Tuesday, May 1, 2018

Huduba game da mata masu yawo tsirara da tufafi

HDUBAR JUMA'A DAGA MASALLACIN ITN

Daga bakin Sheikh Dr. Saeed Yunus Zaria





Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wa barakatuhu 

Dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah, muna gode masa mu na neman taimakon Sa, mu na neman gafarar Sa muna tuba gare Shi.

Mu na neman tsari daga sharrin kawunan mu, da kuma munanan ayyukan mu, duk wanda Allah ya shiryar da shi babu wanda ya isa ya batar da shi. Duk wanda Allah ya batar da shi ya bace  babu mai iya shiryar da shi. Allah ka shirye mu! 

Muna shaidawa babu abin bauta face Allah shi kadai, kuma mu na shaidawa Annabin mu mosoyin mu Muhammad SAW (Farin Jakadan Allah) tsira da amincin Allah su tabbata gare shi Bawan Allah ne, kuma Manzon Allah ne, Allah ka dada tsira da aminci  ga Annabin sa, Annabi Muhammad (SAW) da Alayan Sa, da Sahabban Sa. 

Bayan haka ‘Yan uwa mu ji tsoron Allah mu siffantu da siffofi irin na Al-Kurani. Lallai Annabi ya kasance halayansa Al-Kurani ne, idan kana so ka kalli Kurani, ka kalli rayuwar Manzon Allah SAW. Annabi yana nisantar duk wani hani na Kurani, yana tafiya da duk wani umurni na Kur’ani, kuma shi Kur’ani shine shiriya ga dukkan mutane. Allah ya shiryar da annabi ta hanyar Kur’ani, don haka Annabi ya cigaba da tafiya akan wannan hanyar ta Kurani. Annabi yayi hakane (kamar yadda Allah umarce shi) don ya fitar da mutane daga duhu zuwa haske. Lallai Kur’ani Ambato ne wanda Allah ya saukar da shi mai hikima, mai dadi, kuma hanyar Allah ce. Kur’ani yana shiryar da mutane zuwa ga hanya madaidaiciya, duk inda aka bi Duniya da Lahira yana shiryar da mutane kan hanya da take mafi tsayuwa a cikin umarni da hani, da kuma rayuwa da kwanciyar hankali. 

Daga cikin karantarwar addinin Musulunci da karantarwar Kur’ani ‘Yan uwa akwai abubuwan da Allah ya ambata dangane da Iyayenmu Mata; Matan shugaban tafiya watau Annabi Muhammad SAW, sannan inda Allah a cikin Kur’ani Ya nuna tsarkakar Matan Annabi Muhammad SAW. Matan Annabi tsarkakakku ne, wanda ya zage su ya tabe, wanda ya zagi daya daga cikin su ya tabe Duniya da Lahira, saboda Allah ya tsarkake su, Allah ya ambace su a matsayin Muminai masu da’a ga Allah. Allah ya kira Matan Manzon Sa da cewa “Watau ku zauna a cikin dakunan ku yaku matan Manzon Allah kada kuyi fita irin ta matan jahiliyya ta farko”, fitan tsaraici ku sani cewa bayan an aiko Mijin ku Annabin Rahma ya ba wa Mata ‘yancin su a yayin da su ke tafiya tsirara, ku tuna da ayoyin da ake saukarwa Annabin yayin da yake dakunan ku, sai dai ku ga fuskarsa ta canza jikinsa ya canza. Wanda kuma ba matan Manzon Allah ba fa? Lallai ana karanta Kur’ani a dakunan Mata suna sauraro, don haka Kur’ani ya shiga ko wani daki, ko wane kauye, sabpda haka ku yi koyi da Matan Manzon Allah don inuwa daya ta tara mu duka, ita ce Al- Kur’ani mai girma. 

Lallai a daina bayyana tufafi, ko kawa, ko ado, ko kuma jiki ga mjin da muharrami ba. Kur’ani ya hana mata fita sai da lalura wanda shari’ah ta yarda da shi, amma fita haka kawai babu dalili, Kur’ani ya hana ki, lallai Kur’ani ya tsawatar ga mata da su zama masu kula da mutuncinsu, su yi tsayin-daka a kan hakkin Allah, da na Mazajensu. Su ji tsoron Allah, idan har an fadawa Matan Manzon Allah haka, to ina ga Matan wadansu wanda ba na Annabi ba, kasancewar ba su da fahimata irin na matan Manzon Allah da karancin Imani saboda haka su suka fi cancanta ayi masu wannan wa’azin. 

