Saturday, September 16, 2023

Deputy CBN Governor nomination; Dattijo’s journey towards national development

Deputy CBN Governor nomination; Dattijo’s journey towards national development 


- 17th September, 2023.

 

 

In a nation marked by its vibrant democracy and diverse talents, individuals who embody dedication, innovation, and a commitment to public service stands out.

Muhammad Sani Abdullahi, affectionately known as Dattijo, is one such individual whose journey from international development expert to a public servant in Nigeria's government has been nothing short of remarkable. 

 


Recently nominated as one of the Deputies to the Governor of Nigeria's Central Bank by President Bola Ahmed Tinubu, Dattijo's potential to contribute to national development is both promising and inspiring. Dattijo's career trajectory has been characterized by a selfless commitment to improving the lives of Nigerians. His academic background is a testament to his commitment to gaining the knowledge and skills necessary to effect meaningful change. He obtained his master's degree in Development Economics and Policy from the University of Manchester and a second master's degree from Ahmadu Bello University, where he studied International Affairs and Diplomacy. These qualifications laid the foundation for his future contributions to international development and diplomacy.

Furthermore, Dattijo's pursuit of excellence didn't stop at formal education. He actively sought opportunities to enhance his understanding of critical subjects that would later prove invaluable in his public service career. He earned certificates in Public Finance at the prestigious London School of Economics, delved into Sustainable Development at Columbia University, and mastered the intricacies of Advanced Project Management at Oxford University. These achievements highlight his commitment to continuous learning and his dedication to being a well-rounded leader.

Dattijo's passion for leadership and global affairs was further evident when he was selected to be part of the 2017 cohort of Georgetown University's Leadership Seminar. This experience broadened his horizons, allowing him to interact with a diverse group of leaders from around the world and share ideas that would eventually benefit his homeland.

His tenure as a policy adviser at the office of the United Nations Secretary-General Ban Ki Moon in New York was the culmination of his academic and professional journey. In this esteemed role, he played a pivotal part in forming the core team that developed the Sustainable Development Goals (SDGs), which are now guiding nations, including Nigeria, in their pursuit of sustainable development. However, Dattijo's dedication to his homeland led him to make a pivotal decision—to leave his prestigious UN appointment and return to Nigeria to serve as the Chief of Staff to the Governor of Kaduna state and later Commissioner for Budget and Planning in Kaduna State Government. This decision showcased his unwavering commitment to being a catalyst for positive change at the grassroots level. In this role, he contributed significantly to the development of Kaduna State, working tirelessly to ensure that public resources were allocated efficiently to benefit the people.

Even though Dattijo resigned from his role as Commissioner to contest for Gubernatorial and later senatorial seat representing the Kaduna Central Senatorial Zone in the 2023 general elections, his commitment to public service remained undiminished. While he may not have clinched victory in the electoral contest, his dedication to the welfare of his constituents and his unwavering belief in the potential of Nigerian democracy were evident throughout the campaign. Dattijo's latest endeavor, the publication of his book titled "Disruption: Rethinking Governance to Work for the Poor," further underscores his commitment to addressing the challenges facing Nigeria's governance structure. In a time where innovative solutions and fresh perspectives are desperately needed, Dattijo's book offers a roadmap for reimagining governance to be more inclusive and responsive to the needs of the most vulnerable in our society.

President Bola Ahmed Tinubu's nomination of Dattijo as one of the Deputies to the Governor of Nigeria's Central Bank is a commendable choice. It recognizes Dattijo's wealth of experience, his dedication to service, and his potential to make a significant impact on Nigeria's economic landscape. As we confront the complex economic challenges facing our nation, having individuals like Dattijo in key positions is crucial for driving positive change.

Muhammad Sani Abdullahi (Dattijo) is an exemplary leader, a scholar, and a public servant who embodies the qualities that can drive Nigeria towards a brighter future. His academic achievements, coupled with his extensive experience, make him a beacon of hope for our nation's development. As he takes on this new role in the Central Bank, Nigerians have every reason to be optimistic about the positive changes he can bring to our nation's economic landscape. With his nomination, we have reason to be hopeful that Dattijo will continue to be a beacon of hope for our nation's development, ensuring that the principles of inclusivity, accountability, and progress remain at the forefront of our national agenda.

