HUDUBAR
JUMA’A DAGA MIMBARIN ITN-ZARIA
HANI
DA ABIN KI DA KUMA KIRA GA ABIN ALHERI A ADDINI DAGA BAKIN IMAM SHEIKH S. S
ABUBAKAR
A’udhu BilLahi minasshaidan
Ar-Rajim, BismilLahir Rahman Ar-Raheem,
Bayan godiya ga Allah SWT!
Allah Madaukaki ya sa wannan
al’umma ta zama mafificiyar al’umma; ita ce al’ummar da ta ke umarni da alheri
kuma ta ke hari game da abin ki da shari’a ta hana. Mu na godiya ga Allah SWT bisa
ga abubuwa da dama na ni’ima, mu na kuma shaidawa cewa babu abin bauta da
gaskiya sai Allah Mai Girma; shi kadai yake, babu abokin tarayya. Allah Ya
wajabta ayyuka na alheri da abubuwan da za su kai ga rabota kuma Shi ne yayi kira
a samu masu umarni da alheri da hani ga mummuna.
Muna shaidawa lallai Shugaban
mu, Annabi Muhammad SAW, Bawan Allah ne kuma Manzon Sa ne. Shi ne wanda yake
rike da tutar kira ga Allah da kuma jihadi wajen daukaka Kalmar Allah da kuma
gwagwarmaya wajen gyara a kasa.
Saboda haka, shi ya shiryar da Sahaban
S\a bisa tafarkin da ya dora su akai.
Bayan
haka ‘Yan uwa, Imani ga Allah da bin tafarkin gaskiya da kuma yin nasiha da
Allah da Manzon sa da littafin sa da kuma tsakanin junan mu da kuma yin nasiha
ga junan mu na taimakekeniya da hakuri wajen aikin gaskiya tare da kuma cewa mu
ne masu yada abubuwa na alheri da falala sannan da yaki da sharri da duk wani
abu na kasakanci a doron Kasa da tunbuke abubuwa na sharri a al’umma. Duk
wannan su na cikin alamu mafi bayyana na al’ummar Annabi Muhammad SAW. Ta
hanyar wadannan ayyuka ne wanan al’umma ta kerewa sauran al’ummai kamar yadda
Allah SWT ya fada cikin Al-Kur’ani cewa: ‘Ku
kun tabbata mafificiyar al’umma… ku na masu umarni da alheri da hani ga sharri
alhali ku na masu Imani!’
Saboda
haka wannan al’amari na umarni da alheri da hani ga sharri shi ne babban aiki
da aka dorawa wannan al’umma, kuma shi ne aikin da aka dorawa Annabawa da
Manzannin Allah da Salihai Managarta na gari a doron kasa. Wasu ma dai daga
cikin Malamai sun ce idan har an ce shika-shikan addinin Musulunci guda (5) ne,
to, Al’amru bil ma’ruf wal nahyi an-il munkar
shi ne na (6). Wannan duk saboda abin da ya kunsa na falala da gamammen alheri
da amfani da kuma maslaha na yanzu a Duniya da an-jima a Lahira. Yin watsi da
wannan aiki zai yada barna a ban kasa tare da sa duk wani abu na sabon Allah ya
bazu cikin al’umma. Kuma watsi da wannan aiki shi ne zai jawo fushin Allah SWT.
Kuma Allah Mai Girma yana gargadi da cewa a guji jawo fushin sa da kyamar sa da
azabar sa ta gaggawa!
Ya
ku ‘Yan uwa, wannan babban aiki ne Allah SWT ya daura mana na yin umarni da
alheri da hani da abin ki; su ne alamomin da ke nuna cewa lallai mun cika masu Imani
sannan kuma watsi da wannan aiki ke nuna cewa lallai ba da gaske mu ke ba; kuma
Munafukai ne mu! Allah Madaukaki yana fadi a cikin Al-Kur’ani cewa: Munafukai (Maza da Mata) sashen su majibacin
sashe ne; su na umarni da abin kwarai kuma su na hani da abin da Allah ba ya
so. A wata ayar kuma Allah yana cewa: Su
kuwa Mumunai (Maza da Mata) sashen su majibacin sashe ne; su na umarni da
alheri su na hani da mummuna. Wannan yana cikin Sauratul Taubah.
Allah
ya nuna mana halin kowane irin mutane inda su Munafukai so su ke yi a rika yin
aikin barna kuma idan an ce ayi daidai, sai su hana wannan! Su kuwa masu cewa
dole a hana barna kuma ayi alheri, su ne masu Imani! Saboda haka, Mumini, duk
inda ya ji an samu wani Mutumi wanda ya ke kokarin hana sharri tare da umarni
ga alheri, lallai ya samu ‘Dan uwa a matsayin sa da yake na mai Imani ba
Munafuki ba. Wani kuma a matsayin sa na sunan Musulmi sai yace don me za a hana
barna ayi kira ga alheri, wannan Munafuki ko da yayi ikirarin Musulunci bisa
nassin Al-Kur’ani!
Wadannan
al’amura su ne abubuwa mafi girma da su ka kawo nasara wajen abokan gaban Musulunci,
kuma su ne ke sa ayi nasara wajen shimfida tsari na Musulunci a doron Kasa.