‘Yanuwa yana daga cikin munanan abubuwan da muke gani a cikin wannan kasa, da garuruwa, da lunguna shine ka ga mace ta fita Matar Musulmi ta fita zuwa kasuwanni haka kawai, ba gaira babu dalili, musamman kusantowar azumin nan; mata su je su cika kasuwa, babu hijabi, ka ga mata a titi, su na siye suna sayarwa, babu hijabi tattare da su. Musulunci bai hana ki zuwa kasuwa ba amma sai da dalili, sai kim sa tufafi kuma sai kin dauki izini daga Mijinki, ko kuma daga Mahaifin ki, ko kuma Waliyyin ki. ‘Yanuwa Wallahi wannan al’amari ya cika Kasa ya cika Garuruwa. Ka ga mahaukaci yana tafiya tsirara, kaga kuma mai hankali a cikin mata ita ma tana tafiya tsirara. Mumini da Fasiki, da Maihakali, da Wawa, da Mara hankali yayi ta kallon tsiraicinta, bata damu ba, saboda rashin tsoron Allh da kiyaye dokokin Allah, da kuma ganin cewa ai ba ita kadai bace. Allah ya rufeta da wani Hijabi amma ta kware shi, ta bude shi, ta fito tsirara cikin kasuwa, akan kwalta da titi ba su jin kunya, ko kuma cikin makarantu, daga cikin makarantu wanda muke da su manya-manya, kai har da Sakandare, mara hankali yayi farin ciki, mai hankali yayi bakin ciki. 

‘Yanuwa ku sani cewa wulakanta mace ne ta fito tsirara, wato shi ne ta fito babu hjiabi,  haduwar maza da mata a ko wanu mataki, yana daga cikin abubuwan da ke sa Allah yayi fushi hakan yana fusata Allah,  kuma abu ne wanda Allah ya haramata. Hijabi, wajibi ne a musulunci, yan uwa wanda suka zauna da manzon Allah su ne suka ga yadda mata su ke sa hijabi a lokacin manzon Allah, saboda haka ba ka da wata fassara face daga Manzon Allah, babu wani Malami da zai ce ai sa gyale ya wadatar.

Ya ku masu Mata, ya ku masu ‘Ya’ya ku sani cewa fitan Matanku tsirara yana kawo matsala a Kasa, ku  sani cewa duk Musulmi mai kishi bai kamata ya bari shaidan yayi wasa da hankalin sa ba, bai kamata yayi wasa da shari’ah ba, kada ka bari ayi wasa da hankalin ka da wasu fassarori, da wasu ‘yan yaudara irin na shaidan, domin wannan na iya sa Allah yayi fushi da kai da matarka, da dukiyar ka. Ka sani cewa Annabi ya nuna mana cewa karshe shi ne nasara, idan karshen ka ya munana, na matanka su ka munana, an yi mummunan karshe!

Saboda haka kowa ya sa Iyalin sa su sa Hijabi, Annabin Rahama na cewa “Ko dai kuyi umarni da kyakkyawan aiki, kuma ku yi hani da mummuna, ko kuma Allah ya kusa ya saukar da wata bala’i mai girma”. ‘Yan uwa mu ji tsoron Allah lallai wanda ke karkashin mu na iyalin mu, mu tabbata cewa sun sanya Hijabi, lallai wasu daga cikin mutane sukan fadi cewa ga wasu sun sanya Hijabi amma suna sabon allah, kuma ga wasu wanda basu sa hijabi ba amma suna biyayya ga Allah, to duka sai ayi masu wa’azi Huduba tana kira cewa mai sa Hijabi ya cigaba da sawa amma ya ji tsoron Allah, ka da ace ka bar gemu kuma kana cuta, ka dage wando kuma kana yaudara, ka zama Ustaz amma mayaudari. 