Muhammad Abdullahi Sani Dattijo's journey from a young scholar to an internationally recognized development expert and Nigerian public servant is an inspiration to all. His contributions to global development initiatives, dedication to public service, and visionary leadership make him an ideal candidate for the role of Deputy to the Governor of Nigeria's Central Bank. As Nigeria strives for economic growth, social development, and poverty reduction, Dattijo's expertise, passion, and commitment to sustainable development will undoubtedly contribute to the nation's progress. It is with great anticipation that we await his future endeavors and the positive impact he will undoubtedly make on Nigeria's path to a brighter future.

 

Written by Abba Gadagau

Saturday, June 10, 2023

Nada Sabon Gwamnan CBN a Najeriya

Nadin Gwamnan rikon kwarya a CBN


Dauko Adebisi Shonubi a matsayin Gwamnan rikon kwarya ya na da alamar tambaya – ba wai saboda asalinsa Injiniya ba ne. Ya kamata mutane su san tun shekaru kusan 40 da suka wuce ya yi watsi da Injiniyanci, ya yi digirgi a MBA kuma ya kware a fannin tattalin arziki.

Bankin CBN Hoto: thewhistler.ng    


Kafin zuwansa CBN tun 2018, Adebisi ya yi aiki da manyan bankuna irinsu Citibanki Ecobank, Union, FCMB. Bayan manyan mukamai da ya rike a bankuna, sai da ta kai ya shugabanci bankin NIBBS na kasa. Saboda haka ba abin mamaki ba ne Injiniya ya saki layi zuwa banki.

Inda gizo ke sakar. Akwai mataimakan Gwamnoni 4 a CBN – Edward Adamu, Aisha Ahmed da Kingsley Obioro. Kusan duka wadannan sun riga Adebisi zuwa babban banki, su na gaban shi. Don haka za ayi zargin cewa ya samu kujerar ne saboda shi kadai ne Bayarabe a cikinsu.

A lokacin da Goodluck Jonathan ya dakatar da Sanusi Lamido, sai ya umarci Dr. Sarah Alade ta zama gwamnan riko domin ta dade a bankin (ina tunanin tun 2004 ta zo). Dr. Alade kwararriyar ma’aikaciyar banki ce kuma asalin ta mutumiyar Arewa maso tsakiyar Najeriya ce.

Wata matsala kuma ita ce, a shari’ar Sanusi v Gwamnatin tarayya, kotu ta ce shugaban kasa zai iya dakatar da gwamnan babban banki amma bai isa ya yi nadi (ko da na rikon kwarya) ba, sai da yardar ‘yan majalisa. Yanzu SGF ya ce Adebisi ya fara aiki, alhali ba a rantsar da majalisa ba.

  

Saturday, March 12, 2022

2023: Kwankwaso da jam'iyya mai kayan marmari a Najeriya

Kwankwaso da jam'iyya mai kayan marmari a Najeriya


Kusan shi fa Kwankwaso ya san samun mulki a 2023 zai yi masa wahala. Duk da dai magoya bayansa akwai 'dan-karen karfin hali. A irin gogewa da yawan mabiyan da yake da su, matsayin da aka ba shi a APC ne ya yi masa kadan, da ya je PDP sai ya iske su ma duk ba su da niyyar gwabzawa da APC da kyau, sun sa son rai kuma sun raina karfin APC da na Kwankwaso. PDP sun kama wasu tarkace saboda su na da baitul mali, abin da Kwankwaso bai da shi, a sakamakon murde zaben Kano a 2019. Murdewa Abba Gida Gida zabe ya jawowa Kwankwasiyya cikas na gaske; ya rabawa Kwankwaso hankali, ya tilasta shi shiga siyasar gida, ga kalubale na rashin mulki. 
 