Allah SWT yana cewa: …Wadanda idan mun ba
su iko a doron kasa, sai su rika tsaida Sallah su na bada zakkah, tare da umarni
ga alheri da hani ga mummuna…’ Wannan shi ne duk wani shiri na nasara kuma
shi ne jijiyar shayarwa na alheri a Duniya. Allah ya fada mana a cikin Al-Kur’ani
game da wanda su ka mance da abin da aka tunatar masu, Sai mu ka tseratar da wadanda su ke hani da sharri tare kira ga alheri.
Sannan kuma aka damke fasikai masu zalunci daga cikin su da azaba mafi tsanani!
Wadannan
abubuwa 2 watau Al’amru bil ma’ruf wal
nahyi an-il munkar, su ne mafi girman abubuwa da mutum zai yi bayan Imani. Wadannan
abubuwa su ne ke tabbatar da Imani. Haka kuma su ne ke manyan al’amurra da
farilla da wajibai kuma su ne mafi soyuwar aiki wurin mai Imani ga Allah. Ya zo
a cikin littafi cewa game da yin umarni da wadannan. Allah yace: Lalle, ya kasance a cikin ku akwai wasu
mutane da ke kira da alheri. Manzo SAW yana cewa: Alherin da za a kira; littafin Allah da sunna ta! Lallai ya kasance
a cikin ku akwai masu kira ga alheri su na umarni da shi.
Haka
kuma kamar yadda Imamu Musulmi ya rahoto daga Abu Saidu Al-Khuduri RA wanda
yace ya ji Manzon tsira SAW yana cewa: Duk
wanda ya ga wani abin sharri, yayi kokari ya canza wannan abu da hannun sa. Idan
mutum ba zai iya ba, yayi amfani da harshen sa. Idan kuma ba zai iya ba yayi
amfani da zuciyar sa ta hanyar jin zafi da takaicin wannan barna (wanda wannan
ne mafi raunin Imani.). A wata ruwayar kuwa an ce idan ya zama baya ga
wannan (watau na karshen) babu daidai da kwayar gadagi na Imani ga wannan
mutumi. Ta ya Allah SWT zai ce ba ya son abu a mallakar sa (na rashin gaskiya
da cuta da ha’inci ko yaudara) sannan kuma wasu su ce dole sai an yi barnar,
kuma a zura masu idanu, ina imanin yake?
Haka
nan kuma Imam Tirmidhi ya ruwaito daga Huzaifa ‘Dan Yamani RA wanda yace Manzon
Allah SAW yana cewa: Na rantse da wanda
rai na yake hannun sa, ku rika umarni da alheri. Kuma Wallahi, ku rika hani
daga sharri ko kuwa Allah yana daf da ya aiko masu azabar sa. Ka na kuma ku
rika rokon Allah sannan a ki karba. Yace: ku kuma hannun azzalumi dole sai yayi gaskiya ku tankwara sa, ko kuwa
Allah ya buga tsakanin zukatan ku! Bayan nan kuma sai Allah mai girma ya tsine
maku kamar yadda ya tsinewa Ahlul-Kitab.
Ya
ku wadanda Allah yayi wa kirari, wadanda aka fitar domin aikin umarni da alheri
da hani ga sharri. Ku sani cewa wannan aiki ba abu bane da aka ayyana ga wata
kungiya ko wani mutum, abu ne da yake kan dukkanin Musulmi gwargwadon iyawar sa
na matsayin sa da mukamin sa. Sai dai akwai mutane (irin Malamai, da
Shugabanni) da nauyin Jama’a ya rataya kan su da aka daura masu nauyi na
musamman na wannan aiki. Uba a Ranar kiyama zai zama abin tambaya game da
iyalin sa. Malami kuma za a tambaya sa game da ilmin sa. Haka za a tambayi Ma’aikaci
game da wurin aikin sa. Attajiri kuma za a tambaye sa game da dukiyar sa. Duk
dai wanda Allah SWT ya ba kiwo, za a tambaye sa abin kiwon na sa.
Ai
shi Musulmi na gaskiya ko a ina yake zai zama bai da wani aiki sai umarni da
alheri da hani kan abin ki. Ta ya za ace ana barna a cikin kasa amma da zarar
an kama maras gaskiya sai ka ji Musulmi ne? Kuma mu na kirari cewa mu na cikin
mafifitan al’umma! Ta ya za a ce don mutum bai samu abin da yake so ba, sai ya
kawo barna yana bata komai? Ya kamata Musulmai su hada-kai wajen umarni da
aiwatar da dokar Allah tare da hani wajen aikin barna. Wannan ne zai tabbatar
da yada alheri a wannan kasa ya kuma tunkude sharri. A wannan kasar dai babu
lokacin da mu ke bukatar wannan aiki kamar wannan lokaci kuma dole mu kara
gwagwarmaya wajen tabbatar da wannan ka’ida saboda alheri ya game kasar mu da
sauran kasashen Musulmi har ya zama an yi dabaibayi wajen buge kan barna da
sharri.
Allah ka ba mu fahimtar Addini
ya
sa ya amfane mu gaba daya. Allah ya bamu
fahimtar sunnar Annabin mu Muhammad SAW. Allah kayi dadin tsira da Annabi SAW da Iyalan Sa
da Sahaban Sa musamman Khalifofin Sa shiryayyu.
Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba ta
10-11-2017 daga Masallacin I.T.N-Zaria.
Twitter: @Ya_waliyyi
No comments:
Post a Comment