Saturday, November 18, 2017

Hudubar Juma’a game da Malaman Makaranta





Hudubar Juma’a daga Mimbarin ITN-Zaria

 

‘Hudubar Juma’a game da harkar Ilmi a ban kasa da Jihar Kaduna -Daga Bakin Imam Ustaz Sa’eed Yunus.

 

 

Assalamu Alaikum wa Rahmatul Lah, 

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah SWT, tsira da amincin Allah su tabbata ga wanda babu Annabi bayan sa, Shugaban mu, kuma Annabin mu, farin Jakadar Allah; Annabi Muhammadu SAW, tare da iyalan sa da Sahaban sa tare da duk wadanda suka bisa da kyautatawa zuwa har Ranar karshe.
Bayan haka, mu sani cewa mu na cikin wani lokaci da mu ka shiga cikin wani hali a ban kasa. Babu abin da ya jawo wannan sai rashin karatu da neman ilmi. 

Ilmin da ya kamata a maida hankali a kai sun hada da: Na farko, dole a komawa Al-Kur’ani, ayi aiki da shi ana tadabburi kuma tare da haddacewa kamar yadda Allah ya fada. Sannan kuma ilmin fassara Al-Kur’ani watau Hadisan Manzon Allah SAW. Sannan kuma ilmi na Akida wanda ke fitar da mutum daga sharrin shirka. Sannan kuma da ilmin nan na Fikihu. ‘Yan uwa masu girma ilmi yana da yawa; daga ciki har da ilmi na harshen larabci wanda za ayi magana da shi a gobe kiyama gaban Allah SWT. Da yaren larabci aka saukar da Al-Kur’ani. Daga cikin ilmin da ya kamata a ba muhimmanci akwai ilmin kimiyya, tattali da kuma shari’a da kuma ilmi na koyan Malanta. Duk wani ilmi ya kamata ace an samu Musulmi a wannan wuri. Daga cikin ilmi masu amfani kuma akwai ilmi na aikin Soja wanda za a juya duk wani makami wanda za a kare addini kamar yadda Al-Kur’ani yake cewa ku yi tanadi na kare kai! Ana bukatar masu tare wurare na harba bam domin kare addini a kuma kare kasa da manyan kasa. Yanzu wadannan mabarnata masu garkuwa da mutane a kasa, ya kamata ace an samu ilmin da zai kawo karshen su. 

Huduba tana kuma kira gare ku da a samu ikhlasi watau tsarkin niyya. Idan aka ce kai Injiniya ne, to ka zama Musulmin Injiniya, ko kuma ace kai Musulmi ne kuma Likita ko kuma Soja ko Malamin Makaranta ko kuma Makanike ko mai aiki a Kamfani amma Musulmi. Kuma don Allah duk wadanda za su rubuta wani abu da Dalibai su ke amfani da shi su ji tsoron Allah. Wallahi idan har ka sa abin da kuma zai bata tarbiyyar yara za kayi bayani a Ranar tashin kiyama ka gane kuren ka. Ku san irin Makarantun Bokon da za ku sa yaran ku; wasu iyayen su na jefa yaran su cikin tabo sannan kuma su na cewa ka da yaran su jike, wannan hauka ne! Sai ka ga mutum ya dauki diyar sa ya kai wurin wadanda ba Musulmi ba. Saboda haka yana da kyau mu gyara don kuwa za a tambaye ku a gobe kiyama. 

Sannan kuma Malaman Makaranta ku ji tsoron Allah don ku na da hakki da kuma abin da za su ku fada. Hudubar yau tana jinjinawa Malamai, ina gaishe ku Malaman Makaranta. Malaman Makarantar Gwamnati ba wanda yake koyarwa a Makarantun kasuwa ba. Ni ina ce maku ‘Salamu Alaikum’ don kun cancanci gaisuwa, ku ne Malamai na gaskiya kuma na san aikin da ku ke yi. Kun cancanci a ba ku tukwuici a duk matakin da ku ke na firamare ko sakandare balle ma kuma Jami’a uwa-uba.

