Tun
da Gwamnatin Buhari ta kafu ba a taba nema na ba Inji Atiku
- Atiku yace yayi mamakin yadda Boko Haram ta gagara
- Babban Dan Siyasar yace Jam'iyyar tayi sakaci a mulki
- Haka kuma yace akwai gibi wajen yaki da cin hanci
Tsohon Mataimakin
Shugaban kasa Atiku Abubakar yayi kaca-kaca da Gwamnati mai mulki a wata hira
da yayi da Gidan VOA na Amurka.
Alhaji Atiku Abubakar wanda
yana cikin Jam'iyyar APC mai mulki yace tun da aka kafa Gwamnati bai kara cewa
komai ko aka nemi ta shi ba. Haka kuma Atiku yace tun lokacin har yau Jam'iyyar
APC ba ta kira taro domin a zauna ba sai sau daya tak.
Atiku ya kara da cewa har yanzu akwai sauran 'Yan Boko Haram a Arewa maso
Yammacin kasar kuma yayi mamaki ace an gaza kawo karshen su. Yace ko
maganar yaki da sata da sauran aiki har gobe don kuwa babu wani barawo da aka
kama da kudi ba kamar lokacin da su kayi muki ba a 1999.
Jiya
mu ka ji wani daga cikin magoya bayan tsohon Mataimakin Shugaban kasar nan
Abdullahi Sugar yace Obasanjo na neman tsaida El-rufai ko Kwankwaso ne a
matsayin Shugaban kasa a zabe 2019. Haka kuma an ga daya daga cikin Ministocin kasar ta soma yi masa kamfe.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment