Nadin Gwamnan rikon kwarya a CBN
Dauko Adebisi Shonubi a matsayin Gwamnan rikon kwarya ya na da alamar tambaya – ba wai saboda asalinsa Injiniya ba ne. Ya kamata mutane su san tun shekaru kusan 40 da suka wuce ya yi watsi da Injiniyanci, ya yi digirgi a MBA kuma ya kware a fannin tattalin arziki.
Bankin CBN Hoto: thewhistler.ng
Kafin zuwansa CBN tun 2018, Adebisi ya yi aiki da manyan bankuna irinsu Citibanki Ecobank, Union, FCMB. Bayan manyan mukamai da ya rike a bankuna, sai da ta kai ya shugabanci bankin NIBBS na kasa. Saboda haka ba abin mamaki ba ne Injiniya ya saki layi zuwa banki.
Inda gizo ke sakar. Akwai mataimakan Gwamnoni 4 a CBN – Edward Adamu, Aisha Ahmed da Kingsley Obioro. Kusan duka wadannan sun riga Adebisi zuwa babban banki, su na gaban shi. Don haka za ayi zargin cewa ya samu kujerar ne saboda shi kadai ne Bayarabe a cikinsu.
A lokacin da Goodluck Jonathan ya dakatar da Sanusi Lamido, sai ya umarci Dr. Sarah Alade ta zama gwamnan riko domin ta dade a bankin (ina tunanin tun 2004 ta zo). Dr. Alade kwararriyar ma’aikaciyar banki ce kuma asalin ta mutumiyar Arewa maso tsakiyar Najeriya ce.
Wata matsala kuma ita ce, a shari’ar Sanusi v Gwamnatin tarayya, kotu ta ce shugaban kasa zai iya dakatar da gwamnan babban banki amma bai isa ya yi nadi (ko da na rikon kwarya) ba, sai da yardar ‘yan majalisa. Yanzu SGF ya ce Adebisi ya fara aiki, alhali ba a rantsar da majalisa ba.