Amma kuma abin bakin ciki sai aka samu irin wannan tafiyar a yau ta tabarbare. An samu wasu da su ka je su ka koyi karatu daga kwaleji ko FCE kuma su ke karantarwa da kyau. Wasu kuma sun shiga hakkin yara; ba a shiga aji ba kuma a kula da yara. Malamai ku ji tsoron Allah, wannan abin shi ya jawo bala’in da aka shiga a Jihar Kaduna, Allah kadai ne zai yi hukunci gobe a kiyama, wannan abun bakin ciki ne. Allah shi kadai ne mai cikar kamala don babu wanda za ayi wa jarrabawa a ce sai ya ci dari-bisa-dari, amma kun ci amanar kasar ku gaba daya. A makarantun na fa kitso ake yi da sayar da atamfa, kungiyoyi su yi ta kawo tallace-tallace. Sai yara su tafi Makaranta amma ba ayi masu komai ba! Shekara nawa aka yi ana wannan abu? Wallahi ya fi shekaru 30 ana haka! Wadanda su ka sani sun sani, wadanda ba su sani ba, sun jahilta. Wannan itace al’adar Malamai (ba na Jihar Kaduna ba kurum). Idan aka ce a Kaduna kadai ake wannan an zalunci Malaman Jihar, kusan kaf Najeriya ta Arewa shekaru 30 da su ka wuce Malamai kan yi wasa da aikin su. Sannan kuma aka samu Gwamnoni da su ka rika daukar mutanen da su ka cancanta da wadanda ba su cancanta ba, an maida karantawar kamar bola. Lokaci ya kai ana kawo wadanda ba Malamai ba amma su na koyarwa ba tare da sun san komai ba su na karanatar da yara!

‘Yan uwa ku ba ni labarin wadanda aka kama bayan shigowar Gwamnatin Shugaba Buhari su na da ‘ya ‘ya a gida amma ana ba su albashi. Sai ka ga mutum da matan sa 4 da ‘ya ‘ya 24 amma kowane yana samun albashi a karshen wata. Tsakani ga Allah ba canji ku ka nema ba? Kun nemi canji sai Allah ya kawo maku, sai kuma ku ce ba ku yarda ba? Ka na bakin ciki don an kama ‘Dan uwan ka da laifi ba ya shiga aji? ‘Dan uwan ka ya ci amanar hukuma, ba gara ya zama an kama sa tun a Duniya ba a kafin ya isa lahira ya ji kunya? Saboda haka ku ji tsoron Allah, abin da baki ya fada zai iske shi a gobe kiyama. 

Annabawan Allah sun yi gwagwarmya; Annabi Musa AS yayi fama da Fir’auna; Bani Israila sun kai kuka cewa ana kashe su har Allah ya kashe Fir’auna, sai ga shi wadannan mutane sun kuma nemi a kera masu gunki. Annabi Musa AS yace wadannan mutane ba su fahimci abubuwa ba. Ko su ku ke mu ma ayi shekara 40 ana yi mana azaba? Annabi Muhammad SAW ma dai bai kubuta ba don har ta kai Sahaban sa sun nemi Allah ya kawo yaki yayin da aka umarce su da su yi ta sallah. Sai ga shi a lokacin da aka hukunta yaki su na jin tsoro su na cewa meyasa aka ce su fita yaki. Jama’a ku kuce ‘Mai Rusau, Mai Rusau!’Ga shi kuma ya zo ya rusa kuma yana ta rusawa kuma kun ce ba ku yarda ba! Ku na so ku shekara 40 kenan a wulakance? Wallahi ba kamfe bane! Wallahi ba kamfe bane! Wallahi ba kamfe bane! Gaskiya ce dole kuma a fada! 

Ko kun ki ko kun so wanda ya gama Gwamna abin yabo ne amma ku ka zage sa, ga shi kuma Allah ya kawo wannan. Abin bakin ciki shi ne a kan Musulmi duk tsinuwar ta ke karewa; Musulmi ke zagin ‘Dan uwan sa. A karatun da Malam yayi, yake cewa idan tsinuwar ba ta hau kan sa ba za ta hau kan ku kuma sai ta tafarfasa ku. Shiyasa mu na nan mun kasa cigaba har yanzu. Al-Kur’ani ya fada mana cewa; Allah ya kama Fir’auna da Hamana da duk masu laifi. ‘Yan uwan ku kiyaye wannan kamun na Allah. 

