Kwankwaso da jam'iyya mai kayan marmari a Najeriya
Kusan shi
fa Kwankwaso ya san samun mulki a 2023 zai yi masa wahala. Duk da dai
magoya bayansa akwai 'dan-karen karfin hali. A irin gogewa da yawan mabiyan da yake
da su, matsayin da aka ba shi a APC ne ya yi masa kadan, da ya je PDP
sai ya iske su ma duk ba su da niyyar gwabzawa da APC da kyau, sun sa
son rai kuma sun raina karfin APC da na Kwankwaso. PDP sun kama wasu
tarkace saboda su na da baitul mali, abin da Kwankwaso bai da shi, a
sakamakon murde zaben Kano a 2019. Murdewa Abba Gida Gida zabe ya jawowa
Kwankwasiyya cikas na gaske; ya rabawa Kwankwaso hankali, ya tilasta
shi shiga siyasar gida, ga kalubale na rashin mulki.
Idan
har ba sha'awar zama dan kallo yake yi ba, zaman Kwankwaso a PDP a irin
wannan yanayi ba ta da amfani. A nan kusa, ba zai samu takara ba, ba
zai amfana da komai ba, sai dai su amfana da shi. Bayan gwamna,
Kwankwaso ya rike duk wata babbar kujera ta tarayya, burinsa daya ne a
Duniya. Daga nan har zuwa bayan 2023, Kwankwasiyya ba ta cikin lissafin
PDP face nemawa PDP kuri'un Yan Arewa a Kudu. Hakan ta sa yake neman
inda zai fito da kan shi. Kuskure ne a siyasa ka ce wai a zauna ayi
hakuri, 'dan siyasa kullum cikin lissafin zabe na gaba yake yi, ga
shekaru su na tafiya. Kamar dai a 2018, yanzu ma lokaci ya na neman ya
kure.
Kafa
sabuwar jamiyya ta na da wahalar gaske. Wasu sun jarraba a baya, suka
yi asarar makudan kudi, kuma ba a dace ba. Ina ragowar mafita? A hade da wata
karamar jam'iyya kamar su PRP da masu kayan marmari. Hakan ta sa Madugun
Kwankwasiyya ya burma cikin NNPP. Inda matsalar ta ke ita ce a gida
watau Kano. Wasu Kwankwasawa sun ajiye mukamansu a APC, sun bi Kwankwaso
zuwa PDP a zaben 2019, suka yi biyu-babu. Su na tsoron sake tsalle zuwa NNPP
babbar caca ce mai wahalar bullewa.
A
nan ne 'Yan Kwankwasiyya su ka shiga matsala; su tsaya a PDP, ba za a
yarda da jar hularsu ba, su cire jar hula (su rabu da Kwankwaso), ba su
da tasirin kirki a zabe a karon kansu. Su koma APC? Kwamacalar can ta
zarce ta PDP. Ko me zai faru dai, Kwankwaso zai nemi sa'a a zaben kasa a
2023. Hakan babbar asara ce ga jam'iyyar PDP domin babu 'dan hamayya da
zai iya tarar karfin gwamnatin APC irinsa.
Wadanda
za su yi wa NNPP takara a jihar Kano za su iya kasancewa matasa masu ilmi da
jar hula. Za su gwabza da 'Yan uwasu wadanda su ka zauna a PDP ko
bangaren Shekarau da wadanda su Goggo suka tsaida a gefe guda. Wadannan
rukuni ba su da gogewa sosai a siyasa irin abokan gabarsu, amma su na da
farin jinin Kwankwaso. PDP za ta zama ba ta da farin jini, sai dai ta
na tare da masu dukiya da fitattu. APC kuma ta na da gwamnati, burbushin
Buhari, tare da dimbin rikicin cikin gida. A wasu jihohin Arewa, NNPP za ta tattara wadanda suka rasa madafa a PDP da APC, da mabiyar darikar jar hula. Kuma a halin yanzu, jama'a su na bukatar su raba kafafunsu.
Dalilin
Kwankwaso na takara a 2023 shi ne ya fito da kan shi. Idan har ya samu
kuri'u masu yawan gaske, dole PDP ta neme shi idan ta na neman komawa
kan mulki, ko kuma APC ta lallabe shi ya dawo domin gudun ya birkita
mata lissafi. Shi dai zai bata ruwa ne, ba dole kuma ya sha ba. Shiyasa
babu bukatar magoya bayansa su rika zagin PDP, APC da sauran yan siyasa,
ba a san gobe ba. Idan ka ce na-kusa da Madugunka sun ci amana da suka
ki shiga NNPP, a baya ai sun rike amanar, kuma shi yanzu ya kara cin
amanar PDP.
Idan
tayi wa NNPP kyau a 2023, to ta gyaru ga Kwankwaso, idan ba a dace ba,
to ya shiga wani layi mara fita, zai rage nauyi. Muddin NNPP ta bada mamaki a irinsu
Kano, Kaduna, Katsina, Bauchi, da sauransu, to manyan jam'iyyu za sake
jawo Kwankwaso; Su hadu da gawurtattun yan siyasa, su hada karfi su yi
takarar gaske a gaba. Kokarin CPC a 2011 ne ta sa dole Bola Tinubu suka
hakura, su ka yarda aka hade-kai, ba don sun yarda da Janar ba.
Daga tafiyar TNM, zuwa
yanzu babu wasu tulin mutanen kirki daga fadin kasar nan da ke tare da
Kwankwaso, sai wasu tsofaffin barayi da wadanda suka gagara tabukai a gwamnatin APC da wasu tarkace. Akwai sauran aiki.
Kafin Kwankwaso ya samu mulkin kasa, ya na bukatar karbuwa da kyau a ko
ina, dole ya hada kai da 'yan siyasan kirki a Kudu, ya nutsa waje da
Arewacin Najeriya, ya nunawa Duniya matsayarsa a kan tattalin arziki, fasalin kasa,
ilmi, tsaro, da sauransu. Wannan kuma dai jan aiki ne, farin jini kadai
ba zai ba ka shugabanci ba kamar yadda tarihi ya nuna!
[Muhammad Malumfashi yana shafin Twitter @m_malumfashi]