba. Ko su ku ke mu ma ayi shekara 40 ana yi mana azaba? Annabi Muhammad SAW ma dai bai kubuta ba don har ta kai Sahaban sa sun nemi Allah ya kawo yaki yayin da aka umarce su da su yi ta sallah. Sai ga shi a lokacin da aka hukunta yaki su na jin tsoro su na cewa meyasa aka ce su fita yaki. Jama’a ku kuce ‘Mai Rusau, Mai Rusau!’Ga shi kuma ya zo ya rusa kuma yana ta rusawa kuma kun ce ba ku yarda ba! Ku na so ku shekara 40 kenan a wulakance? Wallahi ba kamfe bane! Wallahi ba kamfe bane! Wallahi ba kamfe bane! Gaskiya ce dole kuma a fada! 

Ko kun ki ko kun so wanda ya gama Gwamna abin yabo ne amma ku ka zage sa, ga shi kuma Allah ya kawo wannan. Abin bakin ciki shi ne a kan Musulmi duk tsinuwar ta ke karewa; Musulmi ke zagin ‘Dan uwan sa. A karatun da Malam yayi, yake cewa idan tsinuwar ba ta hau kan sa ba za ta hau kan ku kuma sai ta tafarfasa ku. Shiyasa mu na nan mun kasa cigaba har yanzu. Al-Kur’ani ya fada mana cewa; Allah ya kama Fir’auna da Hamana da duk masu laifi. ‘Yan uwan ku kiyaye wannan kamun na Allah. 

Huduba tana rokon Allah ya azurta mu da ilmi mai amfani. Ina neman gafara gare ku ‘Yan uwa. Sannan bayan godiya ga Allah huduba tana cewa Jama’a ku ji tsoron Allah, ku kiyayi ha’inci na jarrabawa da ake yi, ku kiyayi kai yara Makarantun da ake kira Miracle Centres da ake cin jarrabawa, karya ne munafunci ne. Yaran Musulmai su ka cika wadannan Makarantu alhali su su na Makarantun Gwamnati. Makarantun nan na Gwamnati su ne Makarantun asali, lalata su aka yi. Sai ace wai Shugabanni sun ki kai yaran su Makarantun Gwamnati, ku ina ku kai na ku yaran? Ka yarda cewa diyar ka ta je Makaranta da hijabi na Sunnah amma daga ta isa bakin Makaranta sai ace ta tube? Mun dauki amanar yaran mu, mun kai wurin wadanda ba mu ba! Wannan fa shi ne yake ba ta tarbiyya, wanda bai da abu ba zai ba da shi ba. 

Ku Malamai na Jihar Kaduna ku gyara al’amarin ku, ku ji tsoron Allah. Wasu ne su ka jawo maku wannan bala’i, ba laifin ku ba ne duka Wallahi! Idan ka shiga Jami’ar Ahmadu Bello za ka ji ba za ka iya kwashe ‘Daliban da su kayi jarrabawar kwanan nan ba. Kuma ku duba Daliban da aka fitar zuwa Kasar Uganda domin karatun likitanci amma an dawo da su, meya faru? Duk wadannan mugayen Makarantu su kayi. Amma kun tambayi tarihi mana. 

Don haka ina kira ga Hukuma ta ilmi da duk wani mai ta cewa, ni dai na fadi nawa a matsayi na ‘Dan uwan ku Musulmi; Malaman nan da aka kora a duba al’amarin su, ya ku Gwamnati, ka da ku kori Malamai. Amma duk wanda ya kasance ba Malami bane, ba na goyon bayan a cigaba da tafiya da shi. Ina kira ga Gwamnati don Allah a ba su hakkin su. Malaman nan fa Malamai ne ba za a hada su da wadannan yara ba da ake shirin dauka Wallahi! Ku yi hakuri, da tsohuwar zuma ake magani. A gyara su ne kawai. 

Ku kuma Malamai ku iya bakin ku, ku tuna da Hadisin Manzon Allah da ya ga wasu ana yanka bakunan su da lauje a kabari, da Manzon Allah ya tambaya a kan su sai aka fada masa cewa su ne masu fadar abin da ba su sani ba. Kun zagi wancan Gwamnan, kun zagi Gwamnan da ya wuce, wanda ya wuce ya zama Sanata kun tsine masa, gobe kiyama sai ka fadi abin da Gwamna yayi maka! Tsoho Baba Buhari wadansu har sun fara zagin sa, shi ma ma sai ka fadi abin da yayi maka a gobe kiyama. Ka kiyayi bakin ka Musulmi don duk baki ya jawo mana wannan. 

Mu tambayi tarihin su Sardauna da su Tafawa-Balewa wadanda su ka jawowa kasa izza amma yanzu an jawo mana zilla. Idan ba mu bane da mulkin kasar nan sai ka ji bakin Jama’a shiru, amma daga na mu ya samu sai ka ji ana ta ‘Allah ya tsine.’ Ka sani babu abin da za ka samu saboda wani Gwamna ko yanayi. Matsalar tamu ce mu kan mu, kuma sai an tambaye mu a kiyama.

Huduba tana cewa lallai ku kiyayi ka-ce-na-ce watau kila-wa-kala, ku kiyayi mugun zato ga Musulmi. A kuma daina zagin Shugabanni, a daina tsinewa Malamai, kiyayi zunubi da sabon Allah wanda shi ya jawo mana wannan bala’i. Yau ba mu da Soja mai gaskiya; barikin nan na Zariya an koro yaran mu sama da 800 don ba su da takardun shaida. Meya faru? Sun je Miracle Centers domin jarrabawa. Ga su nan a Jami’a kuma; a dalilin rashin Jarrabawar nan na Post UTME yanzu an yi jarrabawar aji daya duk sun fadi saboda ba a tace ba, su ma sun je Miracle Centers.

 Iyaye ku ji tsoron Allah ku samawa yaran ku Makarantu na gaskiya. Lauyoyin mu, ku zama masu fadar gaskiya. Likitocin mu ku ji tsoron Allah, ilmin ku yayi amfani. Ya kai mai neman Shugabanci ka ji tsoron Allah. Ka sani cewa kabari na nan yana jira. Ya kai wawa wanda ka rafkana, ka dauki Duniya wajen zama, ya kai Saurayi da ka ke ganin za ka dade, Ya kai Shugaba da ka ke danne hakkin Jama’a, ya kai da ake shugabanta da ka ke zagin Shugabanni, duk ku sani cewa akwai tsayuwa gaban Allah kuma akwai kabari. Wallahi kabari sama turbaya ne kasan sa babu wanda ya sani sai Allah! Yau ga shi ka mutu kai ne mai surutu a wata Majalisa. 

Allah ya hada mu cikin masu son gaskiya da riko da gaskiya da aiki da gaskiya. Allah ya sa kabari wajen hutawar mu ne. Allah ka sa mu karbi littafin mu da hannun dama. Allah ka taimaki Shugabannin mu na kirki, wadanda ba za su gyaru ba ka canza mana su. Allah ka biyawa kowa bukatan sa mazan mu da matan mu!

[Akwai wasu sashe na hudubar Malam da su ka shafe daga na’ura]

Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga Masallacin I.T.N-Zaria. Muhammadmalumfashi@gmail.com           Twitter:@Ya_waliyyi

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...