Huduba tana rokon Allah ya azurta mu da ilmi mai amfani. Ina neman gafara gare ku ‘Yan uwa. Sannan bayan godiya ga Allah huduba tana cewa Jama’a ku ji tsoron Allah, ku kiyayi ha’inci na jarrabawa da ake yi, ku kiyayi kai yara Makarantun da ake kira Miracle Centres da ake cin jarrabawa, karya ne munafunci ne. Yaran Musulmai su ka cika wadannan Makarantu alhali su su na Makarantun Gwamnati. Makarantun nan na Gwamnati su ne Makarantun asali, lalata su aka yi. Sai ace wai Shugabanni sun ki kai yaran su Makarantun Gwamnati, ku ina ku kai na ku yaran? Ka yarda cewa diyar ka ta je Makaranta da hijabi na Sunnah amma daga ta isa bakin Makaranta sai ace ta tube? Mun dauki amanar yaran mu, mun kai wurin wadanda ba mu ba! Wannan fa shi ne yake ba ta tarbiyya, wanda bai da abu ba zai ba da shi ba. 

Ku Malamai na Jihar Kaduna ku gyara al’amarin ku, ku ji tsoron Allah. Wasu ne su ka jawo maku wannan bala’i, ba laifin ku ba ne duka Wallahi! Idan ka shiga Jami’ar Ahmadu Bello za ka ji ba za ka iya kwashe ‘Daliban da su kayi jarrabawar kwanan nan ba. Kuma ku duba Daliban da aka fitar zuwa Kasar Uganda domin karatun likitanci amma an dawo da su, meya faru? Duk wadannan mugayen Makarantu su kayi. Amma kun tambayi tarihi mana. 

Don haka ina kira ga Hukuma ta ilmi da duk wani mai ta cewa, ni dai na fadi nawa a matsayi na ‘Dan uwan ku Musulmi; Malaman nan da aka kora a duba al’amarin su, ya ku Gwamnati, ka da ku kori Malamai. Amma duk wanda ya kasance ba Malami bane, ba na goyon bayan a cigaba da tafiya da shi. Ina kira ga Gwamnati don Allah a ba su hakkin su. Malaman nan fa Malamai ne ba za a hada su da wadannan yara ba da ake shirin dauka Wallahi! Ku yi hakuri, da tsohuwar zuma ake magani. A gyara su ne kawai. 

Ku kuma Malamai ku iya bakin ku, ku tuna da Hadisin Manzon Allah da ya ga wasu ana yanka bakunan su da lauje a kabari, da Manzon Allah ya tambaya a kan su sai aka fada masa cewa su ne masu fadar abin da ba su sani ba. Kun zagi wancan Gwamnan, kun zagi Gwamnan da ya wuce, wanda ya wuce ya zama Sanata kun tsine masa, gobe kiyama sai ka fadi abin da Gwamna yayi maka! Tsoho Baba Buhari wadansu har sun fara zagin sa, shi ma ma sai ka fadi abin da yayi maka a gobe kiyama. Ka kiyayi bakin ka Musulmi don duk baki ya jawo mana wannan. 

Mu tambayi tarihin su Sardauna da su Tafawa-Balewa wadanda su ka jawowa kasa izza amma yanzu an jawo mana zilla. Idan ba mu bane da mulkin kasar nan sai ka ji bakin Jama’a shiru, amma daga na mu ya samu sai ka ji ana ta ‘Allah ya tsine.’ Ka sani babu abin da za ka samu saboda wani Gwamna ko yanayi. Matsalar tamu ce mu kan mu, kuma sai an tambaye mu a kiyama.

Huduba tana cewa lallai ku kiyayi ka-ce-na-ce watau kila-wa-kala, ku kiyayi mugun zato ga Musulmi. A kuma daina zagin Shugabanni, a daina tsinewa Malamai, kiyayi zunubi da sabon Allah wanda shi ya jawo mana wannan bala’i. Yau ba mu da Soja mai gaskiya; barikin nan na Zariya an koro yaran mu sama da 800 don ba su da takardun shaida. Meya faru? Sun je Miracle Centers domin jarrabawa. Ga su nan a Jami’a kuma; a dalilin rashin Jarrabawar nan na Post UTME yanzu an yi jarrabawar aji daya duk sun fadi saboda ba a tace ba, su ma sun je Miracle Centers.

