Kayan abincin da Masana lafiya suke so duk namiji ya rika ci
Mun kawo wasu kayan abinci da ake so magidanta su rika ci a gidan aure
Masana sun ce wadannan abinci za su taimaka wajen kara wa maza karfi
Daga cikin nau’ukan abincin da ake bada shawarar a rika ci akwai ayaba
Hoto: https://parade.com
Ga ma’auratan da suke bukatar inganta rayuwar kwanciyar aurensu, akwai wasu jerin abinci da masana suka ce ya kamata mutum ya rika mu’amala da su.
Masana sun ce daga cikin abubuwan da suke jawo karfin namiji a gidan aure ya yi kasa akwai gajiya, rashin sukuni, shiga halin lahaula da shan kwayoyi.
Shafin Body and Soul ya kawo wasu kayan abinci da za su taimaka wa duk wani magidanci.
1. ‘Ya ‘yan kabewa
‘Ya ‘yan kabewa za su taimaka wa namiji da sinadarin zinc wanda yake inganta ruwan sinadarin ‘da namiji, kuma yana kara mai a jikin mutum.
Za a iya jefa ‘ya ‘yan kabewa a abin sha a lokacin kalaci, ko kuma a cikin kayan ganyen salak.
2. Nama
Irinsu naman saniya suna dauke da wani samufuri na na’u’in Amino acid da ake kira L-Carnitine, wanda yana taimaka wa wajen kara karfin gaba.
3. Ayaba
Ayaba suna dauke da bitamin B wanda yana rage gajiya a jikin ‘Dan Adam. Haka zalika ayaba na dauke da tryptophan da potassium da ke kara lafiya.
A jikin ayaba akwai sinadarin bromelain wanda aka ce yana kara karfin gudanar jini a jikin mutum.
4. Cocoa
Masana ilmin lafiya sun ce cin koko ko kuma cakulet da aka sarrafa yana aiki a matsayin kayan maza saboda sinadaran phenols da phenylethylamine.
5. Kwallayen gyada
Yawan cin kwallayen gyadan kashu da almond za su iya taimaka wa magidanci. Masana sun ce wadannan abubuwa suna da mai da sinadarin L-Arginine.
6. Kankana
A wani rahoto da Health line ya fitar, ya nuna kankana yana cikin kayan marmarin da suke kara lafiyar namiji domin ruwansa na dauke da L-citrulline.
7. Kwai
Masana lafiya sun ce kwai suna magance matsalolin ‘da namiji a gidan aure domin suna dauke da samfurin Amino Acid da ake kira L-arginine.