Saturday, September 9, 2017

Za a binciki matar wani tsohon Shugaban kasa

Za a jefa mai dakin tsohon Shugaban kasa a gidan yari saboda cin dukiyar Gwamnati



Ana binciken matar tsohon Shugaban kasar Israila da laifi

Gwamnati na zargin Sara Netanyahu da laifin cin kudin kasa

An dai taso tsohon Shugaba Benjamin Netanyahu a gaba




Da rabon a maka wata matar tsohon Shugaban kasar Israila a gidan yari saboda cin dukiyar Gwamnatia shekarun baya.

Alkalin Alkalai na Kasar Israila yace za a maka Matar Tsohon Shugaba Sara Netanyahu a Kotu saboda zargin cinye wasu kudin Gwamnati $10,000 lokacin mai gidan ta na mulki. Wasu zargin dai sun hada da amfani da kudin Gwamnati wajen gyara wutan gidan da ke Garin Caesarea.

Ana kuma zargin matar sa tsohon Shugaban kasar da wata badakala wajen harkar abinci a lokacin ta na zaune a Fadar Shugaban kasa. Ko da dai ana ganin laifin kamar ba wani laifi ba da alamu dai an taso tsohon Shugaba Benjamin Netanyahu da iyalan sa ne kurum a gaba.



[NAIJ Hausa]

Friday, September 8, 2017

Wani ya auri bera bayan mutuwar matar sa

Wani mutumi ya auri bera a Kasar India

 



A Kasar India wani ya auri bera bayan mutuwar matar sa

Mista Basu yana ganin matar sa ce ta dawo a jikin bera

Bawan Allan ya rasa matar sa ne a hadarin mota kwanaki




Mun samu labari na musamman cewa wani ya auri bera bayan mutuwar matar sa a can kasar India a Watan Junairu.

Wani mutumi mai suna Chidhatma Basu ya auri macen bera a Garin Bangalore na Kasar India bayan mai dakin sa ta rasu a farkon shekarar nan a wani hadarin mota. Mutuwar ta sa wannan mutumi mai shekaru 41 da 'ya 'ya 4 ya zama gwauro.

Mista Basu yace wata rana yana zaune cikin takaici da maraici sai ga shi ya ga wata bera mai idanuwa da hanci sak na marigayiyar matar sa. Mutumin yace ya fahimci cewa matar sa ce kurum ta dawo daga irin abincin da take ci. Malamin da ya daura auren yace tabbas haka aka yi.




[NAIJ Hausa]

Thursday, September 7, 2017

Za a daure 'Dan tsohon Shugaban kasa a kurkuku



Yaron wani tsohon Shugaban kasa zai yi shekaru 24 a gidan yari



Za a maka yaron tsohon Shugaban wata kasa a cikin gidan yari

'Dan tsohon Shugaban kasar Honduras zai yi shekaru 24 a tsare


An same shi da laifin safarar miyagun kwayoyi na hodar iblis




Mun samu labari cewa yaron wani tsohon Shugaban kasar Honduras zai shafe shekara da shekaru a gidan maza.

An samu Fabio Lobo 'dan gidan tsohon shugaban kasar Honduras Porfirio Lobo da laifin safarar miyagun kwayoyi inda yake kokarin saidawa a kasar Amurka. An yi caraf da shi yanzu haka kuma an yanke masa daurin shekaru 24 a kurkuku. 

Alkalin ya yanke masa hukunci mai tsauri inda yace Lobo yayi kokarin amfani da damar sa ta tsohon Dan shugaban kasa wajen shigo da kwayoyin hodar iblis. Shi dai tsohon Shugaba Lobo bai tsaya kokarin kare 'Dan na sa ba yace ta shi ga fice sa.




[NAIJ Hausa]

Wednesday, September 6, 2017

Atiku yayi kaca-kaca da Gwamnatin Buhari


Tun da Gwamnatin Buhari ta kafu ba a taba nema na ba Inji Atiku

  • Atiku yace yayi mamakin yadda Boko Haram ta gagara
  • Babban Dan Siyasar yace Jam'iyyar tayi sakaci a mulki
  • Haka kuma yace akwai gibi wajen yaki da cin hanci


Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar yayi kaca-kaca da Gwamnati mai mulki a wata hira da yayi da Gidan VOA na Amurka.

Alhaji Atiku Abubakar wanda yana cikin Jam'iyyar APC mai mulki yace tun da aka kafa Gwamnati bai kara cewa komai ko aka nemi ta shi ba. Haka kuma Atiku yace tun lokacin har yau Jam'iyyar APC ba ta kira taro domin a zauna ba sai sau daya tak.

Atiku ya kara da cewa har yanzu akwai sauran 'Yan Boko Haram a Arewa maso Yammacin kasar kuma yayi mamaki ace an gaza kawo karshen su. Yace ko maganar yaki da sata da sauran aiki har gobe don kuwa babu wani barawo da aka kama da kudi ba kamar lokacin da su kayi muki ba a 1999.

Jiya mu ka ji wani daga cikin magoya bayan tsohon Mataimakin Shugaban kasar nan Abdullahi Sugar yace Obasanjo na neman tsaida El-rufai ko Kwankwaso ne a matsayin Shugaban kasa a zabe 2019. Haka kuma an ga daya daga cikin Ministocin kasar ta soma yi masa kamfe.  




[NAIJ Hausa]

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...