 Iyaye ku ji tsoron Allah ku samawa yaran ku Makarantu na gaskiya. Lauyoyin mu, ku zama masu fadar gaskiya. Likitocin mu ku ji tsoron Allah, ilmin ku yayi amfani. Ya kai mai neman Shugabanci ka ji tsoron Allah. Ka sani cewa kabari na nan yana jira. Ya kai wawa wanda ka rafkana, ka dauki Duniya wajen zama, ya kai Saurayi da ka ke ganin za ka dade, Ya kai Shugaba da ka ke danne hakkin Jama’a, ya kai da ake shugabanta da ka ke zagin Shugabanni, duk ku sani cewa akwai tsayuwa gaban Allah kuma akwai kabari. Wallahi kabari sama turbaya ne kasan sa babu wanda ya sani sai Allah! Yau ga shi ka mutu kai ne mai surutu a wata Majalisa. 

Allah ya hada mu cikin masu son gaskiya da riko da gaskiya da aiki da gaskiya. Allah ya sa kabari wajen hutawar mu ne. Allah ka sa mu karbi littafin mu da hannun dama. Allah ka taimaki Shugabannin mu na kirki, wadanda ba za su gyaru ba ka canza mana su. Allah ka biyawa kowa bukatan sa mazan mu da matan mu!

[Akwai wasu sashe na hudubar Malam da su ka shafe daga na’ura]

Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga Masallacin I.T.N-Zaria. Muhammadmalumfashi@gmail.com           Twitter:@Ya_waliyyi

Saturday, November 11, 2017

HUDUBAR JUMA’A DAGA ITN





HUDUBAR JUMA’A DAGA MIMBARIN ITN-ZARIA

HANI DA ABIN KI DA KUMA KIRA GA ABIN ALHERI A ADDINI DAGA BAKIN IMAM SHEIKH S. S ABUBAKAR



A’udhu BilLahi minasshaidan Ar-Rajim, BismilLahir Rahman Ar-Raheem,

Bayan godiya ga Allah SWT!
Allah Madaukaki ya sa wannan al’umma ta zama mafificiyar al’umma; ita ce al’ummar da ta ke umarni da alheri kuma ta ke hari game da abin ki da shari’a ta hana. Mu na godiya ga Allah SWT bisa ga abubuwa da dama na ni’ima, mu na kuma shaidawa cewa babu abin bauta da gaskiya sai Allah Mai Girma; shi kadai yake, babu abokin tarayya. Allah Ya wajabta ayyuka na alheri da abubuwan da za su kai ga rabota kuma Shi ne yayi kira a samu masu umarni da alheri da hani ga mummuna. 

Muna shaidawa lallai Shugaban mu, Annabi Muhammad SAW, Bawan Allah ne kuma Manzon Sa ne. Shi ne wanda yake rike da tutar kira ga Allah da kuma jihadi wajen daukaka Kalmar Allah da kuma gwagwarmaya wajen gyara a kasa. Saboda haka, shi ya shiryar da Sahaban S\a bisa tafarkin da ya dora su akai. 

Bayan haka ‘Yan uwa, Imani ga Allah da bin tafarkin gaskiya da kuma yin nasiha da Allah da Manzon sa da littafin sa da kuma tsakanin junan mu da kuma yin nasiha ga junan mu na taimakekeniya da hakuri wajen aikin gaskiya tare da kuma cewa mu ne masu yada abubuwa na alheri da falala sannan da yaki da sharri da duk wani abu na kasakanci a doron Kasa da tunbuke abubuwa na sharri a al’umma. Duk wannan su na cikin alamu mafi bayyana na al’ummar Annabi Muhammad SAW. Ta hanyar wadannan ayyuka ne wanan al’umma ta kerewa sauran al’ummai kamar yadda Allah SWT ya fada cikin Al-Kur’ani cewa: ‘Ku kun tabbata mafificiyar al’umma… ku na masu umarni da alheri da hani ga sharri alhali ku na masu Imani!’ 