 

 
 
 
Idan har ba sha'awar zama dan kallo yake yi ba, zaman Kwankwaso a PDP a irin wannan yanayi ba ta da amfani. A nan kusa, ba zai samu takara ba, ba zai amfana da komai ba, sai dai su amfana da shi. Bayan gwamna, Kwankwaso ya rike duk wata babbar kujera ta tarayya, burinsa daya ne a Duniya. Daga nan har zuwa bayan 2023, Kwankwasiyya ba ta cikin lissafin PDP face nemawa PDP kuri'un Yan Arewa a Kudu. Hakan ta sa yake neman inda zai fito da kan shi. Kuskure ne a siyasa ka ce wai a zauna ayi hakuri, 'dan siyasa kullum cikin lissafin zabe na gaba yake yi, ga shekaru su na tafiya. Kamar dai a 2018, yanzu ma lokaci ya na neman ya kure.
 
Kafa sabuwar jamiyya ta na da wahalar gaske. Wasu sun jarraba a baya, suka yi asarar makudan kudi, kuma ba a dace ba. Ina ragowar mafita? A hade da wata karamar jam'iyya kamar su PRP da masu kayan marmari. Hakan ta sa Madugun Kwankwasiyya ya burma cikin NNPP. Inda matsalar ta ke ita ce a gida watau Kano. Wasu Kwankwasawa sun ajiye mukamansu a APC, sun bi Kwankwaso zuwa PDP a zaben 2019, suka yi biyu-babu. Su na tsoron sake tsalle zuwa NNPP babbar caca ce mai wahalar bullewa.  
 
A nan ne 'Yan Kwankwasiyya su ka shiga matsala; su tsaya a PDP, ba za a yarda da jar hularsu ba, su cire jar hula (su rabu da Kwankwaso), ba su da tasirin kirki a zabe a karon kansu. Su koma APC? Kwamacalar can ta zarce ta PDP. Ko me zai faru dai, Kwankwaso zai nemi sa'a a zaben kasa a 2023. Hakan babbar asara ce ga jam'iyyar PDP domin babu 'dan hamayya da zai iya tarar karfin gwamnatin APC irinsa.
 
Wadanda za su yi wa NNPP takara a jihar Kano za su iya kasancewa matasa masu ilmi da jar hula. Za su gwabza da 'Yan uwasu wadanda su ka zauna a PDP ko bangaren Shekarau da wadanda su Goggo suka tsaida a gefe guda. Wadannan rukuni ba su da gogewa sosai a siyasa irin abokan gabarsu, amma su na da farin jinin Kwankwaso. PDP za ta zama ba ta da farin jini, sai dai ta na tare da masu dukiya da fitattu. APC kuma ta na da gwamnati, burbushin Buhari, tare da dimbin rikicin cikin gida. A wasu jihohin Arewa, NNPP za ta tattara wadanda suka rasa madafa a PDP da APC, da mabiyar darikar jar hula. Kuma a halin yanzu, jama'a su na bukatar su raba kafafunsu.
 
Dalilin Kwankwaso na takara a 2023 shi ne ya fito da kan shi. Idan har ya samu kuri'u masu yawan gaske, dole PDP ta neme shi idan ta na neman komawa kan mulki, ko kuma APC ta lallabe shi ya dawo domin gudun ya birkita mata lissafi. Shi dai zai bata ruwa ne, ba dole kuma ya sha ba. Shiyasa babu bukatar magoya bayansa su rika zagin PDP, APC da sauran yan siyasa, ba a san gobe ba. Idan ka ce na-kusa da Madugunka sun ci amana da suka ki shiga NNPP, a baya ai sun rike amanar, kuma shi yanzu ya kara cin amanar PDP.  
 