Akwai wani hadisi mai abintsoro wanda Abu Huraira ya ruwaito cewa, “Iri biyu (2) na Mutane su na daga cikin ‘yan wuta, Annabi yace shi bai gan su ba, amma za su zo a karshen zamani; Akwai jama’a wanda suke da bulala kamar kunnuwan sa su na dukan mutane ba gaira ba dalili” Sai ka yi bincike wasu mutane ne wanda suke dukan mutane hakanan? “Annabi yace kuma da wasu mata, ga su da tufafi amma tsirara su ke, sun tara gashi kamar tozan rakumi wanda yayi shekara uku, ba za su shiga aljanna ba, kuma ba za su ji kamshin aljanna ba” ‘Yan uwa watau ashe mata, da ‘Ya’ya, da Dalibai, da su ke fito da kan su da tarin gashi, ga ta tsirara kuma ‘Ya Musulma. Allah kuma yace: “Ku kiyaye kawunanku da iyalanku daga wuta wanda yake mutane da duwatsu sune makamashin ta. A cikin wutan akwai Mala’iku masu tsanani, masu fushi, su na azaba ne kawai!” Allah ya kiyaye mu daga shiga wuta, Allah ka kare mu daga sharrin kan mu, ka kare mu daga sharrin wanda mu ka kawo Duniya!

Huduba ta biyu; bayan godiya ga Allah tana cewa ku ji tsoron Allah mai girma, ku kasance masu da’a gare Shi, ku kasance masu biyyaya gare Shi. Mata su kasance masu koyi da musulmai ba da Kafirai ba, su Kafirai Makiya Annabi ne, za kaga mata sun bude kirjin su a waje, wuyanta a waje, ana ganin kafadar ra, wannan bala’i ne, so ake ace Annabin mu bai iya ba. Ku sani cewa su ne irin wannan matan da Annabi yace bai gani ba a lokacin sa amma za su zo nan gaba. Lallai Kafirai sun ce ba za su rabu damu ba, sai sun rabamu da Annabi Muhammad SAW, mu kuma mu rike koyarwar Manzon Allah, mu sanya tufafi irin wanda allah yake so. Akwai bakin ciki a yau a ga cewa mu na koyi da Shaidan, mu na koyi da tufafi wanda ba namu ba, ka ga Musulmi na cin abinci da hannun hagu, yana barin akaifa tayi tsawo, yana barin gashin baki wai don ya ba mutane tsoro, ka ga namiji na gaisawa da mace, Allah ka kare mu daga wannan bala’i, ku sani Manzon Allah yace duk wanda yayi kama da wani zai tashi da shi Ranar tashin Alkiyama. 

‘Yan uwa mu kiyaye koyi da Yahudu, mu yi koyi da Manzon Allah, wannan kadan kenan daga cikin karantarwar Kur’ani da karantarwar manzon Allah SAW. Lallai wani Malami yayi bayani mai dadi lokacin da aka zo yin taro na Sarauniyar kyau a Najeriya, ya nuna cewa kamar kwai ne wanda aka bare da wanda ba’a bare ba, shin wanne za ka zaba? Tabbas wanda ba’a bare ba! Wai shin tsarin kafirai ko na jahiliyya kuke so, ko tsarin musulunci? Ya Allah mun tuba, lallai mace ta karrama kan ta idan tasa tufafi irin na musulunci, sannan ta raba kanta da dabbobi. Za ku ga kafirai suna fitowa tsirara a gaban mazajen su saboda haka Allah ya tsine masu. Ibn Al-Qayyin yace duk jikin da ake rufe shi sai kaga yafi jikin da ba’a rufewa lafiya da kyau. 

Muna rokon Allah ya shiryar da al’umman annabi Muhammad SAW, kuma idan an hana ki sanya hijabi wajen aiki, babu komai kije kiyi aikin ki, idan ta fito ki sa hijabin kuma ki sake shi har kasa, wata rana wadanda su ke hana tan Allah zai canza su, zai kawo wanda za suce a sa. Kuma muna kira ga Shugabanni wanda su ke da ikon bari a sa hijabi da su bari a sa din, idan ba haka ba Allah zai jarrabe su da fitina. Allah yace kaji tsoron mutuwa!

Huduba a karshe tana jawo hankalin malamai da su ke bada fatawa ba bisa yadda Manzon Allah da Sahabbai suka tafi a kai ba, da su ji tsoron Allah, su koma su duba littatafai, da yadda Sahabbai su ka fassara wannan al’amarin. Kuma lallai mata ku ji tsoron Allah, gyale ki sa wa mijinki a gida ko ma ki fito masa tsirara. 

Allah muna rokonka ka daukaka musulunci, ya Allah yadda ka hada kafadun mu, Allah ka hada zukatan mu a kan gaskiya, ya Allah ka kare mu daga dukkan fitina, Allah ka sa mu zama masu gaskiya masu san gaskiya. Allah ka bamu nasara. Ameen!




Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...