Saboda haka wannan al’amari na umarni da alheri da hani ga sharri shi ne babban aiki da aka dorawa wannan al’umma, kuma shi ne aikin da aka dorawa Annabawa da Manzannin Allah da Salihai Managarta na gari a doron kasa. Wasu ma dai daga cikin Malamai sun ce idan har an ce shika-shikan addinin Musulunci guda (5) ne, to, Al’amru bil ma’ruf wal nahyi an-il munkar shi ne na (6). Wannan duk saboda abin da ya kunsa na falala da gamammen alheri da amfani da kuma maslaha na yanzu a Duniya da an-jima a Lahira. Yin watsi da wannan aiki zai yada barna a ban kasa tare da sa duk wani abu na sabon Allah ya bazu cikin al’umma. Kuma watsi da wannan aiki shi ne zai jawo fushin Allah SWT. Kuma Allah Mai Girma yana gargadi da cewa a guji jawo fushin sa da kyamar sa da azabar sa ta gaggawa! 

Ya ku ‘Yan uwa, wannan babban aiki ne Allah SWT ya daura mana na yin umarni da alheri da hani da abin ki; su ne alamomin da ke nuna cewa lallai mun cika masu Imani sannan kuma watsi da wannan aiki ke nuna cewa lallai ba da gaske mu ke ba; kuma Munafukai ne mu! Allah Madaukaki yana fadi a cikin Al-Kur’ani cewa: Munafukai (Maza da Mata) sashen su majibacin sashe ne; su na umarni da abin kwarai kuma su na hani da abin da Allah ba ya so. A wata ayar kuma Allah yana cewa: Su kuwa Mumunai (Maza da Mata) sashen su majibacin sashe ne; su na umarni da alheri su na hani da mummuna. Wannan yana cikin Sauratul Taubah.

Allah ya nuna mana halin kowane irin mutane inda su Munafukai so su ke yi a rika yin aikin barna kuma idan an ce ayi daidai, sai su hana wannan! Su kuwa masu cewa dole a hana barna kuma ayi alheri, su ne masu Imani! Saboda haka, Mumini, duk inda ya ji an samu wani Mutumi wanda ya ke kokarin hana sharri tare da umarni ga alheri, lallai ya samu ‘Dan uwa a matsayin sa da yake na mai Imani ba Munafuki ba. Wani kuma a matsayin sa na sunan Musulmi sai yace don me za a hana barna ayi kira ga alheri, wannan Munafuki ko da yayi ikirarin Musulunci bisa nassin Al-Kur’ani! 

Wadannan al’amura su ne abubuwa mafi girma da su ka kawo nasara wajen abokan gaban Musulunci, kuma su ne ke sa ayi nasara wajen shimfida tsari na Musulunci a doron Kasa. Allah SWT yana cewa: …Wadanda idan mun ba su iko a doron kasa, sai su rika tsaida Sallah su na bada zakkah, tare da umarni ga alheri da hani ga mummuna…’ Wannan shi ne duk wani shiri na nasara kuma shi ne jijiyar shayarwa na alheri a Duniya. Allah ya fada mana a cikin Al-Kur’ani game da wanda su ka mance da abin da aka tunatar masu, Sai mu ka tseratar da wadanda su ke hani da sharri tare kira ga alheri. Sannan kuma aka damke fasikai masu zalunci daga cikin su da azaba mafi tsanani! 

Wadannan abubuwa 2 watau Al’amru bil ma’ruf wal nahyi an-il munkar, su ne mafi girman abubuwa da mutum zai yi bayan Imani. Wadannan abubuwa su ne ke tabbatar da Imani. Haka kuma su ne ke manyan al’amurra da farilla da wajibai kuma su ne mafi soyuwar aiki wurin mai Imani ga Allah. Ya zo a cikin littafi cewa game da yin umarni da wadannan. Allah yace: Lalle, ya kasance a cikin ku akwai wasu mutane da ke kira da alheri. Manzo SAW yana cewa: Alherin da za a kira; littafin Allah da sunna ta! Lallai ya kasance a cikin ku akwai masu kira ga alheri su na umarni da shi. 