Idan tayi wa NNPP kyau a 2023, to ta gyaru ga Kwankwaso, idan ba a dace ba, to ya shiga wani layi mara fita, zai rage nauyi. Muddin NNPP ta bada mamaki a irinsu Kano, Kaduna, Katsina, Bauchi, da sauransu, to manyan jam'iyyu za sake jawo Kwankwaso; Su hadu da gawurtattun yan siyasa, su hada karfi su yi takarar gaske a gaba. Kokarin CPC a 2011 ne ta sa dole Bola Tinubu suka hakura, su ka yarda aka hade-kai, ba don sun yarda da Janar ba. 
 
Daga tafiyar TNM, zuwa yanzu babu wasu tulin mutanen kirki daga fadin kasar nan da ke tare da Kwankwaso, sai wasu tsofaffin barayi da wadanda suka gagara tabukai a gwamnatin APC da wasu tarkace. Akwai sauran aiki. Kafin Kwankwaso ya samu mulkin kasa, ya na bukatar karbuwa da kyau a ko ina, dole ya hada kai da 'yan siyasan kirki a Kudu, ya nutsa waje da Arewacin Najeriya, ya nunawa Duniya matsayarsa a kan tattalin arziki, fasalin kasa, ilmi, tsaro, da sauransu. Wannan kuma dai jan aiki ne, farin jini kadai ba zai ba ka shugabanci ba kamar yadda tarihi ya nuna!
 
 
 
 
[Muhammad Malumfashi yana shafin Twitter @m_malumfashi]

Saturday, October 9, 2021

Na’ukan abincin da ya dace da miji a maimakon ya rungumi 'kayan maza'

 

Kayan abincin da Masana lafiya suke so duk namiji ya rika ci

 

Mun kawo wasu kayan abinci da ake so magidanta su rika ci a gidan aure

Masana sun ce wadannan abinci za su taimaka wajen kara wa maza karfi

Daga cikin nau’ukan abincin da ake bada shawarar a rika ci akwai ayaba

 


Hoto: https://parade.com


Ga ma’auratan da suke bukatar inganta rayuwar kwanciyar aurensu, akwai wasu jerin abinci da masana suka ce ya kamata mutum ya rika mu’amala da su.

Masana sun ce daga cikin abubuwan da suke jawo karfin namiji a gidan aure ya yi kasa akwai gajiya, rashin sukuni, shiga halin lahaula da shan kwayoyi.

Shafin Body and Soul ya kawo wasu kayan abinci da za su taimaka wa duk wani magidanci.

 

1.      ‘Ya ‘yan kabewa

‘Ya ‘yan kabewa za su taimaka wa namiji da sinadarin zinc wanda yake inganta ruwan sinadarin ‘da namiji, kuma yana kara mai a jikin mutum.

Za a iya jefa ‘ya ‘yan kabewa a abin sha a lokacin kalaci, ko kuma a cikin kayan ganyen salak.

2.      Nama

Irinsu naman saniya suna dauke da wani samufuri na na’u’in Amino acid da ake kira L-Carnitine, wanda yana taimaka wa wajen kara karfin gaba.

3.      Ayaba

Ayaba suna dauke da bitamin B wanda yana rage gajiya a jikin ‘Dan Adam. Haka zalika ayaba na dauke da tryptophan da potassium da ke kara lafiya.

A jikin ayaba akwai sinadarin bromelain wanda aka ce yana kara karfin gudanar jini a jikin mutum.

4.      Cocoa

Masana ilmin lafiya sun ce cin koko ko kuma cakulet da aka sarrafa yana aiki a matsayin kayan maza saboda sinadaran phenols da phenylethylamine.

5.      Kwallayen gyada

Yawan cin kwallayen gyadan kashu da almond za su iya taimaka wa magidanci. Masana sun ce wadannan abubuwa suna da mai da sinadarin L-Arginine.

6.      Kankana

A wani rahoto da Health line ya fitar, ya nuna kankana yana cikin kayan marmarin da suke kara lafiyar namiji domin ruwansa na dauke da L-citrulline.

7.      Kwai

Masana lafiya sun ce kwai suna magance matsalolin ‘da namiji a gidan aure domin suna dauke da samfurin Amino Acid da ake kira L-arginine.

 

 


 

 

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...