Haka kuma kamar yadda Imamu Musulmi ya rahoto daga Abu Saidu Al-Khuduri RA wanda yace ya ji Manzon tsira SAW yana cewa: Duk wanda ya ga wani abin sharri, yayi kokari ya canza wannan abu da hannun sa. Idan mutum ba zai iya ba, yayi amfani da harshen sa. Idan kuma ba zai iya ba yayi amfani da zuciyar sa ta hanyar jin zafi da takaicin wannan barna (wanda wannan ne mafi raunin Imani.). A wata ruwayar kuwa an ce idan ya zama baya ga wannan (watau na karshen) babu daidai da kwayar gadagi na Imani ga wannan mutumi. Ta ya Allah SWT zai ce ba ya son abu a mallakar sa (na rashin gaskiya da cuta da ha’inci ko yaudara) sannan kuma wasu su ce dole sai an yi barnar, kuma a zura masu idanu, ina imanin yake? 

Haka nan kuma Imam Tirmidhi ya ruwaito daga Huzaifa ‘Dan Yamani RA wanda yace Manzon Allah SAW yana cewa: Na rantse da wanda rai na yake hannun sa, ku rika umarni da alheri. Kuma Wallahi, ku rika hani daga sharri ko kuwa Allah yana daf da ya aiko masu azabar sa. Ka na kuma ku rika rokon Allah sannan a ki karba. Yace: ku kuma hannun azzalumi dole sai yayi gaskiya ku tankwara sa, ko kuwa Allah ya buga tsakanin zukatan ku! Bayan nan kuma sai Allah mai girma ya tsine maku kamar yadda ya tsinewa Ahlul-Kitab. 

Ya ku wadanda Allah yayi wa kirari, wadanda aka fitar domin aikin umarni da alheri da hani ga sharri. Ku sani cewa wannan aiki ba abu bane da aka ayyana ga wata kungiya ko wani mutum, abu ne da yake kan dukkanin Musulmi gwargwadon iyawar sa na matsayin sa da mukamin sa. Sai dai akwai mutane (irin Malamai, da Shugabanni) da nauyin Jama’a ya rataya kan su da aka daura masu nauyi na musamman na wannan aiki. Uba a Ranar kiyama zai zama abin tambaya game da iyalin sa. Malami kuma za a tambaya sa game da ilmin sa. Haka za a tambayi Ma’aikaci game da wurin aikin sa. Attajiri kuma za a tambaye sa game da dukiyar sa. Duk dai wanda Allah SWT ya ba kiwo, za a tambaye sa abin kiwon na sa. 

Ai shi Musulmi na gaskiya ko a ina yake zai zama bai da wani aiki sai umarni da alheri da hani kan abin ki. Ta ya za ace ana barna a cikin kasa amma da zarar an kama maras gaskiya sai ka ji Musulmi ne? Kuma mu na kirari cewa mu na cikin mafifitan al’umma! Ta ya za a ce don mutum bai samu abin da yake so ba, sai ya kawo barna yana bata komai? Ya kamata Musulmai su hada-kai wajen umarni da aiwatar da dokar Allah tare da hani wajen aikin barna. Wannan ne zai tabbatar da yada alheri a wannan kasa ya kuma tunkude sharri. A wannan kasar dai babu lokacin da mu ke bukatar wannan aiki kamar wannan lokaci kuma dole mu kara gwagwarmaya wajen tabbatar da wannan ka’ida saboda alheri ya game kasar mu da sauran kasashen Musulmi har ya zama an yi dabaibayi wajen buge kan barna da sharri.

Allah ka ba mu fahimtar Addini ya sa ya amfane mu gaba daya. Allah ya bamu fahimtar sunnar Annabin mu Muhammad SAW. Allah kayi dadin tsira da Annabi SAW da Iyalan Sa da Sahaban Sa musamman Khalifofin Sa shiryayyu.



Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba ta 10-11-2017 daga Masallacin I.T.N-Zaria.
Muhammadmalumfashi@gmail.com          
Twitter: @Ya_waliyyi

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...